Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

0
5

TUN KAFIN A HAIFI UWAR MAI SABULU, BALBELA TAKE DA FARIN GASHINTA: NAZARIN HANYOYIN ADANA KAYAYYAKIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

Daga

Magaji Ahmad Gaya PhD

Sashen Koyar Harsunan Nijeriya,

Jami’ar Northwest, Kano

magaya@nwu.edu.ng /magajiahmadgaya@gmail.com

08066009039

Takardar Da Aka Gabatar A Taron Makon Hausa Wanda Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Jami’ar Arewa Maso Yamma (Northwest) Kano Ta Shirya. Wanda Aka Gabatar A Babban Ɗakin Taro Na ‘Yanganau Da Ke A Farfajiyar Jami’ar. Ranar Alhamis 29/01/2026

Tsakure

Al’ummar Hausawa, mutane ne waɗanda tun fil’azal suna da hikimominsu da suka gada tun iyaye da kakanni, waɗanda suke aiwatar da su har ya zuwa yau. Suna amfani da fasahohinsu da hikimimominsu da basirarsu ta hanyar sarrafa albarkatun da suke kewaye da muhallansu, waɗanda suka haɗa da adana kayayyakin Hausawa na gargajiya domin su samar da kayayyakin amfanin kansu.

Manufar wannan takarda ita ce bayyana wasu hanyoyin adana kayayyakin gargajiya wanda suke amfani da su tun kafin haɗuwar su da baƙin al’ummu. An yi amfani da hanyoyin gudanar da bincike, waɗanda suka haɗa da tattaunawa da ziyarar gani da ido da karantawa daga wasu rubutattun bayanai.

An ɗora wannan bincike ne bisa ra’in Adana Al’adu da Cigaban Al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da wannan bincike. Gusau (2015:55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i da suna ‘‘Mazahabar Adana Al’adu’’. Shi kuma Sha’aibu (2013:78), ya kira makarantar da ke da’awar wannan ra’i na Adana Al’adu da suna “Mazahabar Muhafaza”.

Sakamakon takardar ta nuna cewa al’ummar Hausawa suna da hanyoyin adana kayayyakinsu a gargajiyance waɗanda suka gada tun kafin zuwa ko haɗuwa da baƙin al’ummu. Hausawa suna amfani da su wajen adanawa tare taskacewa don gudun lalacewa ko salwanta.

Muhimman Kalmomi: Adana da Kayayyaki da Hausawa da Gargajiya.

 Gabatarwa

Wannan takarda za ta yi duba ne a kan kayayyakin da al’ummar ƙasar Hausa suke amfani da su wajen adanawa. Waɗannan kayayyakin gargajiya da za a yi nazari a kansu, na su ne, kuma har gobe suna amfani da su wajen aiwatar da ajiye-ajiye da aikace-aikace. Akwai tarin fasahohi da hikimomi ta yadda Hausawa suka samar da su, musammanma idan aka yi la’akari da yadda suke taimaka musu wajen adana kayayyakinsu cikin sauƙi, ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma, an nazarci yadda masu sana’ar suke amfani da su, kuma an kawo bayanin yadda suke  samar da su da kuma nau’o’in aikace-aikacen da ake yi da su. Hausawa sun inganta wasu kayayyakin, domin su dace da buƙatun mutanan, da ma na wannan zamani. Har ila yau sun yi ƙoƙari matuƙa wajen rage tsofaffin kayayyaki, waɗanda maimakon su yi wasarere da su gaba ɗaya, akwai buƙatar ƙara inganta su domin tafiya da zamani.

Manufar Gudanar da Bincike

Manufar wannan takarda ita ce, bayyana wasu hanyoyi  da al’ummar Hausawa suke amfami da su wajen adana ko taskce kayayyakinsu domin gudun lalacewa ko salwanta ko kuma domin tarihi da makamantansu.

Haka kuma, wata manufar ita ce, domin bayyana ko fayyace wasu tsofaffin kayayyakin da ake adanawa haɗi da amfani da su. Sannan kuma, wata manufar ita ce, domin fito tare da bayyana alfanun da kayayyakin suke da shi wajen adanawa da kuma mai da hankali wajen nazarinsu ga masu bincike domin gujewa gushewarsu.

Ra’in Bincike

Wannan bincike an ɗora shi ne a kan Ra’in Haƙiƙa, wannan bincike ya bibiyi ra’o’in binciken al’adun Hausawa daban –daban don tantance wanda ya dace da wannan bincike: inda aka gano cewa Ra’in Adana Al’adu da Cigaban Al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da wannan bincike.

Gusau (2015:55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i da suna ‘‘Mazahabar Adana Al’adu’’. Shi kuma Sha’aibu (2013 :78), ya kira makarantar da ke da’awar wannan ra’i na adana al’adu da suna ‘‘Mazahabar Muhafaza’’.

Salsalar Ra’i

Wannan ra’i ya samo asali ne ta hanyar gudummawar masana da hukukmomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, wanda John Hawkes ya assasa a matsayin jagoran wannan ra’i.

 Mabiya Ra’i

Ko da yake John Hawkes ne ya fi shahara wajen gabatar da wannan ra’i, amma akwai masana da hukumomi da dama da suka rungumi tare da bunƙasa wannan ra’in na adana al’ada. Wasu daga cikinsu su ne:

  • Unesco da UNDP (United Nations Development Programme)
  • David Throsby,
  • Jown Hawkes Australian Coucil For the Art
  • Katrilna Soini & Inger Birkeland
  • Nancy Duxbury
  • Keith Nurse
  • Graham Fairclough

Ayyukan da aka Ɗora Ra’in a kai

Akwai bincike masu dama da aka gudanar a baya, waɗanda suka yi amfani da wannan ra’i na adana al’ada daga cikin su akwai John Hawkers (2001) ya yi littafi mai suna The Fourth Pillar of Sustainability: Cultures Assencial Role in Public Planning. Ya jaddada cewa dole ne a haɗa al’adu cikin tsare-tsaren cigaba.

Sannan da David Throsby (2008-2010), Linking Cultural and Ecological Sustainability. The Economic of Cultural Policy: ma’ana dangantakar da ke tsakanin Al’adu, Tattalin Arziki da Ɗorewarsu. Sannan kuma akwai binciken da UNESCO ta tallafa a shekara ta (2003-2015), mai taken “Al’adun Gargajiya Marasa Ganuwa (Intengible Cultural Heritage), da ilimin gargajiya na asali, sai kuma Harsuna da suke fuskantar shuɗewa.

Haka kuma akwai binciken da aka gabatar a jami’o’in gida a kan al’adun Hausawa da suka haɗa da:

  • Aminu Lawan, ya yi bincike a kan “Ɗorewar al’adun Hausawa a Zamanin Zamani”. Jami’ar Bayero, Kano.
  • Zainab Sadiq, ta yi bincike a kan “Rawar Bukukuwan Gargajiya Wajen Raya Al’adu”. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
  • Abdullahi Musa. ya yi bincike mai taken “Tasirin Zamani da Adabin baka na Hausa”. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
  • Hadiza Bello, ta yi bincike mai taken ‘‘Rawar ‘Yammata Wajen Kare da Ɗorewar Al’adu a Arewacin Najeriya”. Jami’ar Ilorin
  • Sani Ibrahim, ya yi bincike a kan “Gudummuwar Sarautun Gargajiya Wajen Ɗorewar Al’adu”. Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua Katsina.

Dangantakar Ra’i Da Nazari

Bayanan cikin wannan ra’i suna da dangantaka ta kai tsaye da wannan nazari, sannan za su zamo wani dandamali da wannan bincike zai taka ya hau har wannan bincike ya samu kammaluwa. Saboda ra’in yana bayani ne kan yadda za a tseratar da al’adu daga salwanta, wanda wannan shi ne ƙudirin wannan bincike da za a gudanar.

Hanyoyin Gudanar da Bincike

Kamar yadda aka sani, babu aikin da za a yi ba tare da bin wasu hanyoyi na gudanar da shi ba. Fayyace waɗannan hanyoyi a bincike irin wannan yana da matuƙar muhimmanci, domin zai taimakawa wajen tabbatar da sahihancin bayanan da aka kawo a cikin aiki.

Ba a bar wannan binciken a baya ba ta wannan fuska, domin shi ma an yi amfani da wasu hanyoyi wajen tattara bayanan da suka taimaka wajen aiwatar da shi. Daga cikin hanyoyin, akwai tattaunawa da mutanan da aka samu damar tattaunawa da su domin samun nasarar wannan bincike.

Wajen gudanarwa an yi la’akari da matsayi da kuma shekaru. Mutanen da aka tattauna da su sun haɗa da tsofaffi maza da mata, waɗanda suka taimaka wajen fito da wasu muhimman bayanai na waɗannan kayayyakin aiki. An kuma kai ziyarar gani da ido, inda kai tsaye aka ziyarci masu gabatar da ayyukan kaba da maginan ƙasa da fatu da sauransu, kuma aka tabbatar da wasu bayanan da aka samo daga gare su.

Baya ga waɗannan hanyoyi, an kuma tuntuɓi masana na sana’o’in gargajiyar Hausawa, kuma an bibiyi rubuce-rubucen magabata inda aka samu tarin bayanai da suka taimaka wajen rubuta wannan takarda.

Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

Akwai hanyoyin da ake amfani da su wajen adana kayayyakin Hausawa na gargajiya masu yawan gaske, waɗanda lokaci ba zai bayar da damar kawa su gaba ɗaya ba, sai dai a kawo misalan wasunsu tare da bayani.

Rumbu

An bayyana kalmar rumbu da shi ne, “ɗakin da ake ginawa da ƙasa ko karan dawa ko gamba domin adana hatsi” (Sa’id, B. da wasu 2006). Ana saƙa rumbu ne da ciyawar gamba wadda take da tsawo da ƙwari, akan ɗora bisa dirkoki ko kuma manyan duwatsu saboda gudun  ƙwari ko ɓeraye.

Akan ɗora masa  ɗan boto a sama a matsayin murfi domin adana kayan amfanin gona irinsu gero ko dawa ko gyaɗa ko wake ko ɗauro cikin zangarniya. Idan ana buƙata sai a tsakura ko kuma a ɗebo domin biyan bukatar yau da kullum.

Randa

Wannan wani mazubi ne da ake ajiye ruwa a cikinta.  Sa’id da wasu, (2006) sun bayyana ta da cewa” “Wata ƙatuwar tukunya da galibi ake zuba ruwa a cikinta ko kuma ta zamanto taskar ajiye kuɗi. Har ila yau tana iya zama rijiyar karofi ta rini. Randa tana daga cikin kayayyakin da Hausawa suke amfani da ita, magina ƙasa ne suke gina randa.

Yayin da za a gina ta magina, suna samo taɓo da ƙasa ta jangargari haɗi da ruwa a cakuɗa har dai a samar da ita. Yayin da aka samar da ita akan ajiye ruwan sha da kuma adanawa domin tanadin abubuwan da za su iya tasowa haɗi da abubuwan yau da kullum.

Ruzu

Wata irin ƙaramar jakace saƙaƙƙiya. Ruzu wata jaka ce wadda ake saƙa ta da kaba ko zare, tana da ɗan faɗi da tsayi sannan tana da maratayi, ana rataya ta a kafaɗa, mafarauta sukan saka naman daji idan sun kamo a ciki, yayin da suka fita farauta ko sharani ko ƙuloto. Sannan idan suka dawo gida akan ajiye naman da suka samo a cikinsa (Tattaunawa da Baba Sayyadi).

Taskira

Ana saka ta dominn aikin kaɗin zare da abawa, tana da faɗi kamar faranti ƙarami ko filet na zamani, sai a shimfiɗa mata fatu riɓi-riɓi kamar talatin ko talatin ko ashirin, mai ɗakin kan ajiye wasu abubuwa masu muhimmanci da suka haɗa da; kuɗi da ‘yankunnaye da sarƙoƙi da sauransu.

Ana yi wa taskira kirari da: “Taskira Asirin Mai Ɗaki. ”Don haka za a iya cewa, taskira, wani ɗan ƙaramin kwando ne da aka saƙa da kaba wanda mata ke amfani da shi wajen zuba auduga da mazari da alli don yin kaɗi (Sa’id, B. da wasu 2006).

Gajiran/Gajirami

Wannan shi ma wata ma’ajiya ce ta gargajiya wadda Hausawa, suke ginawa tare da jera su a ɗaki. Akan yi rami matsakaici kamar yadda tukunya ƙarama za ta shiga cikin ramin sai a layanta su a bango da ƙasa, sai kuma abinne amma bakinsu yana kallon sama, akan adana wake ko gyaɗa ko riguna ko zannuwa ko hatsi da sauransu, wasu ma har kuɗi suke ajiyewa (Tattaunawa da Maisalati Durɓindai).

Adudu

Wannan kuwa, ya kasance ɗaya daga cikin kayayyakin da Hausawa suke amfani da shi musamman wajen ajiye ko adana wasu hajoji da nufin kaucewa salwanta ko kuma lalacewa. Wata ma’ ajiyin sutura mai zurfi da kuma murfi wanda ake yi da kaba (Sa’id, B. da wasu 2006). Adudu wata fasahar Hausawa ce, wanda ake amfni da kaba da gazari wajen saƙa shi domin adana sutura domin kaucewa ɓarnar ƙwari.

Lefe

Mazaubi ne da ake saƙawa da kaba don kaɗar auduga ta zama zare. Yayin da Sa’id da Wasu (2006) suka bayyana shi da cewa: “Wani makai da ake saƙawa da kaba don saka ko ajiye kayan kaɗi ko zuba kayan aure”. Haka kuma, wannan ya sanya Hausawa suke zuba sutura a ciki don kai Toshi gidan su amarya kafin a yi aure.

Kuratandu

Kuratandu wani ɗan ƙaramin tandu ne ake yinsa da jemammiyar fatar akuya ko tinkiya ko wata ƙaramar dabbar domin sa kwalli da mishiyi da akan sa kwallin da shi. Sannan kuma a sa matashi haɗi da murfi domin gudun ka da ya zube ko kuma ya salwanta.

Akurki

Akurki ana saƙa shi ne da itacen geza, za a zubar da ganyayyakin da ke maƙale a jikin itacen, sai kuma a tsaga itacen gezar gida biyu ko uku a tsaye. Ana saƙa kamar yadda ake kife ƙwarya, ana yi masa ƙofa daga ƙasa, yayin da aka kammala sai a samo kashin shanu sai a baibaye shi ciki da waje.

Yana daga cikin kayyakin Hausawa na gargajiya da ake amfani da shi musamman wajen ajiye da kuma adana tsuntsaye nau’in kaji ko agwagi da zabbi da agwagi da makamantansu. Yayin da aka saka su ciki ko kuma suka shiga da daddadare sai a saka murfi a rufe ƙofar ta yadda wani abin cutarwa ba zai sami damar cutar da su ba irin su maciji ko muzuru ko cimola da makamantansu.

Cali

Wannan wani abu ne raga-raga, wanda ake saka tuluna ko ƙore da makamantansu. Wasu lokutan akan ɗora wa jaki idan za a kai su kasuwa. Sannan kuma a wasu wuraren cali kan kasance mazubin kayan amfanin gona kamar albasa ko yalo, ana saƙa shi ne da igiya, yana da ƙofofi don kayan su sha iska. Ana amfani da cali a ɗora kan jaki ko takarkari don ɗaukar kaya.

Taiki

Mazubi ne na jemamiyar fata wadda ake ɗinkawa, wadda za a ɗura tsabar gero ko dawa ko shinkafa wadda zai kwanta kan jaki ko takarkari mai siffar mangala domin kai kayan amfanin gona kasuwa ko kuma wurin da ake da buƙata. Akan zuba tsabar gero ko dawa ko rimi da makamantansu.

Kwatanniya

Kwatarniya wani matsakaicin mazubi ne wanda masu sana’ar ginin ƙasa suke samarwa. Ana samun taɓo da jangaggari da ruwa sai a haɗa a kwaɓa, sai kuma a samo wata tsohuwar kwatarniyar a mamaye bayanta da wannan taɓon da jangargarin da aka kwaɓa, ana bi ana bugawa kaɗa-kaɗan har ta zama ta yi kwafin ta farko, sai a bi a gyaggyara har ta zama abin da ake so.

Ana zuba ruwa musamman idan za a yi wankan jego, haka kuma ana amfani da ita wajen wanki ko wankin kalwa. Haka kuma ana ajiyewa dabbobi irinsu awakai da tumakai ruwan da za su sha idan sun dawo gida daga kiwo. Ana yi mata kirari da cewa: “Kwatarniya kin fi arfin roro”.

Akushi

Akushi kwanon da ake cin abinci ne da shi ne a gargajiyance, sai dai shi ana sassaƙa shi ne da gungumen itace, ana zuba abinci a cikinsa kamar tuwo da miya, kasancewar itacen mai kauri ne yakan sa abincin ya daɗe bai huce ba.

Ƙwarya

Ƙwarya ana samunta ne daga ɗan duma, yayin da ya zama babba ya riƙa. Bayan an ɗebe kayan amfanin gona, sai masu sana’ar fafar ƙwarya su raba ta biyu, inda za su fitar da totuwar da take cikinta, sai kuma su fafe ciki sarai  sannan a barta har ta bushe, sai kuma a sake fafewa yayin da za a fitar da dukkan wata totuwar da take cikinta.

Ita ma ana amfani da ita wajen adana kayyayaki masu yawan a gargajiyance, misali dawa ko gero ko wake ko deɓo hatsi daga rumbu, sannan kuma ana amfani da ita wajen shiqar hatsi idan an yi casa ko kusa zuba mararrakin tuwo idan an kwashe.

Tallen Miya

Maginan gargajiya na Hausawa su ne suke gina tukwanen ƙasa. Tallen tukunyar ƙasa, na daga cikin kayayyakin da ake amfani da su wajen adana ko ajiye kayayyaki wanda Hausawa suke saka suturarsu ko kuɗi ko ko kuma abinci domin gudun salwanta ko ɓata.

Kamar yadda, Sa’id, da wasu (2006). Suka tabbatar cewa, makai da aka gina da laka aka gasa don dafa abinci ko zuba ruwa ko ajiyewa wani lokaci ma da adanawa. Shi kuwa Talle, wata ƙaramar ‘yar ƙaramar tukunya ce da ake dafa miya a cikinta.

Ya kasance kamar tukunya sai dai, bai kai ga tukunya girma ba, da shi ake amfani wajen yin miyar abinci, yayin da aka gama miya akan ajiye ta saboda ka da ta lalace ko kuma ta salwanta wasu lokutan akan adana saboda akuya ko yaro ko wata dabbar ta zubar da ita.

Asusu

Wannan ya kasance wurin ajiyar kuɗi da ake ginawa a jikin bango ko ɗan kurtun yamɓu mai ƙaramar tsaga, ko gwangwani da aka yi masa ‘yar tsaga. Asusu wata ma’ajiya ce da Hausawa suke samarwa ta hanyar sarrafa ƙasa ta yumɓu haɗi da sauran kayyayakin samar da shi.

Za a yi masa ‘yar ƙofa kaɗan yadda hannu ba zai iya shiga ba, duk abin da aka zura cikinsa ya shiga ke nan idan har ana da buƙata sai dai a fasa ko kuma a ɗauki lokaci mai tsawo kafin wani abu ya fito, sannan kuma daga sama ana yi masa mariƙa ta ƙasa. Akan zuba kuɗi domin yin ajiya (Tattaunawa da Mukhtar A. Isma’ila).

Ragaya

Ita ma hanya ce da Hausawa suke amfani da ita wajen ajiye tare da adana kayayyaki domin gudun salwanta ko lulubewa. Sa’id, B.da Wasu (2006). Sun ce: “Ragaya ita ce maratayin ƙore ko kaya da ake ɗaurawa ko ajiye wani a jinkar ɗaki daga ciki, wanda kuma ake saƙawa da tufkarkiyar kaba ko yawa.” Ragaya ita ce wadda ake saka ƙoƙuna ko akusai a ciki, yadda za ta zama an sarrafa ta da kaba sannan a yi mata gida-gida ko kuma hawa-hawa musamman domin ajiyar wani abu.

Kula

Kula ita ce babbar butar ƙasa da ake zuba ruwan sha a ciki domin ya yi sanyi. Ta kasance tana daga cikin jerin kayayyakin ajiyar Hausawa na gargajiya. Ana yin ta da taɓo da jangargari da ruwa. Maginan tukwane da sauran nau’o’in sarrafa ginin ƙasa ne suke samar da ita.

Kula ita ce butar da ake yi da ƙasa, akwai ƙarama sannan kuma akwai manya, ƙananan su ne ake amfani da su wajen sayar da ruwan alwalla a kasuwannin ƙauyuka, Manyan kuma su ake zubawa ruwan sha domin ya yi sanyi, musamman a lokutan bazara yayin da ake tsananin rana. A lokutan sanyi kuwa akan ɗora ta a kan garwashin wuta don a sami ruwan xumi. (Tattaunawa da Muhammad Sani ).

Ƙaho

Ƙaho ya kasance wani abu ƙashi-ƙashi guda biyu da yakan fito a kan dabba, kamar saniya ko rago ko akuya ko barewa (Sa’id, B. da wasu 2006) musamman ma ƙahon rago ko kuma ƙahon wata dabbar daban, sukan sanya layun da aka rufa su da fata ko farin ƙyalle su rataya shi inda suke buƙata kamar a ƙofar gida ko a tsakar gida ko a binne domin yin kafi ko kuma wani muhimmin dalili, domin neman kariya daga al’ajanu ko ɓarayi da dai sauransu.

Adada

Wannan wata rumface wanda ake yinta a tsakar gidan Bahaushe, ana yin ta da gwafanni da bunu ko ciyawa, wasu lokutan kuma akan haɗa da zana da igiya da sauransu, akan ajiye kayayyaki irin su fatun buhuna ko kayayyakin aikin gona da suka haɗa da; magirbi da sungumi da garma da fatanya da gatari Har ila yau akan ajiye karbi da dai sauran kayyakin da ake da buƙata a ajiye (Tattaunawa da Kawu Mu’azu).

Batta

Wani ɗan kuttu ne na ƙirgi wanda ya ɗan ɗara girman kuratandu wanda ake zuba taba gari a ciki ( Sa’id, B. da wasu 2006). Shi ma yana ɗaya daga cikin kayayyakin Hausawa da suke yin ajiya haɗi da adanawa domin ka da su salwanta. Haka kuma matan Hausawa sukan yi ajiyar kayan kwalliya da sauran wasu abubuwa muhimmai, kamar tozali, gyatuma raɗau ko kuma aɗaɗa ko janbaki ko hoda ko jar koya da makamantansu.

Don haka Batta tana da siffa kamar haka, akan shirya da tsara ta tare da yenta kamar siffar adaka, sai dai da katako ko kuma itace, sai kuma a lulluɓe ta da fata wanda Dukawa wato masu sana’ar sarrafa fata suke samar da ita (Tattaunawa da Malam Gambo.)

Angara

Kamar sauran kayyayin ajiyar Hausawa, Angara ta kasance wata ƙaramar jaka ce mai kama da zabira ta wanzamai, galibi maharba ne suka fi amfani da ita, domin adana kayayyakin harbinsu kamar, ’ya’yan date da toka da tsakuwa da ashana da sauransu. Dukawa ne suke samar da ita, saboda ta kasance ta fata ta kowace dabba in dai ta kasance mai faɗi (Tattaunawa da Malam Gambo).

Akwatsa

Wani ɗan ƙaramin wuri ne da ake samarwa mai kama da kanta, sai dai bai kai kanta girma ba, wani lokacin ma ana yin ta daf da ƙofa daga cikin ɗaki ko kuma daga waje. Akan yi ajiyar kayyayakin buƙata kamar su guntun manguli da ashana da kuka da manda da kanwa da gishiri da barkono da sauransu (Tattaunawa da Sa’idu Nakande).

Bankaɗe

Yana daga cikin kayayyakin da Hausawa suke yin ajiya a cikinsa, sannan ya kasu gida-gida akwai bankaɗen tabarma da bankaɗen gado da bankaɗen lefe da bankaɗen mataki da bankaɗen faifai da sauransu. Hausawa sukan yi masa waƙa da cewa: “Bankaɗan lefe na ka zuba mini ba ni bari sallah ta wuce ni” (Tattaunawa da Adamu Isyaku).

Kuikuita

Wata hanya ce ta Hausawa da suke yin ajiya a ciki, ana yin ta da kaba, sannan tana da siffar kuttu, sai dai ba ta kai kuttu girma ba.  Kuikuita tana da ɗan zurfi kaɗan, tana da murfi, sannan akan yi mata ‘yar mariƙa kamar yadda jaka take. Akan adana kayan kwalliyar mata kamar ‘yan kunnaye da barima da’yan hanci da duwatsu da murjani da sarƙa da awarwaro da zobba da tagulla da azurfa da sauransu (Hira da Maisalati Durɓunde).

Salka

Wata sarrafaffiyar fata ce da mahauta kan yi wa dabba fiɗar zuga-zugi, inda za su zare fatar ba tare da an yanka ta ba, musamman daga wuya zuwa ƙasa. Yayin da su kuma Dukawa suke jeme ta, wato su kawar da gashin da take ɗauke da shi, sai kuma su rina ta don ta bayar da kalla.

Sai kuma a ɗaure dukkanin ƙofofin ƙafar ko a ɗinke su domin ka da abin da aka ajiye ko adana su zube. Akan ajiye muhimman abubuwa kamar ruwa da mai da hatsi da gari da sauransu. Sannan kuma a wasu lokuta matafiya ko kuma fatake  kan yi jagami da ita, ko kuma su ɗora a kan jakuna ko alfadarai (Hira da Maisalati Durɓinde).

Sanho

Shi ma yana daga cikin  kayayyakin da ake yin ajiya ko adanawa wasu muhimman abubuwa wanda al’umar Hausawa suke amfani da shi a cikin al’amuransu na yau da kullum.

Sanho wata saƙaƙƙiyar kaba ce da masu sana’ar saƙar kaba suke samarwa, yana da siffar saƙa irin takumkumi, amma ya kasance ba shi da ƙofofi ko raga irin ta takumkumi, ya kasance haɗaɗɗiyar saƙa ce irin ta mangala. Akan ajiye kayayyakin amfani gona kamar su gero da dawa da alkama da dankali da wake da sauransu (Hira da Abdullahi Madaki).

Kammalawa

Wannan takarda ta karkata akalarta ne a kan kayayyakin da ake amfani da su wajen adanawa ta hanyar gargajiya, inda aka kawo bayanansu da kuma yadda Hausawa suke amfani da su a lokacin da buƙatar hakan ta taso. Kayayyaki ne na gargajiya, kuma suna da inganci da sauƙin samuwa haɗi da sauƙin sarrafawa.

Amfani da waɗannan kayayyaki ya haifarwa Hausawa samun hanyoyi masu yawan gaske wajen adana kayayyakinsu domin amfanin yau da kullum. Takardar ta mayar da hankali kan kayyayaki da ake amfani da su wajen adanawa da kuma bayyanawa masu nazari da ‘yan baya masu tasowa su san su don ka da su wofantar da su.

Sakamakon Bincike

Bayan kammala wannan takarda. Babu aiki mai manufa da za a gudanar a kasa samun sakamakon da ya haifar ba. Daga cikin sakamakon da aka samu bayan kammaluwar wannan maƙala, sun haɗa da yadda aikin ya gano waɗansu hanyoyi da Hausawa suka bi cikin hikima da fasaha suka ƙirƙiri kayayyakin aikinsu waɗanda suka dace, kuma suka yi daidai da yadda za su yi amfani da su, ba tare da wata barazana ba.

Da farko, takarda ta gano cewa ta hanyar amfani kayayyakin da ake yin ajiya ko kuma adanawa ake samar da wasu abubuwan da suke taimakawa wajen taskacewa don gudun lalacewa ko salwanta. Misali, kamar sanho da randa da rami da makamantansu.

Haka kuma, takardar ta ƙara fito da sunayen wasu kayayyakin gargajiya masu amfani waɗanda ake samarwa, sannan kuma al’umma suke amfani da su don gudun ɓacewarsu. Misali kuikuito da salka da sanho da rumbu da makamantansu.

Haka kuma takardar ta gano cewa mutane masu sarrafa kayayyakin adanawa ko ajiyewa suna bayar da gagarumar gudummawa wajen kyautata al’adu da kuma haɓaka tattlin arziƙin ƙasa. Domin sakamakon amfani da su na samar da abubuwan gargajiya don amfanin yau da kullum.

Bayan nan kuma, takardar ta lalubo waɗansu kayayyaki waɗanda a yau Hausawa sunayensu kawai suka sani ko suke ji. Amma a da suna ganinsu tare da amfani da su yadda ya kamata. Misalin irin kayayyakin su ne irin su: zunguru da akwasa da tulu  da sauransu.

Bayan da aka ƙare wannan takarda, an gano cewa har ma gwamnati da sauran hukumomin gwamnati na sayen wasu kayayyakin da aka sarrafa na gargajiya, suna adanawa a gidajen adana kayan tarihi na jihar Kano da sauran jahohin ƙasar nan da  nuna su a wajen taron baje kolin al’adu ko lokatan nunin kayan amfanin gona da ma sauran tarurruka.

Shawarwari

Wannan takarda tana bayar da shawara ga wasu rukunnan al’umma da ƙungiyoyin cikn al’ummar ƙasar Hausa kamar haka:

Da farko, ana bayar da shawara ga al’umma, musamman waɗanda suke amfani da waɗannan kayayyakin a cikin gonaki da gidaje baki ɗaya, da su ci gaba da amfani da su. Dalili kuwa shi ne, rashin amfani da waɗannan kayayyaki zai iya janyo  sakaci da lalaci da karya gwiwar masu yin su wanda daga ƙarshe ma suna iya yin fatali da su baki ɗaya.

Haka kuma, ana bayar da shawara ga hukumomi da mahukunta, musamman gidajen tarihi da gidajen sarauta da cibiyoyin koyar da al’adun Hausawa da cibiyoyin ilimi na kwalejojin ilimi da jami’o’i na jihohi da na tarayya da su riƙa ba masana da manazarta ƙwarin gwiwa da goyon baya a duk lokacin da suka je yin irin wannan bincike a wurarensu.

Haka zalika, ana bayar da shawara ga ɗaliban ilimi, musamman matasa masu jini a jika da su tashi tsaye, tsayin daka, su ba da himma da ƙwazo wajen yin nazari da bincike dangane da abin da ya shafi irin wannan ɓangare. Dalili kuwa mafi yawan ɗalibai sun karkata ne a kan jigo da salo da sarrafa harshe. Abin, ya kamata mu fuskanci al’adunmu na gargajiya kar mu guje su mu faɗa ga na waɗansu.

Bayan haka kuma, wannan takarda tana shawartar masana da manazarta da su ƙara ba ɗalibai ƙwarin gwiwa dangane da yin nazarce-nazarce waɗanda suka danganci irin waɗannan al’adu musamman amfani da kayayyakin da ake adanawa, don ta yin haka ne za a gano waɗansu abubuwa da aka riga aka manta da su. Sannan a san waɗansu sababbi waɗanda ba a san da su ba. Amma hakan ba zai yiwu ba har sai  an zurfafa bincike a wannan fage. Sannan za a iya cim ma wannan buri.

Wata shawarar ita ce ga gwamnati da masu hannu-da-shuni da su tallafa wa masu irin waɗannan sana’o’i na sarrafa kayayyakin da ake amfani da su, a riƙa ba su tallafi na jari ko kayan aiki, za a samu ci gaban da ba a tunani.

Haka kuma, gwamnati ita ce ya kamata ta tabbatar da aiwatar da koyar da sana’o’in gargajiya a manhajojin ilimi tun daga matakin firamare har ya zuwa matakin jami’a, wannan zai ƙara haɓaka sana’o’in gargajiya da bunƙasa al’adu da tattalin arziƙi baki ɗaya.

Manazarta

Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Government Printing Press, Nigeria.

Akodu, A. (1985) A Comparative Study of The Traditional and Contemporary Arts of The Maguzawa of Kano and Kaduna states Ph.D. Thesis, Department of Fine Arts, Faculty of Enviroment Design. Zaria: Ahmadu Bello Uniersity.

Alhassan H. Da Wasu, (1982).Zaman Hausawa. Bugu na Biyu, Kaduna: Islamic Publication Bureau.

Bargery, G.P.(1934).English Hausa Vocabulary. London: School of Oriented Studies, University Press.

Bunza, A.M. (2006). Gadon Fexe Al’ada. Lagos: Tiwal Publication Company.

Sa’id, B. da wasu,(2006).Qamusun Hausa.Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Muhammad, M.S. (2020).Bahaushiyar Al’ada.Tetfund. Kano: Bayero University Press.

Soba, S. A. (2012). “Muhallin Bahaushe Jiya da Yau”.Kundin Digiri na Biyu da Aka Gabatar ga Sashen Harsunan Nijeriya.Sokoto:Jami’ar Usman Xanfodiyo.

MUTANEN DA AKA TATTAUNA DA SU

Lamba Suna Shekaru Sana’a Gari Rana
1. Saidu Nakande 60 Manoni Ɓangashe 20/1/2026
2. Ibrahim Abubuakar 65 Manomi Aku 21/1/2026
3. Mustapha Ibrahim 40 Maƙeri Gaya 2/1/2026
4. Malam Gambo 65 Baduku Gaya 13/1/2026
5. Tabawa Adamu 61 Sana’ar Kaba K/ Gabari 11/1/2026
6. Baba Sayyadi 43 Maƙeri Gaya 5/1/2026
7. Mukhtari A.Isma’ila 45 Magini Ƙwanadroso 11/1/2026
8. Dr. Abdullahi Madaki 62 Malamin Jami’a Gaya 6/1/2026
9. Kawu Mu’azu 57 Wanzami Tarauni 3/1/2026
10. Maisalati Durɓindai 58 Sana’arTukwane SRCOE 1/1/2026
11. Adamu Isyaku 68 Masanin Al’adu Gamoji 15/1/2026
12. Sadiya Sabo 60 Saƙar Kaba Aku 29/1/2026
13. Dauda Yusif 50 Manomi Gaya 26/1/2026
14. Muhammad Sani 65 Sana’ar  Fafa Shagogo 19/1/2026
    15. Mu’azu Adamu      72 Mai Unguwa Matamawa 20/1/2026

 

 

Danna nan don karanta Tarihin Dr. Magaji Ahmad Gaya (PhD)

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTarihin Garin Kudan
Dr. Magaji Ahmad Gaya
Dr. Magaji Ahmad Gaya shahararren malami ne a fannin harshen Hausa. Ya yi digiri na uku (PhD) a ɓangaren nazarin al’adu a jami’ar Umaru Musa “Yar Adua da ke Katsina. Haka kuma ya yi aikin koyarwa a wasu makarantun firamare da sakandare da kuma Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso. A halin yanzu yana koyarwa a Jami’ar Northwest, Kano Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya.