“Yawan jin motsin jariri a ciki babbar alama ce da take nuna cewa jariri yana lafiya, domin idan akwai matsala, to, raguwar jin motsinsa za ta iya zama ɗaya daga cikin alamomin matsalar. Amma ba ina nufin kowace raguwar motsin ce take nuna alamar matsala ba.
Sa’annan yanayin kwanciyar jariri a mahaifa, tsufan ciki, da kuma ɓangaren da mahaifa take su ne suke nuna ɓangaren da mai juna biyu za ta riƙa jin motsinsa kamar haka:
1. Idan ciki ya tsufa kuma kan jariri yana ƙasa (cephalic or vertex presentation), to, mai juna biyu za ta riƙa jin motsin jariri a sama ta wurin haƙarƙarinta ko kuma zuciyarta. Hakan yana faruwa ne saboda da ƙafafunsa yake shure-shuren, kuma ƙafafun suna kallon sama.
2. Idan ciki ya tsufa kuma kan jariri yana sama (breech presentation), to, mai juna biyu za ta riƙa jin motsin jariri a ƙasan mararta ta wurin mafitsararta, har ta ji kamar zai fito waje. Hakan yana faruwa ne saboda da ƙafafunsa yake shure-shuren, kuma ƙafafun suna kallon ƙasa.
3. Idan ciki ya tsufa kuma jikin jariri yana gicciye (traverse presentation), to, mai juna biyu za ta riƙa jin motsin jariri a gefen cikinta na dama ko hagu. Idan kansa yana gefen dama ne, to, za ta riƙa jin motsin a gefen hagu. Idan kuma kansa yana gefen hagu ne, to, za ta riƙa jin motsinsa a gefen dama. Wato duk inda ƙafafunsa suke, to, ta wannan ɓangaren za ta riƙa jin motsinsa.
4. Idan mabiyiya (placenta) tana maƙale a gaban mahaifa (uterus) shi kuma jaririn yana bayan mabiyiyar (anterior position), to, mai juna biyu ba za ta riƙa jin motsin jaririn sosai ba koda kuwa cikin ya tsufa, har za ta riƙa tsammanin ko akwai matsala ne. Sa’annan wannan shi ne dalilin da yake sanya wasu matan su daɗe ba su ji jaririnsu ya fara motsi ba. A gaskiya ba wai bai fara motsi ba ne, a a mahaifar da take gabansa ce take hana a ji motsinsa.
5. Idan mabiyiya (placenta) tana maƙale a bayan mahaifa (uterus) shi kuma jaririn yana gaban mabiyiyar (posterior position), to, mai juna biyu za ta riƙa jin motsin jaririn sosai koda kuwa cikin bai tsufa ba. Sa’annan wannan shi ne dalilin da yake sanya wasu matan su fara jin motsin jaririnsu tun cikin yana ƙarami.
Idan kuma mace ta ji kamar jaririnta ya dunƙule wuri ɗaya, to lallai ya dunƙule ɗin ne. Jariri yana yin kwanciya iri-iri a cikin uwarsa, kuma ba za ta iya hana shi yin kwanciyar da yake so ba. idan ya yi kwanciya irin ta mai jin sanyi, wat ya takure hannayensa da kafarsa wuri ɗaya, to, shi ne za ta ji ya dunƙule wuri ɗaya. Idan kuma ya warware, to, za ta ji dunƙulewar ta ba je. Wannan dunƙulewar ba matsala ba ce.
Allah ya Sauki duk Masu Juna Biyu lafiya.
Don karanta Menene Hiatal Hernia? Danna nan
Edita@rumasau-kallamu