Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Huɗu

0
30

Kwanci tashi cikin wannan rayuwar da Khadeeja take a gidan Mustapha har ta gama level 2 a karatunta ta shiga level 3, kuma shekararsu biyu kenan da Rashida mai aikinta. Zaman dai haka ake yinsa cikin dagewa da dagiya; idan Mustapha yana son buƙatarsa a wajenta sai ta ji kamar ba shi ba saboda yanda yake kwantar da kai ya samu buƙatarsa ta biya.

Amma kuma da zarar ta yi maganar karatunta ko wani abu da zai sa ta fita daga gidan ba tare da ta tafi da yara ba to sai ya nuna ɓacin ransa. Domin a halin yanzu kowa a danginsu ya santa da ‘yayanta domin tare ake ganinsu ko bikin wa ake yi. Gidan Mommy kuwa sun mayar da shi kamar gidan kakarsu, kuma da yake sun sami karɓuwa sai suka sake sakewa.

Karatunta yana tafiya daidai tunda ta saka auduga ta toshe kunnenta daga duk wata mita ta Mustapha, sai dai kawai kullum a gajiye take daga aikin gida da kuma aikin tunanin abinda za ta yi Mustapha ya daina nuna mata halin ko in kula. Yaran ba su saba ba ta matsala ba a da, amma zuwa yanzu duk tana neman ta rasa kansu; musamman Afaf da Nasreen.

Idan dai aiki ta saka su ba za su ce ba za su yi ba amma idan ba su ga dama haka za su yi kunnen uwar shegu da ita sai dai ko ta yi aikinta ko kuma ta sa Rashida ta yi mata. Sannan kuma yanzu Afaf ta ƙulla ƙawance da Samira ‘yar wajen Yaya Jidda, don haka kusan duk wani motsi na Khadeeja Afaf sai ta gayawa Samira wadda take kai wa uwarta rahoto na kai tsaye; don haka ne ma matsawar da Yaya Jidda take wa Khadeejan ta ƙaru.

Sai dai a yanzu ba wannan ne damuwar Khadeeja ba, babbar damuwarta ita ce rashin haihuwa. Tun bayan da ta yi ɓari a loakcin corona ko ɓatan wata ba ta sake yi ba ga shi ana neman shekaru biyu. Zaman gidan ba ya mata daɗi, ba ta jin daɗin yanda yaran suke mata, musamman Afaf wadda a da take tunanin sun zama ɗaya. Tana fatan ita ma Allah ya ba ta nata ‘yayan waɗanda za su kalle ta a matsayin uwa.

Ta riga shi kwanciya kamar yanda suka saba saboda yanda ta kula idan ta zauna jiransa su kwanta tare ita ake cuta tunda dole ta tashi kafin asuba ta shirya yara. Sai wajen sha biyu saura sanna ya gama abinda yake ya kwanta a kusa da ita, ta juya ta gyara kwanciyarta.

Yana kwance amma ya ɗaga waya yana chattinga kamar yanda ‘yan kwanakin nan ta kula kullum kafin ya kwanta sai ya yi chatting. Ta miƙe ta je ta yiwo fitsari, ta sha ruwa sannan ta dawo ta kwanta, zuwa lokacin ya gama chatting ɗin ya ajiye wayar yana azkar. Ta kwanta ta gyara kwanciyarta, bayan da ta kula ya gama azkar ɗin ta lalubo hannunsa ta riƙe cikin sanyin murya tace ‘Abban Afaf.’

‘Umm.’ Ya amsa yana kallonta duk da hasken da yake cikin ɗakin bai kai ya kawo ba. ‘Uhm, gaskiya ina son zuwa asibiti na ga gynae doctor.’ Ta faɗa tana wasa da hannunsa wanda ta riƙe. Ya riƙe hannunta a cikin nasa ya ƙara ba ta hankalinsa yace ‘Baki da lafiya ne?’

‘No ba wani specific issue. Ka san dai kwanaki nace maka ina son na je a duba a ga abinda yasa har yanzu ban sake samun ciki ba, kada na je wata matsala ce na yi ta zama gara na je a duba. Ya gyara kwanciya ya ƙara matsowa kusa da ita ‘Kina dai so ki ɗorawa kanki damuwa, har yanzu fa ba a yi shekaru biyu da ɓarin ba.

Iya wannan ya isa ya sa ki san cewa lafiyarki ƙalau, kawai Allah ne bai kawo ba tunda wancan ɗin ma ba asibiti kika je kika samo ba ko? Na sani, amma dai gaskiya ina so na je a duba ni ɗin na sami nutsuwa. Tunda ka ga idan na je aka ce min lafiyata ƙalau ai dawowa zan yi kawai na cigaba da addua’a, idan kuma matsala ce sa na nemi maganinta.’

‘Babu wata matsala kina dai son tonowa kanki matsalar. Ke yanzu ma da kike neman ciki ido rufe ya za ki yi da karatun? Tunda ga shi kin shiga level 3 kuma ke da kanki kina cewa ya fi wahala. Ya za ki yi da laulayi ga karatu? Ko har kin mata ne? Ai zai fi sauƙi idan ma dole ne sai kin je asibitin ki bari ki gama karatun kafin ki kwantar da kanki.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci, kowa da abinda yake tunani. Jimawa kaɗan tace ‘Ina son zuwa gaskiya, amma dai ina jin zan bari mu gama exams ɗin wannan semester in ya so kafin a koma hutu sai na samu na je. To Allah ya kai mu.  Tana son ta haihu duk da dai Mommy ma tace mata lafiyarta ƙalau amma ita gaskiya tana so ta je a duba ta.

Kuma yanda Mustapha yake gwada mata halin ko in kula idan ana maganar haihuwa ya sa gaba ɗaya ta fara tunanin ko bai damu da ta haihu ba; to ya ma za a yi ya so ta haihu tunda shi masoyiyarsa ta haifar masa yara har uku? Haka ta yi ta saƙe-saƙe tana juyi, sai gefin asuba sannan bacci ya ɗauke ta.

Kamar kullum yana shiga office ɗin yau ma damuwarsa ta yaye; musamman yanda ƙamshin turarenta ya yi wa ƙofofin hancinsa maraba bayan da ya shiga office ɗin nasa ya rufo ƙofar. Wannan ya tabbatar masa da cewa ta riga ta zo office ɗin wataƙila wani office ɗin ta je. Ya ajiye jakarsa a kan table ya ƙarasa ya zauna a kan kujerarsa cike da farin ciki.

Sabuwar sakatariyarsa Naja’atu Musa Bello; watanta uku da fara aiki amma soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanisu. Duk wata damuwa da Khadeeja za ta ɗora masa da ya shigo office ɗin ya ganta yake mantawa da ita, idan kuma an tashi daga office ko a ranakun da babu aiki ya kan je gidansu zance. Duk da dai manya ba su riga sun shiga zancen ba amma dai yana ji a jikinsa Naja’atu tasa ce.

Bai daɗe da zama ba ta turo kofar ta shigo, daga tsaye ta sakar masa kyakkyawan murmushinta wanda ba ya gajiya da kalla. ‘Ranka ya daɗe barka da shigowa.’ Ta faɗa tana juya ƙwayar idonta. ‘Good Morning my dear.’ Ya amsa yana ta faman murmushin da yake barazanar ƙarawa bakinsa faɗi.

Ta ƙarasa ta zauna a kujerar gabansa, sannan ta ɗauki file a kan teburin ta miƙa masa. Nan take ya buɗa ya fara karantawa yana mata tambayoyi tana yi masa bayani. Bayan sun gama ya ajiye file ɗin a gefe ya dube ta yace ‘To meye labari? Ta yi dariya ta sunkuyar da kai a kunyace tace ‘Komai normal. Good. So na yi mana order ɗin lunch ko? Don na san ko an ce ki zo mu je mu ci a waje ba kya son zuwa eateries, sai shopping ko?’

Ta yi dariya tace ‘Gara dai a yi order ɗin. Ba damuwa, ki yi mana order ɗin sai ki turo min account number na tura kuɗin.’ Yes Boss, an gama. Suka yi dariya gaba ɗaya. Tana shirin tashi yace ‘Yauwa, gobe ana open day a school ɗin su Afaf, please idan kika shigo around 10am sai ki je musu, ki jiyo min duk bayanansu da performances ɗin su.’

Ta gyara zama tace ‘Uhm, ok. But Madam ba ta nan ne ko ba ta jin daɗi? Ya gyara zama ya fara lilo a kujerar da yake kai yana kallonta sosai sanna yace ‘No, lafiyarta ƙalau but na dai fi son ke ki je ki jiyo min komai. Cike da farin ciki ta sake faɗaɗa murmushinta tace ‘Yes Sir, Allah ya kai mu. Kuma Allah ya sa kada ka sa yayata ta ba ni query saboda na shiga aikinta duk da dai ni ma ‘yayana ne.’

Ya yi dariya ‘Kada ki damu, ba ki da matsala da ita. Suka sake ɗan taɓa hira sannan ta fice ta koma office ɗinta cike da farin cikin yanda alaƙarsu take tafiya ita da ogan nata. Ba za ta taɓa bari Mustapha ya kufce mata ba don ta ga mijin aure. Ta gama degree ɗinta har ta yi masters, saurayinta na ƙarshe har sun zo gaisuwa haka kawai ya daina zuwa sai ji kawai ta yi ana bikinsa da ‘yar uwarsa.

Duk da ta san ba wasu shekaru ne da ita masu yawa ba domin shekarunta 28 kacal, amma dai ta san an matsu ta yi aure a gidansu; musammam ummanta wadda aikin ma so ta yi ta hana ta sai ta yi aure. Sai ga shi ashe mijin yana wajen aikin. A hankali suka saba, har suka kai yanzu da take jin za ta iya cewa ta fi matarsa sanin halin da yake ciki da inda yake a kowanne lokaci.

Don haka ma take jin cewa ƙwace shi a wajen Khadeeja kamar ƙwace goruba ne a hannun kuturu, domin tun yanzu tana jin ta fara samun nasara tunda kullum ita yake kawowa ƙarar Khadeejan sai ta ba shi haƙuri, ta riga ta fahimci irin zaman da suke yi da Khadeejan don haka ta gama shirya musu; lokaci kawai take jira.

Ƙarfe sha ɗaya take da lecture don haka sai da ta gama shirya yaran dukansu suka fita makaranta sannan ita ma ta ƙarasa ayyukanta ta shirya. Ƙarfe goma da minti biyar tana zaune a gaban mudubi tana gyara fuska ta tuna jiya da daddare Shukra ta ce mata Anty tace kowa ya zo da Mommy ɗinsa open day 9am to 11am sannan sai a zarce da sports.

Kuma idan dai ba ta manta ba ma Afaf ta gaya mata duk da section ɗin su Afaf ɗin daban da na su Shukra. Sai dai ba su yi maganar da Abbansu ba, bai gaya mata ita ce za ta je ko shi ne zai je ba gaba ɗaya ta manta ba ta tambaye shi ba. Ta miƙe ta ɗauko wayarta wadda take ajiye a gefen gado ta dannan masa kira.

Sai da ta kirawo sau uku duka wayar ba ta shiga ba, don haka ta yanke hukuncin idan ta fita sai ta fara tsayawa a makarantar tasu tukunna kada ta je sai ta wuce makaranta ya bugo waya yace ita ce za ta je ya jiƙa mata aiki. Nan da nan ta ƙarasa shiryawa ta saka jilbab ɗinta me kalar lilac sanna ta saka baƙin sneakers ɗinta ta sallami Rashida sannan ta wuce.

Tana zuwa makarantar kai tsaye ajinsu Shukra ta wuce, duk malaman nasu sun santa saboda zuwa ɗaukansu don haka ba tare da ɓata lokaci ba aka ba ta bayanan Shukra da kuma results ɗinta na CA. Tana gamawa ta ja hannun Shukra suka wuce ajinsu Nasreen inda nan ma aka haɗa mata komai, Nasreen tana cikin waɗanda za su yi wasan tsere don haka ba ta samu ta fita daga aji ba Khadeeja ta ja Shukra suka nufi secondary section don ta karɓo sakamakon Afaf da Habib.

Tun kafin su ƙarasa kofar secondary section ɗin ta hango Afaf tare da wata mata sanye da baƙar abaya da brown envelops a hannunta, suna tafe suna hira; ga dukkan alamu a dai malama ce a nan makarantar duk da ita Khadeeja ba ta taɓa ganinta ba. Da suka ƙara matsowa kusa Shukra ta zare hannunta daga na Khadeeja tana cewa ‘La, Anti Naja ce ga su nan ita da Yaya Afaf.’ Ta ƙarasa wajensu da gudu.

Da fara’arta ta cimmusu, suna haɗuwa ta ƙara faɗaɗa murmushinta cike da girmamawa tace ‘Sannu Anti. Cike da mamaki ita ma ta ɗan yage baki mai kama da murmushi tace ‘Yauwa, sannunmu. Ya aiki ya yaran?’ ta kula da yanda ta ke magana kamar da ƙyar don haka kafin ma ta ba ta amsa ta mayar da hankalinta ga Afaf tace ‘Yaya Afafa mu je na karɓo muku CA report ɗinku ke da Habib na wuce don ni ma school zan je.’

Ta ɗan ɗaga gira cikin halin ko in kula tace ‘Anti Naja ta karɓar mana ai, dama na su Shukra za ta je ta karɓa yanzu. Ta kalli Afaf ɗin sannan ta kalli malamar da aka kira Anti Naja tana mamaki tace ‘Me yasa? Anti ai da kin bar shi na zo gashi sun saka ki aiki. Ta kawar da kai ta ɗaga gira tana cewa ‘No ba wani aiki, ai Abbansu ne yace na karɓar musu.’

Ita ma Khadeeja ta dan zaro ido tace ‘Oh, ya zo kenan ko yaushe yace a karɓar musu?’ Afaf ta fahimci Khadeeja ba ta san Naja ba kuma ba ta ma san da zamanta ba, sabanin ita da ƙannenta waɗanda a cikinsu za ta iya cewa Shukra ce kawai ba ta san Naja ba ko kuma ta santa amma ba ta san wacece ita ba. Ta ɗan yi gyaran murya tace ‘Anti ba fa malamarmu ba ce, sakatariyar Abba ce kuma shi ne ya turo ta daga office ta zo mana open day ɗin.’

Mamakin Khaddeja ya ƙaru, ta sake ƙarewa Naja kallo na ɗan takaitaccen lokaci sannan ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa. Ta ɗan yi murmushi da gefen baki sannan ta kalli ƙasa ta ɗago suka haɗa ido da Najan wadda take mata kallon da ta kasa fassarawa sanna tace ‘Oh, ok, Umm.’

Kafin ta ce wani abu Habib ya ƙaraso wajen yace ‘Yauwa Anti kin ƙaraso? Dama ke nake jira; don Allah zo mu je ki cewa uncle ni ba na son basket ball team ya bar ni na shiga football team. Haka kawai wai saboda ni dogo ne sai na yi basketball. Kafin Khadeeja ta yi magana Najan tace ‘Au shi ne ba ka gaya min ba Habib, ai da ka gaya min na yi masa magana.

Dama Anti nake jira.’ Ya faɗa cikin halin ko in kula ya zari envelop guda ɗaya daga hannun Najan ya miƙawa Khadija yana dariya yace ‘Anti guess what? Ta ɗan yi murmushi yayin da suka bar Naja da baki buɗe, tace ‘What? Ya zaro takarda ɗaya ya miƙa mata yana cewa 38 naci a Hausa yau don haka yau da shawarma zan yi dinner ko?’

Ta karɓa tana dariya sannan ta ba shi hannu suka tafa tace ‘Iyye, ai dole ka ci shawarma tunda yau ka wuce gori. Haba ko kai fa, kullum komai ka ci A da B amma a Hausa ka dinga cin D da F. Ya miƙawa Khaddeja envelop ɗin yana cewa ‘To za ki ga Uncle ɗin? Tace ‘No, tunda yanzu ka ga kun riga kun fara games ina jin ka bari sai gobe sai na zo na gan shi.

Kafin nan mun tattauna a kan football da basketball ɗin kuma mun yi magana da Abbanka ko? Ya gyada kai ‘Eh, haka ne. Naja ta yi sauri tace ‘Idan kina sauri ne ai sai na je naga Uncle ɗin. Tace ‘No ba sauri nake ba, kamar dai goben zai fi dacewa kawai. Habib ya katse su yana miƙawa Khadeeja envelope ɗin yana cewa ‘Anti sai mun dawo, goben kya zo kawai.’ Ya wuce ya bar su a nan.

Naja ta miƙawa Khadeeja hannu tana cewa ‘Ki kawo na tafi wa da yallaɓai takardun tunda office zan koma. Ta ɗan yi murmushi tace ‘No ina ga gara ni na tafi masa da su tunda a gidansa zan kwana. Ta ɓata rai tace ‘Um, sai an jima. Ta wuce riƙe da takardun Afaf da suke hannunta Afaf ɗin tana biye da ita suna hira.

Khadeeja ta bi bayansu da kallo tana mamaki; to yaushe ya yi sabuwar sakatariya? Tunda da dai ta san sakatarensa namiji ne. kuma har yaushe sakatariyar ta kai matsayin ta zo wa yara open day har tana wani cewa a ba ta takardu ta kai masa? Tukunna ma; kamar dai yaran nan sun sa wannan sakatariyar, ita ce ba ta santa ba.

To kenan har ya yi introducing ɗinta a wajen yaransa a matsayinta na wa? Me yasa suka kwana tare bai ce mata tazo open day ba kuma bayan ya fita ma ya kasa kiranta? Wanda tunda ta aure shi duk wata harkar makarantar yara ita ce take zuwa kuma shi yake saka ta ta zo. To me yasa wannan ya sa sakatariya? Naja? Ba ta son ta yanke hukunci cewa akwai wani abu tsakanin Mustapha da Naja amma dai tabbas tana da tarin tambayin da zai amsa mata.

Sai da ta raka Shukra aji sannan ta nufi fita daga makarantar. Tun kafin ta gama fitowa daga cikin ginin makarantar zuwa farfajiyar wajen da ake ajiye motoci ta hango su, tana riƙe da hannun Afaf suna magana har suka ƙarasa bakin motar gefen direba ta sa mukulli ta buɗa motar; ta dan ja baya ta labe. Me take gani ne? Motar Mustapha? To shine ya kawo ta ko me? Tana nan a laɓe ta hango su; Naja ta buɗe motar ta zauna a kujerar direba sannan ta yi wa Afaf sallama ta ja motar.

Sai da ta karanta lambar motar a fili domin ƙara tabbatarwa motar Mustapha ce; kanta ya ɗaure gaba ɗaya. To me hakan yake nufi? Ya aiko sakatariyarsa ta zo wa yara open day kuma a motarsa. To haɗa kuɗi suka yi suka sayi motar a tare? Ko kuwa dai tsabar ƙauna ce ko rashin hankali ya sa suke sharing motarsa da sakatariya? Me yasa bai aiko ta a motar haya ba ko a motar office? Wato motar da ita idan dai makaranta za ta ko a rage mata hanya ba ta isa ya yi ba ita ce ya ba wa sakatariya take yawo a gari.

Kai! Gaskiya Mustapha ya raina ta. Ta yi sauri ta fito daga inda ta raɓe lokacin da ta hango Afaf ta nufo wajen. Ta yi mata sallama sannan ta wuce ta fice daga harabar makarantar. A bakin titi ta tsaya, motocin haya sai tsayawa suke ba tare da ta hau ba; gaba ɗaya ma ta manta inda za ta saboda yanda zuciyarta take zafi; me Mustapha yake nufi da ita?

Har ta juya za ta koma gida saboda yanda take jin ba za ta iya zuwa lecture ɗin ba sai kuma ta tuna idan ta je gidan me za ta yi? Rufe kanta kawai za ta yi a ɗaki ta yi kukan da ba zai mata maganin komai ba; don haka ta sake juyawa ta koma bakin titi ta hau motar BUK. Ta kalli waje ta tagar motar, ta yi murmushi ita kaɗai; wai ita ce a motar haya yayin da ga wata can tana yawo a motar mijinta.

Ta kawar da kai ta share ƙwalla. Ko da ta ƙarasa makarantar ta san an riga an yi nisa da lecture ɗin kuma ko ta shiga ma ta san babu abinda za ta gane, don haka kai tsaye ta wuce hostel ɗakinsu Rahma inda suka saba zuwa su huta; duk da dai ta san suna wajen lecture amma ta san inda suke ajiye mukullansu. Tana shiga ɗakin ta yi watsi da kayanta ta faɗa gadon Rahma ta kwanta ta fashe da kuka.

Sai wajen ƙarfe ɗaya da kwata sanna suka shigo ɗakin suka same ta a kwance ta ci kuka ta ƙoshi. Suna shiga Farida tace ‘Haba Malama, tun ɗazu muke kiranki a waya kin ƙi ɗaga wa ashe kina nan abunki. Suka ƙarasa suka faɗa kanta Asiya tace ‘Ko dai abun ya zo ne a tanadi goro da ledar amai. Ta sake fashewa da sabon kuka.

Suka yi tsuru-tsuru. Rahma ta shafa bayanta tace ‘Kawata kina faɗar mana da gaba fa, don Allah me ya faru? Ko Babe ba shi da lafiya ne? Haka suka yita jero mata tambayoyi, ita kuwa ta yi banza da su har suma suka gaji suka yi shiru, suka zauna kawai suna jiranta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ba su labarin abinda ya faru.

Rahma tace ‘kada fa na yi ashar ƙawata, kut! Wannan wanne kalar wulaƙanci ne mutumin nan yake miki? Farida tace ‘Motar da yake ƙyashin ɗaukanki ya je ya ba wa budurwa ko ma karuwa take yawo a titi? Lallai an gaida uban Afaf. Rahma tace ‘Gaskiya idan ya dawo yau ya kamata ya yi miki bayani na ganewa, duk da babu wani explanatin da zai sa na yarda babu wani abu a tsakanishi da ita ba sakatariya ba ko DG ce wallahi.

Ya yi miki bayani kuma kema ki karanta masa; wannan ai zubar da mutunci ne kina yawo a motar haya wata side chick tana yawo a motar mijinki? Mijinki na sunna fa, Haba! Gaskiya dai ya kamata ki san yanda za ki yi ki ƙwaci kanki a hannun mutumin nana tunda shi ga alama bai san mutunci ba.’

Amina tace ‘Don Allah ku bar ta ta bi abun a hankali. Ta kalle ta rai a ɓace ‘A hankali Amina? Shi a hankali kika ga yana yi min? Ni budurwarsa take cewa wai na kawo takardun yara ta kai masa saboda tsabar samun waje? Haba mana! Farida tace ‘Toh shi dai na gani, aure ai ba hauka ba ne. Wallahi ya kamata ki dage ki gaya masa abinda yake ranki tunda dai an daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa, ai ba siyo ki ya yi a bakin rimi ba da zai mayar da ke kamar wata sokuwa.’

Amina tace ‘Don Allah ku bari a bi abun a hankali, miji fa ba kamar saurayi ba ne haba!’ Rahama ta ja hannun Amina tace ‘Taso ‘yar uwa mu nemo abinci wannan batun na masu aure ne ba namu ba kin ji. Haka ta wuni a makarantar nan Amina tana ba ta baki yayin da Farida da Rahma suke ƙara jaddada mata ya kamata ta ɗauki mataki idan ba haka ba rainin zai wuce haka. Sai bayan la’asar sannan ta kwaso kayanta ta dawo gidan.

Wunin ranar haka ta ƙarasa shi cikin ƙunci, sai da ta cewa yara ba ta da lafiya sannan suka ƙyale ta don kowa yana so ya ba ta labarin sports day. Rashida ce ta ƙarasa duk wata hidimar gida da ta yara, har abincin ma da ba ya so Rashidan ta girka yau cewa ta yi ta girka don a yanda take jin ko ta dafa ba zai yi daɗi ba.

Sai bayan sallar magriba sannan ya dawo gidan, bayan ya gama hayaniya da yara ya wuce ɗakin ya same ta. Tana kwance ba ta ko juyo ta kalle shi ba don haka ya yi zaton bacci take yi. Sai kawai ya kintsa ya fice daga ɗakin. Ba ta son yi wa yaro alƙawari ta karya don haka tun da ta dawo ta sa Rashida ta haɗa mata duk wasu kayan da take buƙata na haɗa shawarma sanna ta kwaɓa mata fulawar, yanda idan ta fito bayan isha’i sai ta haɗa shawarma kamar yanda ta yi wa Habib alƙawari idan ya yi passing Hausa.

Suna zaune shi da yaran ta wuce su ta shiga kitchen, nan da nan ta fara ƙoƙarin ɗorawa. Tana daga kitchen ta jiyo yana amsa waya yana kwatancen gida; ta ja tsaki a fili tana fatan Allah ya sa ba baƙo zai yi ba don ko me zai yi ba za ta gaisa da wani baƙo ba balle ta ba shi ko da ruwa. Sai dai ya yi duk abinda zai yi. Kafin ta gama wannan tunanin ta ji shi yana cewa yanzu zai fito, inda ba tare da ɓata lokaci ba ta ji fitarsa.

Jimawa kaɗan ya shigo da leda ya wuce ya same ta a kitchen tana yayyanka fulawa za ta fara gasawa. Ya miƙa mata ledar yana cewa ‘Ga wannan shawarma ce; sakatariyata ce Naja ta aiko delivery man ya kawo a ba wa yara. Sai ki duba ki zubo a tray mu ci don na ji kamar da yawa’Ta kalle shi da jajayen idanuwanta waɗanda suka koɗe saboda kuka da tsabar mamaki; ta yi murmushi mai ɗaci sannan ta kashe wutar abinda ta ɗora a wuta ta nufo shi yayin da ya miƙa ledar a zaton za ta karɓa.

Ta bigi kafaɗarsa ta wuce ta shige ɗaki ta bar shi a nan tsaye. Ya bi bayanta da kallo cike da tsananin mamaki saboda Khadeeja ba ta taɓa yi masa irin wannan wulakancin ba; kuma a gaban yara don duk biyo shi suka yi da suka ji yana maganar a juye a ci. Nan take ya ajiye ledar kan sink sanna ya bi bayanta ɗaki; yana shiga ya same ta a tsaye a gaban mudubi tana cika tana batsewa kamar ma jiransa take yi.

‘Wannan wane irin wulaƙanci ne ina miki magana za ki yi min tsaki a gaban yara saboda raini.’ Ya tambaya cikin jin kai da isa. Ta kalle shi ta ɗauke kai tana murmushin takaici tace ‘Ji na yi kamar zagina ka yi. Kallon takaicin da yake mata ya koma na mamaki, ya tsare ta da ido kuma ita ma ta ƙi ɗauke nata idon. Yace ‘Ni na zage ki? Ko kuwa dai ke kika zage ni?’

Ba tare da ta ba shi amsa ba tace ‘Wacece Naja Mtseww!’ ya ja tsaki sannan ya cigaba ‘Sakatariyata ce; shi ne kike nema ki zage ni saboda nace ta kawowa yara abu? Ba ka gaya min ka mayar da ita wakiliyarka a makarantar yara ba, har sai da na je musu open day sannan sai na ganta wai kai ka tura ta. Har tana cewa wai na ba ta takardun yara ita kace ta karɓo.’

‘Eh, ai ni nace ta karɓo tunda na fita ban gaya miki ba. Kuma ka kasa yi mi waya kamar yanda kafin yau duk abinda kake so a yi na yaran kake min waya ko da ina sama jannati ne na je na yi? Ya fara hasala saboda yanda take maganar a tsiwace ga wani kallon raini da take masa.

‘Ba fa na son wulaƙanci khadeeja; ni na tura ta ta karɓo ko ban isa ba ne? Na zata za ki yi murna tunda kullum cikin ƙorafi kike da mitar hidimar yaran saboda kina gani ba ke kika haife su ba, ke naki karatun ne a gabanki. Ta yi murmushi tace ‘Ka isa har ka yi yawa, kuma alhamdulillahi tunda an sami mai karɓa ta yanzu kam zan huta da wasu abubuwan. Kuma na gane ni ce ban isa na shigar maka mota ba shi yasa ita da kake ganin mutuncinta ka koya mata mota har ga shi nan ta kai ta ɗauki motarka ta fita yawo.’

Ta ɗaga ƙafa za ta shige banɗaki sai kuma ta tsaya ta kalle shi suka haɗa ido sannan tace ‘Bayan hidimar yaran sai kuma wacce hidimar take maka? Ko ma dai ka aure ta ne ni ce ban sani ba? Ba fa na son iskanci Khadeeja! Kina ji nace miki sakatariyata ce kike wannan maganar banzar. Na aike ta don haka na ba ta mota ta ta je ta dawo, shi ne kike wannan rashin kunyar?

Idan da kina hidimar yaran ba tare da ƙosawa ba ai babu wanda zan nema. Na san idan na gaya miki sai kin yi mita don haka na nemi wadda za ta yi cikin walwala na saka ta, sai dai duk abinda za ki yi ki je ki yi amma idan kika zage ni wallahi ba za ki ji da daɗi ba. Ta yi murmushi ‘Hmmm! Ka fi ƙarfin zagi yallaɓai, amma tabbas ka yi yanda kake so don haka ni ma zan yi yanda nake so.’

Ta juya ta shige banɗaki ta turo ƙofar ta bar shi nan tsaye. Haka ya gaji da tsayuwa ya juya ya fice daga ɗakin; tana jin fitarsa ta fito ta saka mukulli ta kulle ɗakin ta bar mukullin a jiki ta koma ta kwanta. Tun a office Naja’atu ta sanar da shi haɗuwarsu da Khadeeja, kuma ita kanta sai da ta nuna rashin jin daɗinta a kan ya san Khadeeja za ta je ya tura ta.

Sai da ya yi ta faman ba ta hakuri sannan ya samo kanta. Bai taɓa zaton Khadeeja za ta ba shi matsala, don ya zata idan yace mata sakatariyarsa ce za ta fahimce shi, yanzu ga shi ita ma Khadeejan so take ya lallashe ta. Yana da niyyar auren Naja don sun ma yi magana da Alhaji kwanan nan ma za a kai kuɗin aure; kawai dai bai shirya gayawa Khadija ba saboda bai shirya ba, ya fi so sai magana ta tsaya an kusa biki sai ya sanar da ita.

Kafin lokacin ya gama gininsa sai su tashi su koma don a can yake so amarya ta tare. Yanzun ma kuma da hakan ta faru ba gaya mata zai yi ba, idan ta gama fushin nata ya san me zai gaya mata. Tun yana saka rai za ta buɗe ƙofar ɗakin har dare ya fara yi ba ta buɗe ba, yara har sun gaji da tambayarta. Haka ya sa Rashida ta ba su abinci sannan ta taya su suka shirya suka tafi suka kwanta, shi ma ya shiga ɗakinsa ya kwanta yana sauraron lokacin da zai ji motsinta.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Uku

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th Nuwamba 2025
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyar
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.