Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Shida

0
79

Tun wajen 12pm ta nemi izini a wajen aikin nata ta fice, kai tsaye gidansu ta nufa. Ta ci sa’a ta sami Mommy da Yaya Mama suna zaune a parlor suna hirarrakinsu. Bayan sun gaisa Khadeeja ta dubi Yaya Mama tace ‘A nan kika kwana Yaya. Ta yi dariya tace ‘Ga jakata a kusa da ni kina kallo amma kike min wannan tambayar, to ni yanzu ma zan tashi saboda 2pm zan ɗauko yara a makaranta sannan mu wuce gidan.’

Ita ma ta yi dariyar, ta umurci Hafsa da ta shiga ɗakin Nabila ko ta je kitchen wajen masu aikin gidan ta zauna. Tun kafin tace wani abu Mommy ta dube ta tace ‘Lafiya dai na ganki kamar a fusace, sarkin rigima. Ta zumɓura baki ta sunkyar da kai tana kallon hannunta kamar me ƙunƙuni, sai da ta gama zumɓura bakin sannan cike da takaici tana ƙoƙarin danne hawayen da ya taso mata tace ‘Mommy ni Mustapha zai mayar ‘yar aiki, kuma Baffa ya goya masa baya.’

Mommy ta gyara zama ta fuskance ta sosai tana kallon fuskarta da mamaki sannan tace ‘Ban gane ba, kuma me kawo Baffanki a cikin mayar da ke ‘yar aiki? Shi Mustaphan me ya yi miki? Tana buɗe baki za ta yi magana hawaye ya ƙwace mata, ta sa bayan hannunta ta goge sannan ta labartawa Mommy abinda ya faru.

Zuwa lokacin hawayenta ya gama ƙwacewa yana zuba kamar ana zubar da ruwan famfo, Mommy ce ma take ƙoƙarin goge mata. Tace ‘Mommy yanzu shikenan haka zan yi wata tara ina mata hidimar gida tana kwana da miji, bayan ni haka na yi nawa laulayin ko tausayina ba ya ji. Ko haihuwar Hammad fa ana gama suna dole na miƙe na koma hidimar gidan saboda ban ma ga fuskar cewa ba zan iya ba.

Amma yanzu saboda ya auro ‘yar gwal shi ne zan karɓar mata aiki ita kuma ta yi laulayi. Yaya Mama tace ‘Ni fa gaba ɗaya ban gane ba. To ke me yasa ba kya zuwa ɗakin kike barinta ta je, ai da sai ki je ki yi kwanciyarki a can ki ga ta inda marasa kunya za su kwana tare.’

Kafin ta yi magana Mommy tace ‘Gaskiya ni ma dai ban gane dabarar yin hakan ba, ai ɗakin ya kamata ki gyara ki tare har sai kin gama kwananki. Ta sa bayan hannunta ta goge hawayenta sannan tace ‘Mommy ba zan iya ba, ya kwana da wata matar a kan gadon sannan ni ma ya kwana da ni a kan wannan gadon.

Wataƙila ma da ya yi aurensa ba tare da ya ci min mutunci ba abubuwa da dama za su zo min da sauƙi, amma gaskiya ba zan iya ba. Tunda ko bayan ta tare ranar da zan karɓi girki bayan da ta gama kwana takwas ɗinta na shirya tsaf zan shiga ɗakin, amma har magriba ba ta fito daga ciki ba. Lokacin shi kuma ya riga ya fita.

Don haka na ƙyale ta na shirya masa abincin dare tunda na gama kintsawa. Amma yana dawowa ko kallon abincin bai yi ba ya same ni wai tunda ina jego na ba shi kwanakin ya kai wa amaryarsa in ya so idan na yi arba’in sai a fara rabon kwanan. Kin ga kenan ita ta riga ta san ba zai ba ni kwanan ba shi yasa ta ƙi fita ma daga ɗakinsa.

Daga wannan lokacin ɗakin da me ɗakin suka ƙarasa fice min daga rai gaskiya. Idan yana buƙata ta ya same ni a ɗakina, kuma yana zuwa ɗin. ’Mommy wadda take binta da kallo tana jijjiga kai tace ‘Lallai Mustapha, ni na rasa ma me zan ce. Ni fa mamakin da nake Baffanki ko gaya min bai yi zai je ba balle da ya dawo ya gaya min, wataƙila jiya bayan ya fita da magriba Mustaphan ya yi sa’a ya same shi a gate suka gama magana.’

Yaya Mama tace ‘Hmm! Ai komai daɗinki da miji idan dai wata macen ta gifta to sai abinda kika gani. Watan haƙurinki ne ya kama har ya gama yayinta. Mommy tace ‘To yanzu ya za a yi? Kin ga Baffanki ya riga ya sa baki a maganar ba tare da kin gaya masa ainahin abinda yake faruwa ba.

‘To Mommy ya za ayi na yi masa duk wannan bayanin ya gane, ai ban ga alamar zai ma gane ba tunda ko a lokacin ma yace amfanin mata biyu kenan ɗaya ta taimakawa ɗaya. Kuma ya za a yi na zauna ina gaya masa Mustapha yana satar min kwana saboda na ƙi zuwa ɗakinsa? Umm, haka ne kuma. To Allah ya kyauta.

Yanzu kam sai dai ki yi haƙuri a ga abinda hali zai yi tunda dai babu wanda zai je ya kwance maganar Baffanki. Ina ga kula da yaran wanda kika yi a baya bai kashe ki ba ba na jin na wata tara nan gaba zai dame ki. Haka suka zauna suka yi ta ba ta hakuri; sai daga ƙarshe Yaya Mama tace ‘Kuma ke ma idan kin gaji kawai ki yi pretending ki kwanta masa, wallahi da kaina zan zo na taho da ke na kawowa Mommy ta yi jinyarki idan kin huta kya koma.’

Mommy ta kai mata duka tana cewa ‘Allah ya shirye ki yayar kwabo. Suna nan zaune wajen 1:30pm Baffa ya shigo gidan da sallama, bayan ya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwa ya dubi Mommy tana zaune a tsakiyar su Khadeeja yace ‘Gulmar wa kuke yi suka saka ki a tsakiya haka. Ita ma dariyar ta yi tace ‘Ba dai gulmarka muke yi ba.’

Yaya Mama ta yi musu sallama ta fice yayin da Khadeeja ta miƙe ta nufi ɗakin Mommy ba tare da tace komai ba. Baffa ya bi bayanta da kallo sannan ya yi dariya ya dubi Mommy yace ‘Wannan iya rigimar ƙarata ta kawo ko? Ta harare shi tace ‘Ashe ka san ka yi mata laifi? Ya yi dariya yace ‘Rabu da ita da-Allah, ya za a yi a ce mutum yana da mata biyu a ce ɗaya ba za ta karɓi ɗaya aiki ba idan ba ta da lafiya? Ai ita ma ba ta so a zauna lafiya ba.’

Nan ta ƙara yi masa bayanin yanda zaman nasu yake, sai dai ta kasa gaya masa cewa Mustaphan yana ba wa Naja kwanan Khadeeja saboda Khadeejan ba ta yarda ta je ɗakinsa. Yanda ta san shi ta san tabbas ba zai ɗauki wanna ba, tunda shi ma tashi uwar har ta koma ga Allah turaka take zuwa ranar kwananta.

Haka dole Khadeeja ta haƙura ta cigaba da hidimar gida da ta yara. Shi ma Mustapha da ya gama zagaye-zagayen haka ya same ta a ɗakinta yana nuna mata jin daɗinsa ganin yanda take kula da yaran sai dai baya jin daɗin yanda idan ta jera abinci take komawa ɗaki ta bar su shi da ‘yayansa.

Duk yanda ya so ta ba shi haɗin kai su tattauna maganar ta ƙi, da ya dame ta da zance ma sai tace ‘Don Allah ka bari! Kai dai ba so kake na cigaba da hidimar gidanka da yaranka ba amaryarka tana hutawa? To ai ina yi ko? Ina ga duk a inda na zauna na ci abinci ma wannan bai kamata ya zama damuwa ba tunda dai ku kun ci naku.’

Kafin ya ba ta amsa ta fice ta bar masa ɗakin. Dole ya haƙura ya zuba mata ido tunda dai tana yin abinda yake so kuma duk ranar da ya kai mata kwananta ba ta hana shi buƙatarsa.

Da fari lokacin da Mustapha ya ƙara aure Khadeeja ta ga ‘yan uwansa ba sa wani damunta ta yi zaton tunda an mata kishiya sun fita harkarta. Sai dai tunda suka ji labarin Naja tana da ciki sai suka kama zarya gidan; babu yanda za a yi Yaya Jidda ta yi sati ba ta zo gidan ba. Haka za ta taho da girki a flask wai Hajia ce tace a kawo wa Naja saboda kwaɗayin mai ciki.

Ga shi idan ta zo a wajen Najan za ta sauka, sai dai idan Khadeejan tana nan ta shiga su gaisa sai ta koma wajen Najan. Sai kuma ta yi ta aiko yara; a ba ta abinci. Idan ta cinye kuma tace a ba ta wani ɗan abun taɓawa. Ranar da ba ta zo ba kuma sai a turo yaranta da abincin; haka za su zo ta wuni surutu da hidima da su ba ta taɓa jin wani yace Hajia tana gaisheta ba.

Kuma shi ma Mustaphan yana kallo ana yi amma bai taɓa cewa komai ba; sai dai yawan godiya da za ta ji shi yana yi wa mutan gidan nasu. Haka ta kawar da kai ta cigaba da duk wannan hidimar tana ganin rawar kai kala-kala. Haka ta cigaba da dagewa har Allah ya sauki Naja lafiya, aka sami yarinya mace wadda tun ranar da aka haihu Mustapha ya yi mata huɗuba da suna Rukayya.

Ba su tsara za ta tafi gida ba don haka sai aka kawo ƙanwar mahaifiyarta Alawiyya wadda suke kira da Anti Wiyya ta zo yi mata zaman daɓaro. Tun Khadeeja tana saka ran za ta ji Mustapha yace zai haɗe mata kwanan saboda Naja tana jego har dai ta fitar da rai. Ranar da aka kwana takwas da haihuwa ranar ta kama kwanan khadeeja ne sai dai a daren ranar za ta fita daga girki.

Da yake a ɗakinta suka kwana a nan yake shirin fita office; musamman tunda banɗakin ɗakinsa ya kwana biyu rabon da a wanke saboda Naja ba za ta iya wanke wa ba kuma Khadeeja ta ƙi ma shiga ɗakin; ga shi kuma yana ƙyashin ya saka Afaf ta wanke tunda ba ya son damuwarta. Yana zaune a gaban mudubinta yana shafa mai ta fito daga wanka, ta ɗauki kayan shafawarta ta koma gefen gado, suna yi suna taɓa hira.

Jimawa kaɗan tace ‘Yauwa, tazarce za mu yi ko? Sai na haɗe kwanakin tunda Naja tana jego har zuwa ta yi arba’in ko? Ya ɗan yi dum, alamar maganar ta shammace shi; tun ranar da Naja ta haihu ta gaya masa ba za ta bayar da kwananta ba saboda ko ba za ta iya biya masa buƙatarsa ba tana so ya kwana da su ita da Baby, in ya so kwana biyu sai su haƙura.

Ya riga ya amsa mata hakan domin shi ma hakan ya yi masa; duk da dai shi ba mutum ne mai son jarirai ba domin ko ɗaukan yaro ba ya son yi har sai yaro ya iya zama sosai. To amma dai tunda ta nuna tana so shi ma sai ya ji hakan ya yi masa ko hira ce sa yi, musamman da yake bai taɓa tsammanin Khadeeja za ta nemi wani ƙarin kwana ba duk da ita ta ba da nata kwanan an ba wa Najan.

‘Um, no ina ga ba haka za a yi ba. Na riga na yi magana da ita amma ba ta ba da kwanan nata ba, tunda kin ga ke ma tambayarki na yi kika bayar ba tare da na yi miki dole ba. To ita ba ta bayar ba, don haka sai a cigaba da kwana bibbiyun kawai.’ Ya faɗa cikin in-ina yana satar kallon Khadeejan ta cikin mudubi.

Sai da ta yi da gaske sannan ta haɗiya malolon da ya tokare mata maƙogoro; duk da dama hakan ta sa rai zai faɗa amma sai da abun ya yi mata ciwo. Ita ba ta ma yarda Naja ce ba za ta ba da kwananta ba, ta fi yarda shi ne dai ba zai iya ba ta kwana arba’in ba ba tare da ya ji ɗumin rabin ransa ba.

Ta daure ta yi murmushin yaƙe sannan tace ‘Allah sarki haka ne kam, to babu damuwa Allah ya raya mana Rukayya ita kuma mai jego Allah ya ƙara mata lafiya. Shikenan ai tunda ta haihu lafiya idan ta karɓi kwana yau to ta haɗa da sauran hidimar gida da yara da nake yi ni ma na samu na huta.

Ya yi shiru da bakinsa a buɗe yana kallon Khadeejan ta cikin mudubi; to a gaban Antin tata zai sakar mata aikin gida da na yara bayan ga ɗanyen jego sannan kuma ga Khadeejan tana kallo? Kuma a ce ita ce za ta tashi ta shirya masa yara, duk da dai kusan sun iya shirya kansu amma dai idan ba a tsaya a kansu ba haka za su yi ta shiririta har su makara.

Ga shi Afaf ta shiga SS 3 yanzu tun 7:15 am ake tare su makara. Ya san idan dai ba a tsaya a kansu ba to kullum sai dai ya dawo da Afaf. Ya rasa ma me zai ce mata, domin ya san kusan ko me yace tana da amsar ba shi kuma ya tabbatar fitinar da ba ta yi ba ce a lokacin da Baffanta yace ta dinga taya Naja aiki take shirin biyan bashinta yanzu. Ta miƙe ta kwashi mayukanta da ta gama shafawa ta ƙarasa gaban mudubin ta ajiye.

Ta ɗan tsaya daga gefensa tana kallonshi fuskarta cike da walwala kamar ba yanzu ta haɗiye ɓacin rai ba, tace ‘Kuma ni na yafe nawa kwanan ka haɗa mata, idan kuka yi arba’in sai mu cigaba da rabon. Ka ga ita da Baby suna buƙatar lokacinka da kulawarka sosai a waɗannan kwanakin. Ta wuce ta nufi gaban wardrobe domin saka kaya.

Yana nan zaune a gaban mudubin ta shirya ta fice ta bar shi a ɗakin; nan da nan ta haɗa masa breakfast ta jera a kan table sannan ta dawo ɗakin ta same shi ya riga ya gama saka kaya. Tana tsaye daga bakin ƙofa tace ‘Na yi serving breakfast. ‘Ok.’ Ya amsa. Ta juya ta fice ya biyo bayanta. Suka zauna tare suna cin abincin. Har suka ci kusan rabin abincin babu wanda yace wani abu; kowa da abinda yake ransa.

Ya ajiye kofin shayinsa bayan da ya kurɓa sannan ya ɗauki fork ɗinsa ya tsikari dankalin baturen da yake gabansa, ya ɗan ajiye fork ɗin ya kirawo sunanta a hankali kamar ma ba ya so ta ji kiran. Ta ɗaga kanta daga kallon kwanon abincinta ta amsa tana kallonsa. Ya yi gyaran murya sannan yace ‘Um, da-Allah ki yi haƙuri ki cigaba da girki a ƙalla har zuwa lokacin da Antin Naja zata gama yi mata wanka ta tafi.

Tunda kin ga ga Hafsa nan tana taimaka miki kuma na san Afaf ɗin ma yanzu duk abinda kika gwada mata za ta iya taya ki da shi. Saura kaɗan dariya ta ƙwace mata; wato yanzu Afaf ta kai ta taimaka wajen girki kenan tunda ya auro matar so? Ashe ma ya san kunya tunda ga shi ba ya so ya ji kunyar iyayen Naja.

Ta ajiye cokalinta ta kurɓi shayinta sannan tace ‘Don Allah Abban Afaf mu bar wannan maganar, hidimar gidannan ta wata takwas na karɓar mata. Ai na yi ko? Yanzu sai ta cigaba daga inda ta tsaya. Kwanan kuma da nace na ba ta da gaske nake, ku je ku yi jegonku na masoya kwana arba’in; wataƙila dai a kwankin da suka kama nawa ne na yi aikin gidan idan ina nan in ya so ita sai ta kwana da angonta.’

Cike da jin zafin abinda ta faɗa yace ‘Khadeeja ni kike gayawa wannan maganar? A cikin abinda ta faɗa ba ta san menene ya ɓata masa rai haka ba tunda ita dai a iya saninta ba rashin kunya ta yi masa ba, amma ta ga ya fusata yana faman yi mata muzurai. Ita da ya kamata a ce ita ce ranta ya ɓaci haka saboda nauye-nauyen da yake nema ya ɗora mata waɗanda ƙarara suke nuna rashin adalci.

Ta kalle shi ta kawar da kai tace ‘Allah ya ba ka haƙuri. Ta kurɓe ragowar shayinta ta miƙe da kofin da kwanonta ta wuce kitchen. Tana ajiye kwanukan ta fito ta wuce ɗakinta, tana turo ƙofar ɗakin hawayen da take riƙewa suka ƙwace mata, ta ƙarasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi. Ta zubawa mudubin ido tana kallon yanda hawaye suke fita daga idanuwanta suna gangarewa ta kan kumatunta.

Wai me Mustapha ya ɗauke ta ne? Mai aikin Naja? To da me yasa ya aure ta ne? ko dama haka ake soyayya? Ba ta sami amsar tambayoyinta ba ƙarar fitar motarsa daga gidan ta katse mata tunani, ta tuna ita ma aiki za ta tafi. Don haka ta miƙe ta wanke fuskarta ta ƙarasa shiryawa ta fice daga gidan zuciyarta cike da damuwa.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Biyar

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Biyar
Labarin na GabaYadda Wasu Kayan Da Hausawa Ke amfani Da Su Ga Doki Suke
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.