khairatu.shehu
Shan ƙwaya shi ne, shan ƙwayoyi waɗanda a likitance bai zama dole ba ko kuma a sha fiye da kima da kuma shan ƙwayoyi waɗanda doka ta haramta a yi amfani da su, kamar wiwi da hodar Iblis wato coceine da makamantansu.
A yau, yanayin da muka tsinci kanmu a ciki na gurɓacewar ɗabi’u da halaye a tsakanin ‘yan mata da zawarawa kai har ma da wasu matan aure sai dai mu ce abubuwa sun zama yadda suka zama, wato shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma kayan maye abin sai a ce Lahaula! A da dai mun fi sanin maza da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da magunguna da kuma sauran abubuwan da suke sa maye, wanda har yara idan suka ga mai irin wannan ɗabi’ar yana tafiya yana tamɓele, suna bin sa da waƙa suna cewa:
Ya yi marisa,
Ya sha kafso.
Amma ban da yanzu, an sami yawaitar masu shan miyagun ƙwayoyi, musamman ma dai matasa maza da mata. Idan mutum ya tsayar da hankalinsa ya kuma tambayi kansa da kansa menene dalilin da yasa mata a halin yanzu suka tsunduma a harkar shaye-shayen magunguna masu sa maye, na tabbatar ba zai iya ba wa kansa amsa gamsasshiya ba.
Amma ƙila amsar da masu yin wanan shaye-shaye za su bayar ta fi zama abin dogaro da kuma amfani da ita fiye da wadda ba mai shan ba zai bayar, don an ce mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo. Saboda haka zan yi wanan magana ne a kan iya fahimtata da kuma wasu bayanai da na samu daga irin binciken da na yi ,musamman mata masu shan ire-iren waɗannan magunguna ko ƙwayoyi.
Babban abin damuwa shi ne ko da Allah ya yi wa mutum gyaɗar dogo ta hanyar kare shi daga amfani da magunguna ta hanyar da ya ga dama, wannan ba ya nufin ya kuɓuta daga illolin da suke haifarwa ba ne, in ma mutum ba ya aikata wannan ta’asar, to za a samu wani makusancinsa yana aikata wannan ɗanyen aiki.
Ko da ma a ce an yi matuƙar sa’a ba a samu wani a dangin mutum yana yi ba, abu ne mai matuƙar wahala a ce ba a samu wani daga cikin ‘yan uwansa da ya taɓa gamuwa da wata matsalar ta hanyar wasu ‘yan ƙwaya ko ‘yar ƙwaya ba. Misali,a rikice-rikicen siyasa da ƙabilanci ko kuma na addini, wanda ‘yan ƙwaya ke yin uwa su yi makarɓiya a ciki. Ba ma wannan ba, hatta iskar da muke shaƙa na iya gurɓata da hayaƙin shaye-shayen ‘yan ƙwaya da sauransu.
Idan muka yi la’akari da misalan da suka gabata, za mu iya cewa ba wani ko wata a cikin al’umma da za su iya ta’ammali da ƙwayoyi ta hanyoyin da ba su da ce ba. Sai dai kawai mu ce wasu sun fi wasu.
Danna nan don karanta Mecece Ƙwaya?
Edita@rumasau-kallamu