Menene Motsin Rai?

0
29

Motsin rai shi ne sanin yanayin da kake ciki ko yanayin da wasu suke ciki (farin ciki ko baƙin ciki) da sanin yanda suke faruwa da iya sarrafa wannan yanayi sannan ka iya mu’amala da mutane, har ma ka iya jan ra’ayin mutane.

Motsin rai ya kasu kashi hudu, wanda ya haɗa da:

  1. Sanin yanayin kai (na farin ciki ko na baƙin ciki)
  2. Iya sarrafa kai
  3. Sanin yanayin wasu
  4. Iya mu’amala da mutane (a duk yanayin da suke ciki)

Bayani

  1. Sanin yanayin kai: shi ne sanin yanayin da kake ciki (na farin ciki ko baƙin ciki) da kuma sanin yanda suke faruwa da kuma me ke kawo su.

Abubuwan da suka haɗa sanin yanayin kai:

  1. Gane yanayin kai: sanin yanayin ka/ki da sanin menene zai iya faruwa idan kana/kina a cikin wannan yanayin.
  2. Auna kanka/ki  a mizani: sanin me zaka/ki iya da iyakokin ka/ki.
  3. Amincewa da kai: sanin darajar kanka da abubuwan da suke dai-dai da kai.

Muhimmancin mutum ya san yanayin kansa:

  1. Iya zartarwa da kai hukunci a cikin kwanciyar hankali.
  2. Amincewa da kai.
  3. Iya mu’amala da mutane.
  4. Iya riƙe kansu.

Hanyoyin da za ka bi don iya gane yanayinka

  1. Yawan lura da abubuwan da kake aiwatarwa da kuma yanayin da kake/kike ciki a yayin aiwatarwa.
  2. Yawan kallon kanka idan za ka aiwatar da wani abu.
  3. Tambayi mutane kan yanda ɗabi’unka suke a duk yanayin da kake ciki.
  1. Iya sarrafa kai: shi ne iya amfani da sanin yanayin kai gurin sarrafa yanayin da kake ciki da kuma karkatar da ɗabi’unka a lokacin da ya dace.

Abubuwan da za ka yi dan iya sarrafa kai

  1. Daina yawan tunanin da bai dace ba.
  • Ka/ki dena haɗe kowa ka soke su da wani abu.
  • Ka/ki dena faɗan abubuwan da ba su kamata ba akan mutane
  • Cire girman kai
  • Yi kokari ka/ki sa mutane nishadi
  • Karkatar da fushinka
  • Sanin yanayin wasu: shi ne kintatar dai-dai irin yanayin da mutane suke ciki (farin ciki ko baƙin ciki), sannan ka san me ke faruwa da su.

Abubuwan da suke da alaƙa da sanin yanayin wasu:

  1. Zurfafa tunani
  2. Tausayi
  3. Girmama mutane
  4. Yadda da bambancin da ke tsakanin mutane
  1. Iya mu’amala da mutane: shi ne amfani da sanin yanayin kanka da na wasu dan ka riƙe mu’amala da ke tsakaninku ta cigaba.

Abubuwan da suke da haɗi da iya mu`amala da mutane

  1. Jan ra’ayi
  2. Jagoranci
  3. Sadarwa
  4. Gina mu’amala
  5. Aiki tare
  6. Haɗin gwuiwa
  7. Warware matsaltsalu

Amfanin ilimin sanin motsin rai mai kyau

  1. Masu ilimin motsin rai mai kyau sun fi samun farin ciki, lafiya da kuma samun nasara a mu’amalarsu da waɗansu.
  2. Masu ilimin motsin rai mai kyau sun fi iya haɗe tsakanin yanayinsu da kuma dalilan faruwarsu.
  3. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna sane da irin yanayin da suke ciki a kodayaushe.
  4. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna da tausayawa waɗansu.
  5. Masu ilimin motsin rai mai kyau suna da kamun kai.

Matsalolin da rashin ilimin motsin rai yake haifarwa

  1. Ɗabi’a mara kyau
  2. Rashin iya mu’amala
  3. Rashin ƙwarewa a aiki
  4. Tunani mara kyau. Da dai sauransu

Yadda ake Sarrafa yanayi na sauran mutane

  1. Yi amfani da salon mu’amala mai ma’ana
  2. Ba da amsa maimakon mayar da martani ga rikici
  3. Yi amfani da basira wurin sauraro
  4. Ɗauki suka ko zagi da sauƙi
  5. Ka tausayawa mutane
  6. Kasance mai kusanci da zamantakewa

Ilimin motsin rai abu ne mai ƙarfi wanda zai iya haɓaka rayuwarmu ta sirri da ta sana’a sosai. Ta hanyar fahimta da sarrafa motsin zuciyarmu, da kuma ganewa da kuma rinjayar motsin zuciyar wasu, za mu iya gina dangantaka mai ƙarfi, warware rikice-rikice yadda ya kamata, da yanke shawara mafi kyau.

Danna nan don karanta yanayin duniya kafin aiko da manzon Allah SAW

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke Haifar Da Mura Wacce Ba Ta Warkewa (Causes Of Chronic Rhinitis)
Labarin na GabaSunayen Jikokin Annabi