Menene Cutar Suga (Diabetes)?

0
31

Jikin ɗan Adam na buƙatar wani irin nau’in sinadarin suga (glucose) da ke cikin jini domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan ayyukan da suka shafi lafiyar jikin.

Suga (glucose) na bayar da kuzari (energy) ga jikin ɗan Adam wanda ake buƙata wajen narkar da abinci da kuma rayuwar ƙananan halittun da suka tattaru (yawa) suka yi ginin jikin ɗan Adam ko halittarsa tamkar bululluka [tubali] (cells).
Wannan sugan ‘glucose’ shi ne makamashin da ke ba wa jikin ɗan Adam kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne daga abincin da muke ci, wato nau’in abinci mai samar da kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero, dawa, masara ,shinkafa da sauransu. kwakwalwa (brain), ko hanyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa a jiki (nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini ( developing red blood cells) , duk kaninsu suna amfani da wannan makamashi (glucose) domin samun rayuwa.
Ciwon-suga (diabetes) cuta ce wadda suga (glucose) da ke cikin jini yake haurawa sama wato suga ya yi yawa a cikin jini. Yawansa na da illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili da jikin mutum ba ya samar da da wani sinadarin kemical mai suna ‘insulin’
( type 1 diabetes) , ko jikin ne ba ya amfani da ‘insulin’ yadda ake so, ko kuma ma jikin ba ya samar da ‘insulin’ da kyau [wato isasshe]
( type 2 diabetes). Idan har babu ‘insulin’ to fa sugan ‘glucose’ zai cigaba da taruwa da yawa cikin jini har ya yi illa ga lafiya.
Sinadarin ‘insulin’ (a hormone), wata tsoka ce a jikin ɗan Adam take samar da shi (pancreas).
Amfanin sinadarin ‘insulin’ shi ne ɗaukar sugan ‘glucose’ da ke cikin jinin zuwa cikin ƙananan halittun da suka gina jikin ɗan Adam (cells) domin samun kuzari gare su da cigaban rayuwa.
Idan babu ‘insulin’ ko ba ya aiki yanda ake buƙata to suga fa zai cigaba da taruwa cikin jini ya yi yawa har ya haddasa munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa ga idanu, ƙoda, wasu jijiyoyin jini da kuma wayoyi/hanyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa a jiki.
Ciwon-suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar sashen jiki koma ya jaza yanke ƙafar marar-lafiyar. Idan ciwon ya yi ƙarami zai iya haddasa matsalar ƙashi da gaɓoɓi, matsalar fata, matsalar narkewar abinci, rashin ƙarfin mazakuta, matsalar haƙora da dasashi.
‘Type 2 diabetes’ ,wato nau’in ciwon-suga na 2 da muka yi bayani (wanda jiki ba ya amfani da ‘insulin’ yadda ya dace) shi ne nau’in ciwon-suga da ya fi yawa ga mutane da dama fiye da nau’in ciwon-suga na 1: ‘type 1 diabetes’ (wanda mu kace jiki ba ya samar da da sinadarin ‘insulin’).

Alamomin Ciwon Alamomin Ciwon-suga Nau’i na (type 1 diabetes symptoms):
• Yawan jin ƙishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum ya yi ƙoƙarin rage nauyin ba
• Daɗewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a hankali
• Rashin gani da kyau. Awon jini zai iya nuna idan akwai ciwon ko saɓanin haka.

Idan akwai irin nau’in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da sinadarin ‘insulin’ da aka samar a asibiti, za a ba shi sinadarin a asibiti akan ƙa’ida da umarnin ƙwararren likita. An fi yawan samun ƙananan yara da matasa da irin wannan nau’in ciwon-suga (Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes) duk da dai cewa zai iya shafar mutane a kowane shekarun su na rayuwa.

Alamomin Ciwon-suga Nau’i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin ƙishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, ƙaiƙayin fata
• Mutum ya ji kamar ba ƙafarsa ba ko jin tsira a ƙafafu

Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise), rage nauyin jiki yanda ya dace da koyarwar kiwon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci da ya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , za su taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na ciwon-suga.

Cututtukan saifa, magunguna, kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da ake alaƙantawa da suke haddasa ciwon-suga. Allah ya ba mu lafiya AMEEN.

Danna nan don karanta Sinadarin Ka-Fi Suga

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceYadda Tarbiyyar Hausawa Take A Zamanin Da.
Labarin na GabaAmfanin Nonon Raƙumi A Jikin Ɗan Adam
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa