Mene ne Maganin Ƙazamin Kishi ( Haramtacce)

0
903

Nutsuwa da bin al’amura sannu a hankali na ɗaya daga cikin abubuwan da suke hana faruwar ƙazamin kishi.

Bayan haka, addu’a ma babbar makari ce da take maganin ƙazamin kishi.
An karɓo hadisi daga Ummu-salama (Radiyallahu An ha) ta ce: “Haƙiƙa na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa “babu wani musulmi da wata musiba za ta same shi ya faɗi abin da Allah ya umarce shi da faɗar sa (wato) face sai Allah ya musanya masa abin da ya rasa da wanda ya fi shi alheri”. Ummu-salama ta ce: (yanzu) cikin musulmai wane ne ya fi Abu Salama alheri, farkon mutan gidan da suka yi hijira zuwa ga Manzon Allah? (duk da haka dai sai na faɗi addu’ar. Sai kuwa Allah ya musanya mini da aurar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ta ce: “Haɗib ɗan Balta’a Manzon Allah ya aiko wajena ya nema masa aurena. Sai  na ce da shi (ka gaya masa) ina fa da ‘ya’ya, kuma ni mace mai zafin kishi. Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Batun ‘yarta, zan roƙi Allah ya sa mata wadatuwa daga ita, ita kuma zan roƙa mata Allah ya tafiyar mata da zafin kishin da take da shi”. Muslim da wasunsu suka rawaito shi.

Ko waɗanne Illoli Haramtaccen Kishi yake da su?

Haramtaccen kishi yana da illoli kamar haka:
1. Jawo wa mai yin sa fushin Allah
2. Sa gaba da ƙiyayya fafur da kuma haifar da fitina gagaruma a tsakanin al’umma.
An karɓo daga Jabir ɗan Atik (Radiyallahu An hu) ya ce: haƙiƙa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:” Kishin da Allah ba ya so, shi ne kishi ba tare da wani abin zargi ba.” Abu Dawud ne ya rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan kishi iri nawa ne da kashi nawa kishin bayi ya kasu danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceKashi Nawa Kishin Bayi ya Kasu?
Labarin na GabaMene ne Matsayin Mumini Mai Kishi?