Kwamfuta ita ce na’urar da take amfani da wutar lantarki, wacce ke sarrafa tasarrafin ragamar bayanan da aka shigar mata, don sarrafa su zuwa wani abu mai ma’ana ko fa’ida, ta hanyar shigarwa da karɓarwa gami da adanawa tare da fitar da bayanan abin da aka shigar mata.
Na’urar kwamfuta wata aba ce wacce take taimakawa mutane wajen gudanar da ayyukan su cikin sauƙi gami da adana musu bayanan su tare da binciko abin da suke buƙata cikin sauƙi.
Kwamfuta ita ce take mayar da abu mai wahala zuwa sauƙi da kuma kiyaye ingancin wani abu ta hanyar shigar da shi cikinta, wanda tsawon shekarun da zai kwashe a cikinta yana nan, kuma ingancinsa yana nan. Misali littafin da aka ajiye shi a cikin kwamfuta da kuma wanda aka ajiye shi a cikin ɗakin karatu sama da shekaru hamsin, wanne ne daga cikin su zai kasance mai inganci sosai daga cikin su?
Kwamfuta ita ce take karɓar ɗanyen saƙo (data), sai ta sarrafa shi zuwa abu mai ma’ana wanda kuma zai bayar da bayanai masu inganci. Misali mutane sun yarda shinkafa da masara abinci ne, amma idan mutum ya siyo shinkafa a kasuwa ko a shago, ba zai iya ɗauka a matsayin abinci kai tsaye ba, har sai ya dafa ta, ta hanyar yin amfani da shinkafa, tukunya, mai, magi, gishiri, ruwa, kayan miya da sauran su. Sannan idan sun gama dahuwa a tukunya ɗaya, sai mu ɗauka a matsayin abinci. To haka ita ma kwamfuta take wajen sarrafa bayanai.
Domin karanta menene data informationn danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu