Matakan Shiga Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi

0
3

khairatu.shehu

Akwai matakai huɗu da ake bi ta kansu kafin a tabbata a cikin shan miyagun ƙwayoyi da sauran kayan sa maye, ga su kamar haka:

Ɗanɗano

A wannan gaɓar akan fara ne ta hanyar gwaji ta sanadiyyar bayar da kyautar ƙwaya ko kuma kowane irin nau’i na kayan maye, ko kuma samun tayi daga ƙawaye ko abokai masu shan ire-iren waɗannan kayan maye. Wannan kuma ya danganta ga wadda aka bai wa ta gwada, wata daga wannan ɗanɗanawar ta farko ba za ta sake marmarin ƙara amfani da abin da aka ba ta ta ɗanɗana ba don saboda irin yanayin da ta sami kanta a ciki, wasu kuma za su ɗore daga nan, duk da irin halin da suka sami kansu a ciki saboda irin ƙarfin gwuiwar da za su riƙa samu daga ƙawaye ko abokai.

Lokaci-lokaci

A nan kuma yana kasancewa wadda za ta sha ƙwaya ko kayan maye sai a lokutan da take tare da ƙawayenta ko abokanta waɗanda suka fara ba ta kayan maye, wata ƙila idan an haɗu a wuraren biki ko suna ko liyafa ko wajen kallo ko kuma gidan ƙawaye da samari da makamantansu.

Kowane Lokaci

Har ila yau, a wannan matakin kuma shan kayan maye ya fara zama jiki ga wadda aka koyawa, don a wannan yanayin yarinya za ta dinga amfani da kuɗinta ne a kowace rana tana sayen ire-iren kayan mayen da ta saba amfani da su.

Dawwamammiyar Mashayiya

A wannan mataki kuma mace take zama cikakkiyar mashayiya, a lokacin rayuwarta ta zama ba za ta iya tsinana komai ba har sai ta sha abin da ta saba sha, kai a wannan lokaci ba ta ma damu da abin da za ta ci ba baya ga ta sayi kayan maye don ta sha ta sami biyan buƙatarta.

Wata Matashiya da Soyayya ta Shigar da Ita Shaye-shaye

A wata hira da aka yi da Binta Muhammad ranar 29/9/2012 ta wayar hannu (ƙawar wannan yarinya da abin ya faru gare ta) ta bayyyana cewa:

“Wannan labari ya faru a babban birnin Tarayar Nijeriya, wato Abuja, amma don Allah kada ku bayyana sunan yarinyar da kuma mutumin.

Shekarunta kimanin talatin a duniya, fara ce Bafulatana, wadda ta fito daga ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Nijeriya, kuma karatu ya kai ta babban birnin tarayyar Nijeriya wato Abuja. Kyakkyawar matashiya, ‘mai addini, mai kirki, mai mutunci’. Tana yin azumin Litinin da Alhamis, kuma ba ta shaye shaye a waɗannan ranaku, saboda darajar wannan azumi da take уi.

Kuma salla ba ta wuce ta, don ba ta yin shaye-shayen sai bayan an yi sallar isha’i, ta yadda duk buguwar da ta yi kafin asuba ta wartsake.

Wani babban mutum wanda ya kai matsayin minista a wannan ƙasar ta Nijeriya, shi ne yake son ta, amman kuma mashayi ne na sosai. Yau da gobe suna soyayya da matashiyar nan sai da ya ja hankalinta ta soma shan abubuwan da yake sha, kamar hodar Iblis (cocaine) da tabar wiwi da giya da ƙwayoyi masu sa maye.

Yana kuma ɗaukar ta ya fita da ita ƙasashen waje, yana biya mata duk wasu buƙatunta na abin duniya, amma ya illata mata rayuwa da shaye-shaye. Ya bi duk yadda ya bi don ya janye hankalinta kuma ya yi nasarar, ya sa ta a wannan mummunar hanya. Amma yanzu Allah ya taimake ta sun rabu, tana nan tana ƙoƙarin sauya rayuwarta daga mummuna zuwa kyakkyawa.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye Shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino ya wallafa

Danna nan don karanta Shaye-shayen Kayan Maye

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceSiyasa
Labarin na GabaWasu Daga Dalilan Shaye-shayen Ƙwayoyi
Ado Ahmad Gidan Dabino
Shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Najeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni sannan ɗan wasa ne a shirin finafinan Hausa kuma ɗan jarida. Tare da shi aka kafa wasu ƙungoyoyi na marubuta da masu shirya finafinai. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama'a da yake yi a cikin ayyukansa.