Kamar yadda aka yi bayani a baya, makaɗi yana amfani da gurbin furuci na gaɓoɓi a cikin kalmomi da jimloli ya samar da zubin waƙa.
Ta haka makaɗi yake sarrafa harshe, ya harhaɗa ƙwayoyin sauti da amon kiɗa, ya saƙa saɗaru cikin ɗiya, ya rera wa masu ji da sauraro saƙonni masu ɗaga hankali, masu cika fuska, masu daɗi, masu garɗi masu shaguɓe da baƙar magana, masu fallasa muruwa da soke daraja, masu barkwanci, masu tumasanci, masu nuna kasawa, masu ƙasƙantawa da sauransu waɗanda kuma suke yi domin manufofi mabambanta.
A wajen ɗorawa da tafiyar da harshen waƙa, makaɗan baka na Hausa suna bin hanyoyi iri-iri waɗanda muhimmai daga cikinsu suka haɗa da:
4.1 Harshe na Nuna Hikima
Hikima a harshe ta shafi iya magana bisa dacewa da manufa ba tare da tsawaitawa ba. Hikima kuma takan danganci ƙarfin ƙwaƙwalwa ko ƙarfin basira wajen gina zance mai ma’ana tare da ayyana manufa daga mutum ɗaya-ɗaya ko al’umma. A wani bi ma manufar hikima ba takan bayyana a sarari ba, takan zama a sakaye ta yadda a kullum za a dinga ƙoƙarin fahimta ko ganowa.
Hikima kuma takan zama yin wani abu wanda zai birge mutane (CNHN, 2006: 200). Yahya (2012: 238) shi kuma yana ganin hikima wadda ta jiɓinta da harshe takan shafi hanya ko matsalolin rayuwa ta bayyana su cikin zaɓen kalmomi da za su ɗora a kan zance mai armashi.
Makaɗan Hausa sukan yi amfani da harshe mai hikima domin sakaya zance ko su kaifafa tunani ko su zurfafa tunani ko su taƙaita ma’ana ko su saka galmi a zance ko su kawar da gwangwani ko su saka gwangwani ko su yi barkwanci ko su dagule tunani ko su ƙawata rai ko su saka jin daɗi ka su burkuta zuciya ko su tayar da hankali da sauransu.
Sau da yawa kuma makaɗan sukan saka wasu maganganu na hikima ko azancin harshen Hausa kamar karin magana da baƙar magana da ba’a da shaguɓe da zambo da habaici da kirari da makamantansu waɗanda makaɗan suke ƙawatawa tare da taƙaita tunaninsu a waƙoƙinsu.
Haka kuma makaɗa sukan yi amfani da dabaru na jan hankali waɗanda suke raɗe da hikima cikin kwatantawa da ƙarfafawa da jaddadawa da shirɓacen kalmomi ko na ma’anoni duka a mabambantan zubi na ɗiyan waƙoƙinsu. A wannan ɓangare, makaɗan sukan yi kamantawa da siffantawa da jinsintarwa da alamtarwa da kinaya da gamin bautar kalmomi da jaddadar ƙarfafawa da zubi mai jan rai da baubawan burmi da sauransu (Ɗangambo, 2007: 43-54).
Misali, idan aka dubi waƙar Shata ta ‘Sani Audi’ da ta ‘Habu na Habu’ da ta ‘Ummaru ɗan Ɗanduna na Gwandu’, za a ga Shata ya sarrafa hikimomin harshe iri-iri cikin mabambantan manufofi.
Tabbas harshe na nuna hikima a wajen ciro kalmomi na gwaninta da kwatance na ayyana wani yanayi ko siffa ko hali za a iya ganin misalin haka a wannan ɗa na waƙar ‘Gwabron giwa uban Galadima ɗan Sambo, ginshimi, Ginshiƙan Amadu na Maigandi kai a uban Zagi’:
Jagora: Ɗiyan Alibawa ku hanƙure,
‘Y/Amshi: Don Allah ya yo uban zagi, x2
: Domin kura ta wuce,
: Ana ɓacin laka kamar ita,
Jagora: Domin,
‘Y/Amshi: Kura ta wuce, ana ɓacin laka kama ita.
Jagora: Ko jiya na iske gamdayaƙi da tuji,
: Sun iske jinjimi,
: To sun ko mirɗa gardama,
: Sun iske su bubuƙuwa ruwa,
‘Y/Amshi: Dannan ni kau ina gaton gaɓa,
: Sai niƙ ƙwala gaisuwa,
: Su ko sun daƙile ni duk,
: Ni ko niƙ ƙara gaisuwa,
: Dannan gurbin da a cikin gurbi,
: ya amsa gaisuwa.
Jagora: Dannan sai jinjimi da yas sullata,
: Yas suntule su dut,
‘Y/Amshi: Shi ko tuji da ad da girman baki,
: Yak kwashe jinjimi,
: Dannan bubuƙuwa da tur rura,
: Tag gangame su dut,
: Rannan nis san duniyag ga,
: Komina ne wani mayin wani,
Jagora: Rannan,
‘Y/Amshi: Nis san duniyag ga
: Komina ne wani mayin wani.
(Gusau, 2009:145)
4.2 Harshe na Nuna Fasaha da Nagarta
A Ƙamusun Hausa an bayyana fasaha ita ce gwaninta ko ƙwarewa (CNHN, 2006:136). Ita kuma kalmar nagarta tana nufin kyawun abu ko ingancinsa (CNHN, 2006: 355).
Makaɗan baka na Hausa sukan yi amfani da harshe mai nuna fasaha ta fito da gwanintar abu ko ƙwarewar wani abu kan wani ko kuma harshe mai fitar da nagarta a kan kyawo ko inganci na wani abu. Yanayin harshe na nuna nagartar abubuwa a rayuwa ya mamaye zubi na waƙoƙin baka na Hausa har ma wasu daga cikin makaɗan sukan bayyana nagarta da zubi na fasaha na waƙoƙinsu.
Bawa Namiji Jega a wani ɗan waƙa ya tabbatar da fasahae harshe ita ce ke gaba, mai yin jagoranci a wajen shiryawa da rera waƙa mai ma’ana, mai garɗi.
Dubin abin da yake faɗa:
Jagira: Kalangu na da daɗi,
: In ga fasaha ta yi.
‘Y/Amshi: Shalla Barayar Kada,
: Fadama da sanyi take.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar ‘Shalla Barayar Kada’)
Ibrahim Narambaɗa ya nuna fasaha tana daga cikin hanyoyin sarrafa harshe da ke nuna darajar makaɗi a fagen waƙa. Yana cewa:
Jagora: Ai ba a gama ni da yaro,
: Na san yaro bai yi mƙamina ba,
: Ka ku gama ni da yaro,
: Na san yaro bai yi zalaƙata ba,
: Ka ku gama ni da yaro,
: Na san yaro bai yi fusahata ba,
: Ka ku gama ni da yaro,
: Ƙaryab banza,
: Yaro bai kai inda Narambaɗa,
: Mai tabarukun Sarki,
: Gogarman Tudu jikan Sanda,
: Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa.
(Gusau, 2003: 74).
Fasaha da nagartar harshe sun bayyana a zubin wannan ɗa na waƙar ‘Abin duniya tahowa na’:
Jagora: Na ji an ce a daina ma al’ada,
: Al’ada tana nan tana aiki,
: Karatun mutum bai wuce salla,
: Dole sai an yi Alhamdu Lillahi,
: To, ashe ko kana nan ga al’ada,
: Kowaɗ ɗauki kayan da bai ima,
: Bawa tilas ya dawo ya yasshe su,
: Abin duniya mai tahowa na,
: Ran da duk ya wuce sai ga labari,
: Sai ga labarin nan a tashe shi,
: Wane ai yayi irin tashi.
Jagora: Rigimar mutum dut ta rai nai ta,
: Ran da dut babu rai tashi ta ƙare,
: Kur’ani babu gamtsi ciki,
: To Hadisi da ko ba a ruwaito ba,
: Abin ga ko ko zari na mu tanye ku,
: Abin duniya mai tahowa na,
: Ran da duk ya wuce sai ga labari,
: Sai ga labarin nan a tashe shi,
: Wane ai yayi irin tashi.
(Bawa Namiji Jega: Waƙar ‘Abin Duniya’)
Daga cikin waƙoƙin da makaɗan Hausa suka aiwatar masu ɗauke da harshe na fasaha da nuna nagarta akwai waƙar ‘Ɗan’adam’ da waƙar ‘Aiki duka aiki ne’ da waƙar ‘Tica uban karatu’ na Ɗanmaraya Jos da waƙar ‘Mai Martaba ɗan Bayero’ da waƙar ‘Kano garin saye da sayarwa’ da waƙar ‘Na ɗauki angara na saƙala’ na Aminu Ladan Abubakar, Alan Waƙa da makamantansu.
4.3 Harshe na Nuna Yanayi
A luggance kalmar yanayi tana iya zama hali irin wanda ake ciki, kamar damina ko sanyi ko zafi ko bazara da sauransu (CNHN, 2006:478). A ma’ana ta fannu, yanayi yakan nufi bayyana halayyar abu ko halin aukuwar abubuwa ko nuna kamanni na abubuwa (Gusau, 2008:463).
Sau da yawa, makaɗan Hausa sukan zaɓo kalmomi su sarrafa su a waƙa su kuma dace da halayyar aukuwar abubuwa da wuri da lokaci da fasalin abu. A waƙar ‘Haji Garban Bichi ɗan Shehu’, Shata yana gaya wa Alhaji Garban Bichi game da harkokinsa na ciniki cewa:
Jagora: kaka ta matso uban Nura,
: Gyaɗa ta fara jar fata,
‘Y/Amshi: Haji Garban Bichi ɗan Shehu.
Jagora: Auduga ta fara kitse Garba,
: Gyaɗa ta fara jar fata,
‘Y/Amshi: Haji Garban Bichi ɗan Shehu.
Jagora: Gabas riƙa yamma ta kama,
: Gusun riƙa arewa ta samu,
: Baba gabas riƙa na yamma sun samu,
: Gusun riqa arewa ta kama,
:Kaka ta yi uban nura,
‘Y/Amshi: Haji Garban Bichi ɗan Shehu.
(Gusau, 2009:340-341)
4.4 Harshe na Gwagwarmaya
A wata ma’ana an nuna gwagwarmaya tana nufin yin fama ko karawa da wani (CNHN, 2006: 180). Wata ma’ana ta gwagwarmaya takan ƙunshi bijirereniya ko fanɗarewa ko kangara. A gwagwarmaya akan ƙarfafa hanyoyin ƙwatar rayuwa kamar neman abinci ko kiyaye haƙƙi ko neman waraka daga wata cuta ta bayyane ko ta ɓoye ko kishin ƙasa da al’adu ko kishin addini ko makamantan waɗannan hanyoyi.
Wasu makaɗan Hausa sukan shirya waƙoƙi bisa harshe na gwagwarmaya da ke neman daidaito a rayuwar al’umma. Wasu daga cikin waƙoƙin baka waɗanda aka shirya su ta harshen gwagwarmaya sun haɗa da waƙar ‘Buɗaɗɗiyar Wasiƙa’ da ta ‘Raba Gardama Ɗansani’ da ta ‘Alƙalami ya zarce takobi’ da waƙar ‘Jami’a Gidan ban Kashi’ 1-3 na Aminu Ladan Abubakar, Alan Waƙa.
Akwai waƙar ‘Shegiyar uwa mai kashe ‘ya’yanta PDP’ ta Haruna Aliyu Ningi da Waƙar ‘Haɗa kan Nijeriya’ ta Musa Ɗanba’u da waƙar ‘Babbar Ƙasar Shehu Ɗanfodiyo’ ta Alhaji Mamman Sarkin Taushin Katsina da waƙar ‘Haɗa kan Nijeriya’ ta Ɗanmaraya Jos da waƙar ‘Allah rayan jihar Katsina’ da ta ‘Muriki Abincinmu’ na Gargajiya na Alhaji Mamman Shata Katsina da makamantansu.
4.5 Harshe na Faɗakarwa
Kalmar faɗakarwa tana nufin faɗakarwa ko luraswa ko yin nuni ko ishara domin a lura. Kalma ce wadda take daga faɗaka wato farka ko lura ko kula (CNHN, 2006:129). Maganar Hikima wadda Hausawa suke cewa, ‘nuni cikin nishaɗi’ tana nufin yin faɗakarwa cikin wata siga ta raha ta amfani da harshe mai karsashi, mai daɗin ji, mai motsa rai.
A faɗakarwa ana tunatar da mutum ne a kan waɗansu al’amuran rayuwa waɗanda suke yi masa tambihi ya aiwatar da su ko kuma ya guje musu. Yawanci a faɗakarwa akan ƙara tunasarwa ne, ko a lura da wasu abubuwa, ko a janyo hankali zuwa gare su (Auta, 2008:75-76).
A harshen waƙa makaɗan Hausa sukan yi faɗakarwa a kan wasu abubuwa na al’umma domin su tunashe su, su lurar da su ta amfani da kalmomi na nasiha da wayar da kai da jawo hankali, musamman akan yin aure da neman aure da zaman aure da zawarci da haƙƙoƙin iyaye da na ‘ya’ya da yaran gida da faɗakar da matakan zamantakewa a gida da unguwa da gari da ƙasa da tuni kan matsayi da halayen sababbin abubuwa masu faruwa a rayuwar al’umma da sauran abubuwa na zamantakayya.
Akwai waƙoƙin baka da yawa matuƙa a kan harshen faɗakarwa, kuma har wa yau makaɗa na ta aiwatar da su. Misalan waƙoƙin harshen faxakarwa sun haxa da waqar ‘Jawabin Aure’ da waqar Kwalara’ da waƙar ‘Gulmawuya’ na Ɗanmaraya Jos da waƙar ”Don salla da Salatil-Fati’ da waƙar ‘Noma aikin ‘Yan’arewa’ na Alhaji Mamman Shata da waƙar ‘Cutar Taɓin Hankali’ da waƙar;’Irin Ginin Sakarkari’ na Alan Waƙa da waƙar ‘Naira da Kwabo Sabon Kuɗi Haruna Uji da sauransu.
4.6 Harshe na Nuna Alhini
Kalmar alhini tana nuni a kan juyayi ko tausayawa a kan wani rashi na mutuwa (CNHN, 2006:12). Harshen alhini, harshe ne wanda ake ɗura wa kalmomi na yin ta’aziyya tare da sanyaya wa mutum da aka yi wa rashi tare da ba shi haƙuri da yin addu’a.
Makaɗan Hausa sukan yi alhinin mutuwa a zubin waƙoƙinsu, musamman ma waƙoƙin turken ta’aziyya. Tubalan ginin harshen alhini ya ƙunshi kalmomi na tausayawa da juyayi da nuna jimami da addu’a da ba da haƙuri da kalmomin sambarka a kan halayen mai mutuwa ko kalmomi masu tuna ayyukan da ya yi kyawawa, ayyuka na taimako, ayyuka na inganta rayuwa da sauransu. Misalan waƙoƙi na harshen alhini sun hada da waƙar ‘Allah jiƙan Ciroman Gwambe’ ta Mamman Shata da waƙar ‘Mutuwa ba ki da sabo’ ta Abdussalam, Shatan Nijar da waƙar ‘Ɗamarar ko ta Kwana’ ta Alan Waƙa da sauransu.
Dubi abin da Shata ya faɗa a harshen ta’aziyya cikin alhini:
Jagora: Kowa yam mutu bai sauri ba,
: Mu da muke nan ba mu daɗe ba,
: Sai mun zo Ciroman Gwambe.
‘Y/Amshi: Allah jiƙan Ciroman Gwambe.
A wani ɗa Shata yana cewa:
Jagora: Ni me zance ma Sarkin Gwambe,
: Sarkin Gwambe ya yi rashi,
: Haka ni ma Mammalo mai ganga,
‘Y/Amshi: Allah jiƙan Ciroman Gwambe.
(HBTKA, 2003:32&38).
4.7 Harshe na Sanya Sambarka
Sambarka, kalma ce wadda ake amfani da ita don nuna godiya ko yabo ko murna, takan ɗauki ma’anar ‘Allah ya sa albarka. Haka kuma takan nufi tubarkalla ko madalla ko sanya albarka (CNHN, 2006:386).
Waƙoƙin Hausa suna cike da harshe cikin kalmomi masu yabo ko yabau ko bege, kalmomi na nuna sambarka, kalmomi masu saka jin daɗi, kalmomi na ayyana soyayya ko ƙauna, kalmomi masu nuna yanayi na farin ciki ko sakin fuska ko sakin jiki ko farar zuciya ta yin magana kwakkyawa, ta baza alheri, ta baza kyauta, ko nuna hannun baiwa da sauran maganganu masu saka wa jiki annashuwa, ita kuma zuciya ta faranta har a wani lokaci ta ɗimauta, idanu su dinga zubar da hawaye domin daɗi.
Harshe mai saka tsima ta sambarka ya ƙarfafa a waƙoƙin baka na Hausa waɗanda ake yi wa masoya da waɗanda ake ƙauna kamar malamai da sarakuna da attajirai da iyaye, maza da mata, da sauran mutane masu ayyukan bajinta, masu ɗaukaka darajar al’ummar Hausawa.
Mai waƙa Yakubu Muhammad ya yi ishara wadda ya nuna yabo, ta amfani da kalmomin sambarka, yakan saka daɗin zance ya jaddada ƙauna a inda ya ce:
Jagora: Imbambaliba imbambalibo,
: Biyayya daraja ce,
: Yabo daɗin zance,
: Ƙauna ai ƙima ce,
: Son ki gare ni ai hujja ce,
‘Y/Amshi: Alambiyo-biyo yaran badali,
: An yi bibiyo sai in da dalili.
(Yakubu Muhammad: Waƙar ‘Imbambaliba’)
Wannan fage mai faɗi ne wanda yake da waƙoƙi masu ɗimbin yawa, kila waɗanda ma baza a iya gane adadi na yawansu ba. Wasu daga cikin waƙoƙi na harshen nuna sambarka su ne waqar ‘Abdullahi shugaban sahu’ da waƙar ‘Mai yawuri bangon daniya’ da waƙar ‘Babban bijimi Muhammadu Sama’ na Aliyu Ɗandawo da waƙar ‘Amadun Bubakar gwarzon Yari’ da waƙar ‘Gogarman Tudu jikan Sanda’ na Ibrahim Narambaɗa da waƙar ‘Mai dubun nasara garnaƙaƙi sardauna’ da waƙar ‘Zaki ba a ja ka wasa ba’ da waƙar ‘Babban jigo na Yari’ na Musa Ɗanƙwairo da waƙar ‘Bijimin gidan Bello Mamman na Yari’ da waƙar ‘Tsakin Tama na Abashe’ da sauransu.
Sa’idu Faru ya gaya wa Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo wasu halaye nasa tun a lokacin da yake riƙe da sarautar Sarkin Kudun Sakkwato har yake gaya masa Sarkin Musulmi ne na wata rana. Ga abin da ya ce:
Jagora: Maganag ga da za ni faɗa maka,
: Gagarau ɗan Aliyu kai mana gafara,
: Wada duk aka gadon ƙasura,
: Wada duk aka gadon ɗaukaka,
: Wadda duk aka gadon ci gaba,
: Mamman ka gaji Abubakar
: Ko da sayen halin nan akai,
‘Y/Amshi: Baba halin da ka kai kuɗɗi shikai.
Ya ci gaba da cewa:
Jagora: Diba ƙafarka zuwa bisa hannuwa,
: Zaman Shaihu na ba wata sa’ida,
: Sarkin Musulmi wataran kake,
: Da imani da mu’ujjiza,
‘Y/Amshi : Na nan ga Malam Macciɗo,
Jagora: Tun ga Aliyu Maisango naj jiya,
: Halin ga da Bubakar yar riƙa,
‘Y/Amshi: Macciɗo kai ka shirin gado haka.
(Gusau, 2009:154).
4.8 Harshe na Tarihi
Tarihi wani fannin ilimi ne wanda yake ba da labarin al’amura da suka faru a zamanin da ya wuce wato labarin abubuwan da suka shuɗe (CNHN, 2006: 49).
Makaɗan baka na Hausa sukan yi amfani da harshe mai nuna tarihi su gina waƙoƙinsu. Misali, Alan waƙa ya rera wata waƙa a kan, tarihin cinikin bayi a tsakanin Hausawa mai gindi ‘Rayuwar Afirkawa, ga waƙar ‘Mu so Allah Sarkin makaɗa ‘ta Danmungai Daura wadda ya rera game da tarihin, zuwan Bayajidda ƙasar Hausa. Dubi kuma waƙar ‘Ga darajjar Amadu Bello’ ta Sarkin Taushi Salihu jankiɗi wadda ya bayyana tarihin zaman Turawa Nijeriya ta Arewa da hanyoyin da suka biyo da shekarun da suka yi kafin su miƙa mulki a 1960 da kuma bayan tashinsu.
Dubi abin da yake faɗa a wani ɗa:
Jagora: Zakkuwar Turawa nan Tudu,
‘Y/Amshi: Shekara hamsin da tara,
: Ta inda sunka biyo Bidda,
: Sai Kafin-Ɗanyumusa da Makurɗi,
: Kwantagora garin Ibrahim,
: Gwanga ya yi faɗa da Nasara,
: Ga darajjar Amadu Bello,
: Da arziki na mazan jiya yay yi.
Jagora: Dagga Zariya sai Birnin Kano,
‘Y/Amshi: Ƙoramar Zorori wajen faɗa,
: San Kano ya tarbi Nasara,
: Ga darajjar Amadu Bello,
: Da arziki na mazan jiya yay yi.
(Gusau, 2012:119-120)
4.9 Harshe na Koyar da Addini
Addini hanya ce ta yi wa Allah bauta, ko kuma kamar yadda Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006:3) ya bayyana, addini shi ne hanyar bauta wa Ubangiji. Akwai dabaru iri-iri waɗanda al’ummu suke amfani da su wajen yi wa Allah bauta. Mutum, ɗan’adam, ya shirya wa kansa wasu hanyoyi na bautar ubangiji na maguzanci, Allah kuma ya saukar wa ɗan’adam da daidaitacciyar hanya ta yi masa bauta a inuwar addinin Musulunci.
Addinin Musulunci yana ƙunshe da sharuɗɗa da hukunce-hukunce da ake neman kowane mutum Musulmi ya san su, ya yi aiki da su wajen yin wannan bauta ko ibada (Gusau, 2008:389). Haka kuma dole ne a sami wasu mutane daga cikin al’umma waɗanda za su tsayu a wajen koya wa sauran jama’a hanyoyi waɗanda suke yin jagoranci ga sanin matsayin bauta da kaifiyyarta da siffofinta da hanyoyin gudanar da ita.
Bisa wannan aiki ne aka sami wasu suka himmatu wajen koyar da abubuwan da suka shafi bauta ko ibada a addinin Musulunci tun daga Manzanni da Annabawa da malamai da sauransu.
Makaɗan baka na Hausa sun sami dama ta baiwar waƙa wadda suka dinga koyar da ayyukan ibada ta harshen waƙa domin ilmantar da mutane wasu sassa na sha’anin addininsu na Musulunci. Misali, waƙar ‘Fara ba mu ye Allah’ ta Uwaliya Mai’amada an zuba ta a kan harshe mai neman a kaɗaita Allah, waƙar ‘Mu je mu je ba mai yi kamar Allah’ ta Uwaliya ita kuma tana koyar da aikin hajji da kuma waƙar Ɗanyaya ta ‘Allah kai ni Madina’.
Ita waƙar ‘Don salla da Salatil-Fati’ ta Alhaji Mamman Shata Katsina ya gina ta ne bisa harshe na sunnar aure. Dubi kuma waƙar ‘Azumi watan bautar Allah’ ta Alan Waƙa wadda ya sarƙa ta bisa harshe mai yin bayani a kan ibadar Azumi ta watan Ramalana. Ga waƙar ‘Allah ba ku mu samu Alhaji Alhajiya’ har wa yau ta Alan waƙa wadda take karantar da matsaloli na almajirci irin na Ɗankulodu. Kila ko wannan ne ya sanya Alan Waƙa ya ba ta suna Muhajira wato waƙa wadda take ƙaurace wa bara da almajirci irin na ɗanƙolo domin ta zama wata hanya ta koyarwa cikin harshen waƙar baka, da sauransu.
4.10 Harshe na Bara-Gurbi
A hikimar magana ta Bahaushe ne yake kiran sauran ƙwai wanda kaza ta yi kwanci, bayan ta gama ƙyanƙyasa ta bar su da bara-gurbi. Irin ƙwai bara gurbi yakan zama ya ruɓe ko ya ƙafe ko ya zama gunya ko dai wata illa ko lalura ta same shi (Bargery, 1934&1951:81). Ƙwai bara-gurbi yana fita ne daga ƙwayaye masu lafiya waɗanda ake ƙyanƙyashewa su zama ‘yan tsaki.
Harshe bara-gurbi, harshe ne maras kyau, maras daɗi, mai ban haushi wanda wasu makaɗa suke jefawa a cikin wasu waƙoƙinsu. Abincin harshe bara-gurbi a waƙa shi ne zagi da batsa da baɗala da alfasha da munanan kalmomi, musamman irin na bara a kufai (Alan Waƙa: ‘Gara nai bara da bulayi, bara a kufai) da wasa da nassi na Alƙur’ani ko Hadisa ko musanta wani hukunci saukake ko ƙarfafa al’adu munana waɗanda suke kauce wa tubalai kyawawa na gina ingantacciyar al’ummar Hausawa. Lalataccen harshen waƙar baka tamkar lalataccen ƙwai ne wanda yake zama bara-gurbi (CNHN, 2006:37) a cikin ƙwayaye.
Wasu misalai na harshe bara-gurbi a waƙoƙin baka na Hausa sun haɗa da wani ɗa wanda Muhammadu Gambo ya rera inda yake cewa:
Jagora: Ba azumi nika wa gudu ba,
: Yawan sallan nan yau da gobe,
: Ba sallan nan nika wa gudu ba,
: Yawan duƙin nan yau da gobe,
: Ba shi barin mai rai da wando.
(Gambo mai waƙar Ɓarayi)
A wani ɗa ma yana cewa:
Jagora: Ba Allah nika wa tambaya ba,
: Wai laihin mutuwa ɗaukar ɓarayi,
: Ta bar mai kurɗi lahiya lau,
:Shin Allah mis sa hakan ga?
(Gambo mai waƙar Barayi)
A wani ɗa ma yana cewa:
Jagora: Ni dai in ga asara danya-danya,
: Ko ba a ban ko sisin kwabo ba,
: In ishe tsohi sun yi lanƙwat,
:Sai in ji kamar na taki Arfa.
(Gambo Fitilar Sarri mijin Kulu)
Wasu daga cikin waƙoƙi da aka yi su bisa harshe bara-gurbi su ne waƙar ‘Buwayi gasa na Shehu’ ta Ɗangaladima Labbo, Magajin Jankiɗi (Gusau, 1980:57) da waƙar ‘Ɗan’ali’ ta Muhammadu Bawa Ɗan’anace da waƙar ‘Gagaragadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa’ da waƙar ‘Habu na Habu’ da waƙar ‘A sha ruwa ba laihi ba ne’ na Alhaji Mamman Shata da waƙar’ Yau huɗu ga wata’ da waƙar ‘Jirgin sama za ya wuce’ na Aliko Makaho da wasu waƙoƙin Illon Kalgo da wasu na Isa Ɗanmakaho da wasu na Ɗanqurji da wasu na Musa Ɗanƙwairo tun ma ba wasu waƙoƙinsa na noma ba da sauransu.
Domin karanta cikakken bayani akan Dangantakar Harshe da Waƙa danna nan
Domin karanta cikakken bayani akan Yin Waƙar Baka ko Sarrafa Waƙar Baka danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakkken Littafin danna nan.