Maganganu Na Ƙarya A Kan Kashe Husaini (RA)

0
22

Waɗanda suka rawaito labaran kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) da kashe Usman (Radiyallahu Anhu) da sauran yaƙe-yaƙe sun ƙara ƙarerayi da yawa a cikin labaran.

A cikin malamai da suka yi rubutu a kan kashe Husain (Radiyallahu Anhu); akwai manyan malamai irinsu su: Al-bagawi da lbn Abid Dunya; amma duk da haka akwai ruwayoyin da ba su inganta ba, har ma da na ƙarya a cikinsu.

Su kuwa waɗanda suke kawo labaran ba tare da wani Isnadi ba, waɗannan su suka fi kawo ƙarerayi. Kamar yadda suke cewa wai ranar da aka kashe Husaini sai aka ga sama ta yi jawur; alhali wannan abu ne da yake faruwa-tun kafin wannan lokacin.

Wai kuma a ranar duk dutsen da aka ɗaga sai an ga jini a ƙarƙashinsa; wai an yi wa zuri’ar Husaini (Radiyallahu Anhu) tsirara an ɗora su a kan raƙuma ko sirdi babu ana ta yawo da su wuri-wuri, ƙarya ne.

Musulmi ba su taɓa kama wata mace daga banu Hashim ba a matsayin ribar yaƙi; sai dai masu son zuciya ba sa rabo da ƙarya.

Domin karanta cikakken bayani a kan Wane Ne Ya Ba Da Umarni A Kashe Husaini? danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Yaƙi danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTarihin Malam Ɗankwandarai
Labarin na GabaMusa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa