Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za a Magance

0
85

Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu a halin bacci, yakan iya faruwa sau ɗaya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan riƙa fuskantar yanayin akai-akai. Yanayi ne mai kama da mutuwa duk da yakan kasance mutum na a cikin hayyacinsa farke sai dai sam yakan rasa ikon motsawa ko magana. 

Wani lokacin ma yakan zamo idon mutum a buɗe zahiri duk da cikin bacci yake; abinda wasu kan kira da baccin zomo… to sai dai hakan duk bai sa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa yana cikin mawuyacin hali ko yana buƙatar ɗauki an maƙure shi. Shi yasa ga duk mai son fahimtar me ake nufi da firgici to dannau shi ne cikakken misalin firgici ko in ce ihunka banza domin ko ihun ka yi ba a ji, ba a san ma kana yi ba. 

Alamomin Dannau

Mutane kan fuskanci ma bambantan alamu; Sai dai duk yana daga alamun dannau. Mutum ya ji kamar an nannaɗe shi cikin wani bargo mai nauyi, ko kamar an ɗaure hannuwa da kafafunsa a miƙe kamar gawa, wasu kuma su ji kamar an shaƙe su sun kasa numfashi, wasu kamar wani abu ya kakare musu a moƙogoro sun kasa shakar iska, wasu kan ji sun kasa magana, wasu kuma su a karan kansu sun ji suna maganar amma kuma babu wanda yake jin su, sukan kasa motsa komai nasu, wasu kan riƙa jin tamkar mutuwa ce ta kusanto su.

Me ke Haddasa Hakan

Ɗaya Daga Manyan Ababen Da Ke Haddasa Hakan Shi ne: Ƙarancin bacci, wato mutane masu fama da larurar rashin bacci, ko kuma waɗanda suke ƙin kwanciya su samarwa da jikinsu isashshen bacci, haka nan samun canjin lokutan bacci kai tsaye watakila saboda yanayin aiki ko tafiya zuwa wata ƙasa da lokaci ya bambanta sosai. 

Haka nan shan wasu magunguna da ke aiki a ƙwaƙwalwa; kamar a mutane masu ciwon farfaɗiya, larurar halayya (personality disorders), ko kasancewa cikin tsananin halin matsi wato stress a ko da yaushe, ko larurar hawan jini, ko larurar damuwa wato depression duk suna iya haddasa dannau. Idan kanason karanta Alamomin Cancer Danna nan 

Sai kuma halayyar kwanciya ta rigingine wato ta gadon baya  fuska na kallon sama. Sai mutane masu shan ƙwayoyi ko magunguna masu sanya maye. Sai dai galibi mutane masu fuskantar ƙarancin bacci sun fi fuskantar wannan matsala sama da sau 10 fiye da saura daga nan sai masu kwanciya ta gadon baya fuska a sama.

Yaushe Dannau Ya Fi Faruwa

Ya fi zuwa da safe, ko dai gabannin asuba, ko masu irin komawa baccin nan bayan sun yi sallah asuba ƙarfe shida na safe ɗin nan. Hakan na faruwa ne walau a farkon bacci wato yayin farkon baccin wato sanda mutum ya kwanta ba tare da jimawa ba, idan yakan ga abun tamkar na faruwa ne a tunani ba zahiri ba, saboda sanda bacci ya fara ɗaukar ka ba ka sani sai dai ka ji ka shiga baccin kai tsaye amma in ya zamto ka fara bacci amma kana jin tafiyarka zuwa cikin baccin counsiciously to a lokacin za ka ji ka kasa magana ko motsi yadda dannau ke zuwa kenan.

Sai kuma ƙarshen bacci wato gab da farkowa, domin sanda bacci ya zo ƙarshe duk da idanuwanka suna rufe ƙwayar idonka ke fara farkawa wanda hakan zai sa idanuwan su riƙa kaɗawa sosai yayin da duk sauran jikinka yake a sake wato relaxed, a dai-dai wannan lokaci ne mafarki kowanne iri kan zo. Toh Idan ya zamto idanuwan sun farka process ɗin zai ci gaba da gangarowa tsokokin wuyanka, kafafuwanka zuwa hannayenka, gadon baya sannan ƙafafunka sai ka ji ka farko harda yin miƙa.

Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Shiga nan

To amma idan bayan farkawar idanun jikinka ya cigaba da zamowa relaxed wato yai jinkirin farko saboda position ɗin da kake ko kuwa bacci bai isa ba wata larura ce ta farko da kai hakan ke haddasa dannau ka ji idonka biyu amma sauran jikinka ya ƙi farkowa.

Yadda Ake Magance Matsalar

Babu wani gwaji da likitoci ke yi domin gano dannau, sai dai ga wanda abun ya tsananta akai-akai ta kai ga har numfashinsa na ɗaukewa akan binkici mutum ko yana ɗauke da wata damuwa a ba shi magani da zai kau da ita ko shawarwari, ko magance hawan jinin ya zamto under control ko yaushe.

  • Kyakkyawan shirin kwanciya wato ya zamto kaya ba masu nauyi ba a jika, sannan ai alwala inda hali ga maza ko mata ko da ana cikin haila, tare da addu’oi yayin kwanciya hakan nasa jiki samun nutsuwa da aminci ko da cikin halin tsoro ake.
  • Ƙuracewa kwanciya ta rigingine,galibi wannan shi ne dalili ga mutanen dake kwance ta  gadon baya fuska na kallon sama. Don haka ku kwanta a kowanne position amma banda rigingine, za ku ji kun dena da ikon Allah.
  • Gyarawa tare da ɗorewa bisa tsarin bacci me kyau da zai sa kake samun baccin awa 6 zuwa 8 a rana ko a dare. Ko me kake in lokaci ya yi rufe wayar nan ko kuma ka saita ta automatic take rufe kanta. 
  • Tabbatar da ingantacciyar tsaftar gurin kwanciya, a ƙalla duk sati ake canza zanin gado da pillow case, ake sharewa tare da kakkabe gurin kwanciya kullum.
  • Baccin rana musamman tsakanin karfe 1:30 zuwa 2:30 na rana in an sami lokaci, kar baccin rana yake wuce awa 1 da rabi… tare da ƙauracewa kwanciya bayan ƙarfe 3 na rana har zuwa magariba. Baccin yamma ba abu ne mai kyau ba sam, sai dai larura.
  • Banda cin abinci mai nauyi ko motsa jiki ƙasa da awa 2 kafin lokacin kwanciya bacci.
  • Banda amfani da electronic items su waya da sauransu awa 1 kafin kwanciya bacci, wasu ma’auratan ma kan sa wa kai dokar hana shiga ɗakin bacci da waya sam don a sami lokacin juna.
  • Cikakken tsaftar baki, ake brush da kyau domin wasu bakinsu kan samar da miyau ɗin bacci wanda in suka kwanta a rigingine miyau ɗinne ke toshe kafar numfashinsu wanda wannan abun tsorone shi ne mutuwa ka iya zuwa in abun bai saki mutum akan kari ba. Muddin Aka Kiyaye Wannan Za a Dinga Ƙwana Lafiya

Menene Abun Yi Yayin Da Dannau Ke Afkuwa? 

Galibi yana zuwa cikin hayyaci ga mutane suna iya tunani tare da komai kurum motsi ko magana ke gagarar mutum don haka abinda ya kamata ka yi yayin da ka ji wannan ɗaurin kazar kukun:

  • A ranka kai salati ka sanar da ubangiji shi ne matakin farko.
  • Kai ƙoƙarin amfani da tsokokin idanunka wato ka jaraba runtse idonka sosai ka rufe shi ka riƙa buɗewa a hankali kai ta maimaita haka.
  • Idan kana iya numfashi to ka shaƙi iska deeply wato ka yi irin shaƙar iskar nan ba tare da ka tsaya fitar da ita ba har sai cikinka ya ɗago…. in kai haka ƙila sai dai ka ji kamar an yaye ma labule ka farko.
  • Kana iya jaraba sanyawa ranka cewa ga shi nan kana ƙoƙarin motsa yatsun hannunka da na ƙafa, kai ta jaraba amfani da yatsun farko kafin sauran sassan jiki hannu, ƙafafu da sauransu.
  • Idan ya kasance a cikin yanayin kana jin motsi ko muryar mutane ko kuwa wani ne ma da ka sani ka ji yana danneka a baccin to ka canza wannan abinda kake ji ɗin zuwa cewa wannan din fa da kake jin muryarsa ƙoƙari yake ya tasheka.
  • A duk irin yanayin da ka sami kanka na dannau ka yi ƙoƙarin jin tunano wani abun muhimmi ka canza yanayin da shi har zuwa sanda za ka farko. Sannan ka zamo mai jaddada kalmar shahada ko Ayatul kursiyyu.

Zuwa Yanzu A Kimiyyance

Babu wani sananne wanda ya mutu dalilin dannau ko ya haɗu da wata illa, yanayi ne kurum da ke buƙatar haƙuri da kwantar da hankali mafi tsayin lokacin da za ka yi a haka bai wuce mintuna 3 sai dai tabbas akwai firgici, domin kana iya farkowa ka ji kana zufa ko zuciyarka na bugawa farfar. Sannan babu wani alamu dake nuna aljani ne gaskiya, saboda mutanen da kan camfa haka ko zargi ga aljanu ko mayu da sauransu. Kamar yadda kuka ji na ce DISRUPTION ne na REM SLEEP saboda ai wasu dukkan adduo’i suna yi kafin kwanciya amma za ka ga duk da haka suna fuskantar lamarin. Allah ya tsaremu.

Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan 

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceToshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki
Labarin na GabaCututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i