Larabci Da Yanda Ya Shigo Ƙasar Hausa

0
33

Da yake addinin Musulunci yana tafiya ne ɗanɗan da yaren Larabci ta yadda duk in da aka ga ɗaya to ba shakka ɗayan ma ya na nan in aka yi duba na tsanaki, duk da kuwa cewa shi Larabci bai cika neman rakiyar Musulunci ba in yai aniyar shiga wani lardi. Akwai zantuka mabambanta dangane da shigowar waɗannan tagwaye ƙasashen yammacin Afirka.

Ustaz Sa’id Galadanci a littafinsa mai suna (حركة اللغة العربية وآدابها في نيجيريا) ya ambaci wasu hanyoyi da masana suka bayyana cewa ta su ne addinin Musulunci da yaren Larabci suka samu shigowa wannan yanki namu na ƙasar Hausan waccen lokacin. Idan muka ajiye batun shigowar Sahabin Annabi (saw) Wasil bin Aɗa(ra) wanda aka ce shi ne ya kawo Musulunci Afirka ta wannan lokacin, ko in ce aka ce da’awarsa ta dangane da wani yanki na lardin, kamar yanda wasu suka ce Libiya ce ƙasar da ya dakata, amma bayan wafatinsa da’awa ta cigaba har ta mamaye yankin gaba ɗaya.

Duk da cewa ba maganar shigowar addinin Musulunci wannan yanki nake ba, amma babu laifi da na ɗan ci ramaniya na wuce. Ba kamar sauran yankuna da addinin Musulunci ya je musu ta ƙarfi ba, wannan kuma har yankin labarawan mu nan ba a kashe ko daki ko mutum ɗaya da sunan ya yi imani ba, waɗanda suka zo da’awa suka yi ba jahadi ba.

Mu koma ga batun shigowar larabcin da na faro. Maganar da ta tabbata cikin littattafan tarihin zuwan Larabawa wannan yanki ta nuna cewa lalle Larabci shi ya fara zuwa ƙasar Hausa kafin addinin Musulunci ya shigo, domin kuwa a tarihi akwai waɗanda aka kira da “TUJJARU” da kuma “DU’ATU”.

Tujjaru waɗansu mutane ne da suka shigo ƙasar Hausa domin kasuwanci, waɗanda su ne baƙuwar Al’umma ta farko da bahaushen wannan yanki ya fara mu’amala da su daga ƙabilun da ke nesa sosai da ƙasar Hausa. Lokacin da waɗannan rukuni suka shigo ƙasar Hausa sun iske al’ummar da ba ta jin yarenta haka su ma ba sa jin nata yaren.

Manyan abubuwan da waɗannan ‘ƴan kasuwa suke siyarwa su ne dabino da kuma makamai, irinsu masu, takubba da sauransu. An ce lokacin da waɗancan Larabawa suka fara tallata dabinon da suka zo da shi sun fuskanci matsalar saɓanin harshe, wanda kuma shi ne ya ba su haske tun farko kan cewa lalle suna da buƙatar sanin harshen waɗannan al’umma da suka tarar domin sauƙaƙa harkar siye da siyarwa.

Bahaushen wancan lokacin bai san kalar dabino irin na ƙasashen larabawa ba sai a wannan karo dan haka yana da buƙatar farko ya san menene ma tukunna sannan ya siya idan yana da buƙata. Da larabawa suka fahimci Hausawa suna yi wa wannan haja tasu kallon ko meye wannan?

Sai suke amfani da kalmar “KUL” wacce a yarensu ta ke nufin “CI” ma’ana dai ya kai wannan da ya ke kallon wannan abu wanda kallon ke nuna kamar bai san menene ba, “CI” ka ji yanda yake, sai aka yi rashin sa’a domin kuwa kalmar “Kul” a yaren Hausa tana nufin “BARI” ko “KAUCE” ma’ana dai kalma ce da take nuni da hani, a can kuma tana nufin umarni, don haka duk mutumin da ya zo zai sayi dabino sai Balarabe ya ce masa “KUL” sai mutum ya kauce ya ba su guri abinsa, wannan shi ne abin da ya fara haɗa waɗannan yaruka mu’amala.

Su kuma DU’ATU sun shigo ne domin yaɗa addinin Musulunci duk da kuwa an ce waɗancan ‘ƴan kasuwar sun yi abin da suka yi wajen yaɗa Musulunci su ma, musamman yanda waɗanda suka sauke su da waɗanda suka ɗauka yara a kasuwancin da suke suka karɓi Musulunci, amma dai ba kamar yanda DU’ATU suka yi ba, a nan za mu iya cewa DU’ATU su ne kamar missionaries da suka shigo don yaɗa addinin masihiyanci.

Da yake zan yi magana ne a kan alaƙa ba tarihi ba kai tsaye, amma babu lefi idan na tsagaita haka na kuma tunkari abin da zai fisshe ni na bayyana wannan daɗaɗɗiyar alaƙa ta fuskar yare da al’adu.

Kamar yanda yake a bayyane cewa Larabci da larabawa sun samu tagomashin girmamawa da soyayya ne kasancewarsu wasu kayan aiki ko alamomi manya da ke nuni kai tsaye ga samuwar addinin Musulunci a duk bigiren da aka ji ko aka gansu. Wannan tasa yaruka da dama kan saki al’adu wani lokacin ma da shi kansa yaren nasu su rungumi Larabci da al’adun Larabawa a tsammaninsu da ƙoƙarinsu na zama yanda Musulunci yake son su zama.

Misali mu ɗauki yaren Hausa da al’adun Malam Bahaushe, ba na jin a tarihi an taɓa samun wata ba’ajamiyar al’umma da take ganin mutuncin Larabci da Larabawa kamar Hausawa, na san da cewa wasu ma barin yarensu suka yi suka rungumi Larabcin wanda ta kai ga yau babu ɗuriya bare labarinsa. Duk da mu ma ana cewa kaso 60 cikin ɗari na kalmominmu Larabci ne (duk da akwai waɗanda suke ganin adadin bai kai haka ba, kuma sahihin bincike ya gaskata su) wanda hakan ta faru ne sakamakon kasancewarsa harshen ƙetare na farko da Bahaushe ya fara mu’amala da shi.

Daga cikin tagomashin da Larabci ya samu akwai karɓuwar wasu kalmominsa zuwa yaren Hausa kamar yanda na bayyana da farko wanda mai karatu zai so ya san dalilin da yasa ake ganin kalmomin ba na Hausa ba ne asalaninsu, da kuma yanda ake bi a gano.

Ga masu karantar kimiyyar harshe akwai hanyoyi da dama da ake iya gane asalin inda kalma ta tsiro, shigowa ta yi ko ‘ƴarsalai ce, daga cikin hanyoyin da ake bi a gano asalin kalmar Larabci a yaren Hausa akwai la’akari da harufan “AL” (ma’arifa) a farkon kalma, ma’ana kusan duk kalmar Hausa da ta fara da “AL” to ana kyautata zaton balarabiyar Kalma ce asalinta, misalinsu su ne:

1-Alkama – Al-ƙamha
2-Alkaki – Al-ka’aka’a
3- Allo – Al-lauhu
4- Almakashi – Al-miƙsu
5- Albasa -Albaslu.

Amma kuma in muka yi duba ya zuwa irin waɗannan kalmomi za mu ga daman yawancinsu kalmomi ne da suke nufin abubuwan da larabawan ne suka fara shigo mana da shi. Don haka bahaushe yake amfani da sigar da ya ji mai su “Balarabe” yana kiransu shi ma yake kiransu da shi.

Alhamdlilah gwara kalmomi ma daman ana yi domin shi ma larabcin ya aro da dama daga Farisanci, ga wanda yake karantar kimiyyar harshe na Larabci ya san da wannan ƙadiyar. Kuma dama aro ba kashi ba ne ga yare, bilhasli ma duk yaren da ba ya aro to akwai yiwuwar ya mutu.

Danna nan don karanta zuwan ilimi ƙasar Hausa

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Dakta Ado Zakari Kudan
Labarin na GabaTarihin Adamu Yero Hunƙuyi