Barkan mu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake kebab sabon salo a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shehu.
Abubuwan haɗawa
Jan nama kilo
Albasa 1
Maggi 4
Yajin barkono cokali
BBQ sauce chokali
Ƙli-ƙuli (gari)
Kayan ƙamshi
Man gyaɗa ¾ cup
Koren tattasai 2
Yadda ake haɗawa
Da farko za ki wanke namanki, ki masa yanka mai fadi ki ajiye a gefe.
Sai ki haɗa yajin da man gyaɗa da garin ƙuli-ƙulinki da BBQ sauce ki sa maggi da kayan ƙamshi sai ki kwaɓa.
Sai ki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya.
Sai ki kawo baking tray ki sa naman, sai a saka a oven bayan minti 15 sai a duba a juya shi, sannan a ƙara yaryaɗa haɗaɗɗen mai. Kar ki sa wutar ta yi yawa.
Idan ya yi, sai ki sauke, ki yanka daidai misali, ki yanka albasa da koren tattasanki sannan a mayar oven na minti 2-3 sai a sauka domin albasa da tattasai su rusuna.