Kansar Bakin Mahaifa

1
100

Babu takamemen abinda yake kawo ta, sai dai hatsarin kamuwa da ita yana karuwa ga wasu matan kama haka:

  • Macen da aka fara saduwa da ita tun tana da kananan shekaru
  • Mace mai saduwa da maza da yawa
  • Mace mai ciwon sanyi
  • Matan da wata a dangin aka samu mai irin cutar ( Mahaifiya ko yar uwa)
  • Mace mai ciwon HIV
  • Mace mai shan taba.

(1)  Fitar jini daga farji 

  • Bayan saduwa
  • Bayan mace ta tsafa ta daina al’ada
  • Tsakanin al’ada zuwa wata

(2) Fitar ruwa daga farji mai yawa da wari sosai wani lokacin hade da jini.

(3) Ciwon mara

(4) Wani lokacin  yakan zo da yoyyon fitsari ko bahaya ta cikin farji.

Samun wannan alamu baya nufin mace nada wannan cuta ba, sai gwajin likita ya tabbatar, saboda akwai wasu cutukan da kan iya zuwa da haka

Domin karanta bayani akan Ƙurajan Pimples Danna nan

labarin da ya wuceƘurajan Pimples
Labarin na GabaMalaria

SHARHI ƊAYA