Ciwon nono ga ‘yanmata masu ƙananan shekaru yawanci ba ya nuna cewa suna da wata babbar matsala a nonon su. Yakan zamo yana da alaƙa ne da canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinsu (hormonal imbalances). Waɗannan sinadaran suna shafar balaga, jinin haila, ko girman nonon mace.
Yawancin mata matasa suna jin zafin nono ko rashin jin daɗi a matsayin wani ɓangare na tsarin girman halittar jikinsu. Ana kiransa da ciwon nono na lokaci-lokaci (cyclical breast pain), kuma yawanci yana warkar da kansa bayan wani lokaci, ko kuma mace ta ji sauƙinsa bayan ta sami sauyin rayuwa idan ta yi aure.
Amma, idan ciwon nonon ya zamo mai tsanani kuma bai daina ba na tsawon lokaci, ko ya haɗu da kumburi ko wasu canje-canje marasa kyau a nono, ko nono guda ɗaya ya shafa na tsawon lokaci, ko ba yana faruwa ba ne a lokacin jinin al’ada, to, ya kamata ki je asibiti domin likita ya duba ki ido-da-ido.
Sa’annan ya kamata ku san cewa ciwon nono a daidai lokacin mace tana budurwa zai iya zamowa sakamakon abubuwa ne kamar haka:
- Sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinki (hormonal changes), kuma shi ne ake kira “cyclical mastalgia”. Wannan ba matsala ba ne In-sha-Allah.
- Buɗewar fatar ƙirjinki, da kuma haɓakar girman tsokar nononki (developmental stretching of skin and tissues as the breasts grow).
- Tasirantuwar fata da tsokar nononki idan aka taɓa su (breast sensitivity), domin wasu matan ko an taɓa nononsu ba su jin komai, amma wasu ko yaya aka taɓa su, to, suna tasirantuwa sosai. Wannan yanayin halitta ne.
- Rashin samun halittar ƙasusuwan baya, ƙirji, da kafaɗu masu kyau (poor posture). Wannan yana nufin idan halittar ƙasusuwan ƙirjinku, da kafaɗunku, da bayanku sun sunkuya ba su tsaya a tsaye ƙyam ba, to hakan zai sanya tsokoki da fatar nononku su takure, daga nan sai nononku ya riƙa yi muku ciwo a kai-a kai, har zuwa bayanku. Idan haka halittar ƙasusuwan ƙirjinku suke, to, za ku iya samun sauƙin ciwon ne ta hanyar yawan yin atisayen banƙare ƙirjinki da bayanku (postural exercises), tare da zama ko kwanciya a wuraren da bayanku da kafaɗunku ba za su takura ba.
- Canje-canjen nono sakamakon ƙullutun nono (fibrocystic breast changes), wanda yake faruwa saboda kullum fibroadenoma. Fibroadenoma shi ne ƙullutun nono wanda yake sanya tsayuwar nono ƙyam. Wani lokacin yakan kumbura ko ya dinga ruwa, ya haddasa jin zafin nono idan aka taɓa ko ba a taɓa ba.
Don karanta Kumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS) danna nan
Edita@rumasau-kallamu