SALMANU FARISS ADAMU
Ittikafi: shi ne dauwama a masallaci, domin yin ibadah, Salloli da tasbihi haɗi da tahlili, takbiri da salatin annabi da karatu alƙur’ani mai girma da sauransu a cikin masallacin Juma’a.
حدثنى يحي عن مالك عن إبن شهاب عن عروة بن الزبير عن عَمْرَةَ بِنْتُ عَبْدُالرَّحْمَنْ عَنْ عَائِشَةُ زَوْجِ النَّبِيُ صَلَى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهَا قَالَتْ :كَانَ رَسول الله صلى الله عليه وسلم إِذَا عْتَكَفَ يُدْنِى إِلَى رَأْسَهُ فَأُرَجِّلُهُ ,وَكَانَ لاَ يَدْكُلُ الْبَيْتَ إِ لاَّ لِحَاجَةِ الإِ نْسَانِ .
An rawaito daga Yahaya daga Malik daga Ibin Shihab daga Urwata bin Azzubairu daga Amrata binti Abdulrahman daga Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ita ce tace “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) ya kasance, idan yana ittikafi, yana kusanto kan sa kusa da ni (ma`ana sai annabi ya miƙa kansa ta taga, saboda gidansa yana kusa da masallaci ne) sai ta tsattsefe (tatacewa) masa kansa, sannan (annabi) ya kasance ba ya shiga gida, don buƙatar wani mutum”. Idan yana ittikafi.
Saboda haka mai ittikafi ba zai shiga gida ba, don buƙatar wani mutum daban, Haka ma mai Ittakafi ba zai fita cikin masallaci ba, sai don buƙatar kansa kamar su, rashin lafiya, abinci, idan babu mai kawo masa abinci da sauransu.
Bugu da ƙari kuma, mai Ittakafi ba zai tafi ziyarar maƙabarta ba, ba zai tafi zance ba ko gurin ɗaurin aure, ba zai kwana a gidansa ba, sai dai idan a cikin masallaci ne, ba zai yawaita yawan surutu ba, sannan kuma dole ne a kan mai Ittikafi ya nisanci dukkanin abin da ya kamata ya nisanta. Misali kamar su kasuwanci, labaran duniya, kallon tsaraici, maganganun batsa ko kwarkwasa da sauransu.
Haka kuma mai Ittikafi ba zai tafi gida ba, idan an ga wata (shan ruwa), har sai ya dawo daga masllacin idi kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisin na annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), sai dai idan akwai wani dalili mai ƙarfi.
حدثنى يحي عن زياد عن مالك : أنه رأى بعض أهل العلم إذا عتكفوا العشر الأواخرين من رمضان ,لا يرد إلى أهاليهم حتى يشهدوا الفطر مع الناس .
An ruwaito daga Yahaya daga ziyadi daga Malik (yace), haƙiƙa shi ya ga sashin ma’abota Ilimi, idan suka yi Ittikafi na kwanaki goman ƙarshen watan Ramadan, ba sa dawowa gidan su (wajan iyalansu), har sai sun halarci masallacin Idi tare da musulmai.
Sannan kuma babu laifi a kan mace ta yi Ittikafi kamar namiji, idan mace tana Ittikafi, sannan sai hailarta ta same ta a cikin wannan hali (Ittikafi) me za ta yi?, Amsa idan mace hailarta ta same ta a wannan hali za ta koma gida ne, idan ta yi tsarki, sai ta dawo masallaci ta gina ko ta ɗora a kan abin da ya wuce na Ittikafinta, kamar macen da akwai ramuwar azumi wata biyu (60) a kanta, kuma waɗanda ake jera su, sai ta fara ramuwar azumin da ake binta, sai kuma hailarta ta zo mata, sai ta tsaya da yin azumin, idan ta ɗauke mata, sai ta ɗora a kan abin da ta yi na azuminta.
Hakan kuma babu laifi a kan mai Ittikafi yin aure ko Aure, matuƙar ba zai fita cikin masallaccin ba, sannan kuma ba zai sadu da matar ba, har sai bayan ya fito daga masallaci. Bugu da ƙari kuma, an hana saduwa da iyali ga mai Ittikafi da safiya ne ko daddare ne, har sai bayan ya kammala Ittikafinsa.
Sannan kuma babu laifi ga mai azumi, idan yana da mataye ko `yan uwa, sai su kawo masa ziyara cikin masallacin, amma kuma ba za su yi maganar wasa ba ko kwarkwasa.
Har ila yau, mafi alherin Ittikafi kwana goma, ƙarancinsa kwana ɗaya da yini, haka kuma ba a yin Ittikafi sai da azumi, kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a cikin Baƙara ayata (187)
Sannan kuma mai Ittikafi ya shagaltul da karatun Alƙur’an ko nafilfili ko Istigifari ko ambaton Allah (S.W.A) dare da rana. Haka ma ya dage da neman kusanci ga Allah da mazonsa haɗi da neman addu’ar ci gaban addinin musulunci da musulmai da kuma kare su daga sharrin maƙiya da mahassada, domin alfarmar annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla). Bugu da ƙari kuma, babu laifi a kansa idan yana da wasu buƙatu ya roƙi Allah (S.W.A).
Saboda haka Ittikafi yana ɗaya daga cikin manya-manyan Ibada masu girman gaske, sannan kuma shi Ittikafi riba biyu ce ko ma uku, na farko Ibadah ce mai girma, na biyu ga samun ƙarin girma a wajen Allah da manzonsa, matuƙar ya cika sharaɗan Ittikafi, na uku ga samun lada mai yawa haɗi da biyan buƙata da kuma samun farin jini a wajen al’umma da sauransu. Haka ne ma yasa ba kowa ba ne yake iya samun yin Ittikafi, saboda falalar dake cikinsa, saboda duk wanda zai aikata abin da zai nisanta shi daga shiga wuta, sai shaiɗan ya ɗora masa kasala da gajiya, wajen ya ga ya hana shi aikata haka.
Bugu da ƙari ma yana hana su yin aikin alheri kamar su kyauta, sadaka, ciyarwa, nafilfili da sauran su. Saboda haka sai ka ga mutane sun ƙi shiga Ittikafi, har sai ka ga masu shiga Ittikafin sun kammala, sun dawo suna zama tare da su, ka ga su, sun aikata Ibadah mai girma, sannan kuma sun dawo suna zama tare da su.
Daga ƙarshe kuma, ina kira ga waɗanda ba su samu ikon shiga Ittikafi ba, to su samu binci ko abin sha ko kayan marmari, su ba masu yin Ittikafi da sauransu, domin samun falalar da suke cikin, saboda duk wanda ya ciyar da mai azumi, Allah (S.W.A) zai ba shi lada kwatan-kwancin wanda ya yi azumi, ballantana ma a ce ka ba mai yin azumi kuma wanda yake cikin Ittakafi.
Saboda haka ina ba da shawara ga waɗanda suke zuwa Umarah duk shekara, ga wata falala mai ɗimbin yawa, wanda ya kamata su dinga aikatawa, saboda kuɗin da suke kashewa a ƙalla zai iya ciyar da mutane abinci haɗi da nama na mutane guda dubu ɗaya, saboda haka yaya kake tunanin a cikin kowane gari a samu mutane guda goma su aikata haka, mutane dubu nawa ne za a taimakawa, a maimakon su dinga zuwa umrah duk shekara.
Sannan kuma duk abin da mutum ya ciyar da wani mutum, to Allah (S.W.A) zai riɓanya masa sau ɗari bakwai (700) ko ma fiye da haka, sannan kuma ga samun zaman lafiya a tsakanin mawadata da talakawa haɗi da yabo na karamci da addu’o`i a gare su da sauransu. Muna roƙon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ba mu ikon aikata wannan Ibadah ya kuma sa mu dace, Ameen, domin alfarma annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), sannan kuma mutum ya guji yin ƙarya a lokacin da yake yin ittikafi, saboda dukkanin wanda ya yi ƙarya ko kasuwanci ko saduwa da mace ko catin da waya (WhatsApp ko Facebook) ko yawan surutu, to ittakafin sa ya baci, sai ya sake wani, matuƙar ya shagaltu da aikata haka. Wasu malamai suka ce kuma a a, ittikafinsa yana nan, sai dai ya rage ma kansa lada”.
Danna nan don karanta Azumin Watan Ramadan
Edita:@rumasau-kallamu