Ina Son Ɗa Namiji,Sadai Iyalina Mata Take Ta Haifarmun,Shin Meke Faruwa,A Kimiyance Laifin Waye

0
117

Da farko dai kamar yadda nasha faɗa bana raba post ɗin lafiya gida biyu tsarina ne komi yawan sa, domin illar da hakan ka iya haifarwa idan na raba zata fi amfaninsa yawa, saboda ba lallai wani yaga part² ɗin ba inna raba wanda karshenta zai tafi yana kafa hujja da rabin ilimi wanda hatsarin sa gara ace bakasan komi ba tun farko.

Abinda na gamsu dashi shine in abu nada mahimmanci a gareka baka ganin wahalar sa, don haka ya rage naka/ki koh ka tsaya ka amfana ko kai gaba babu me yi maka/ki dole,ita social media free world CE. Ko mutum guda rubutun ya canzawa tunani na riga naci riba, ba yayi ko ra’ayin wani nake bi ba, abinda zanyi ya amfani wanda ma ba a haifa ba a gaba shine burina, asami canji a matsalolin lafiya da rayuwa cikin ƴan arewa,don haka ka iya saving sanda kake free ka karanta,rubutun dai yana nan insha Allahu ko bayan mutuwata, randa ta ciwoka ka dawo ka nema in Allah yayi zaka gansa, inkuma ya ɓace ka amfana da ilimin ƴan baya na lokacinka,don haka bari Mu shiga karatun kai tsaye.

1)-Bisa ɗabi’a na ɗan adam galibi duk namiji zaka samu yana so ace cikin ƴaƴansa akwai namiji wato magajinsa,haka idan kuma ansamu wani ɓangaren maza ake ta haifa babu mace toh cikin matan suma zaka samu suna tsananin son ace sun haifi namiji,wannan na daga buri irin na ɗan adam da babu me iya masa sai Allah, ko Allah ɗin wasu mutanen kan nuna masa rashin haƙuri da gazawa. 

Idan kunaso ka karanta Dalilin Shanyewar ƙafa Bayan Allura A Ɗuwawo Da Yadda Za A Magance Shiga nan

Shiyasa wasu lokutan musamman mutanen da suka rasa tarbiyar addini (domin bazan ce rashin ilimi ba: tunda wasu masu karatu ne saide ba ilimin za kaji suna tafka katoɓara) zaka samu sun ɗau tsana sun ɗorawa matan su saboda kurum Allah ya nufi matar da arziƙin haihuwar ƴaƴa mata,su kuma namiji suke so. Don haka sai su rataya duk laifin kanta batare tunanin Allah ke yin ikon komi ba musamman in akwai sarauta ko wadata. 

2)-Da yawa irin waɗannan magidantan basa shayin fara tafkawa mace rashin mutunci, tsangwama,da zagi wanda duk randa taje bango ta maida martani toh inba Allah ya kiyaye ba saki ne zai biyo baya… koda macen tana musu komi na biyayyar aure domin laifinta agurinsa shine tana ta haifo masa ƴaƴa mata.wanda inda zai saketan abinda ake tsoro sai kaga ya faru,wato tarbiyyar yara matan tazo ta sami matsala tunda ƴaƴa mata antsaya musu tsayema ƴaƴa tarbiyarsu ballantana sun taso babu uwarsu tare da uban. 

3)-Toh saide batun tsayawa kana tunasar dasu cewa daga Allah ne wasu son zuciya baya barinsu,wani zai hakura amma Inyaga a ƙara haihuwa 2 babu abinda yake so toh hakurin da yai abaya zai ƙare aga ya kuma fusata, domin wasu da ilimin su inkai wasa ka jawo aya ma suna iya ƙarasa ma saboda isgili..sai dai Kamar yadda Allah ya faɗa shine me baiwa kowa duk irin jinsin da yaso: inyaso ya baka ƴaƴa mata kamar yadda mukaji Annabi Ayyuba duk ƴaƴansa mata ne da Annabi shu’aib (AS),haka inyaso ya baka ƴaƴa maza kamar Annabi Yaqub (AS) da duk ƴaƴansa maza ne,ko kuma ya gauraya maka mata da maza kamar annabi Muhammad (SAW).

Toh saide tunda galibi in ance Allah yace annabi yace son zuciya bai kyale mutane karɓar gaskiya.bari mu dubi abin a kimiyyance ko kuma a likitance.

Domin karanta Matsalar Zubar Yawun Bacci Danna nan

Shin Haihuwar Ƴaƴa Mata Laifin Waye A Tsakani?

4)-Bisa Ƙudura ta ubangiji ya halicci jinsin maza dana mata kowannensu dauke da sinadaran halittar wato ƙwayaye (Ovaries) ga mace tare kuma da maniyyi (Sperm) domin mu hayayyafa da irin jinsin da yai daidai damu wato haihuwar ƴaƴa masu suffar mutane ba dabbobi ko aljannu ba,wanda cikin waɗancan sinadarai ake samun abinda muke kira (chromosomes) wato wani ɗan ƙanƙanin ƙwaya mai kama da zare cikin ƙwayoyin halittar ɗan adam wanda ke kunshe da sinadarin gado (Genes).  

Shi wannan chromosomes nau’i biyu ne

Akwai rukuni me suffar (X’) dake wakiltar mace 

Da kuma  na suffar (Y’) me wakiltar namiji. 

Ita mace asalin halittar ta dama daga namiji Allah ya fidda ita wato (ANNABI ADAM (AS)) hakan yasa ita (X’) ce dama ta sahin namiji amma don ya ƙara cika suffarta sosai ta MACENTAKA sai Allah ya ƙara mata da copy na (X’) wato ta zamo (X’X) wato guda biyu. shiyasa bazata taɓa mikewa ta zama namiji ba domin X a karkace jelar take ta ko ina. 

5)-Shi kuma abu ba’a kamantuwa dashi batare da anrasa alaqa ba,shiyasa wani kai da ganinsa kafin ace ɗangidan wane ne zaka ji tuni kaga kama dama.

Wannan tasa zamu fahimci a farkon halitta mace bazata fito jikin namiji (Adam) ba dole sai in akwai sinadarin macen a jikinsa wanda kuma hakan ne,domin Allah ya sanyawa namiji copy na (X) chromosome shima,sannan domin tabbatar da suffarsa ta MAZANTAKA sai ya ƙara masa da copy na (Y’) don haka sai ya tashi da copy biyu wato (XY) ita kuma mace (XX) kamar yadda nace abaya.

6)-Wannan tasa duk inda juna biyu zai shiga tsakanin mace da namiji kowa zai saki kwafi (copy) na chromosomes dinsa guda ɗaya…wanda abinda kowa ya saki matsayin copy ɗin shine zai zamo jinsin abinda zasu haifa cikin ikon ubangiji,wato kunga kenan ita Mace dai ko yaushe dama copy dinta dole X zai zama ta saki tunda duk (XX) ne da ita, kai kuma namiji kode ka saki kwafi na ‘X ko ka saki Y’ tunda (XY) gareka,kunga kenan acikin [X’X] kowanne copy mace ta saki “X” dai zai zama don haka babu ayar tambaya akanta domin walau ciki ya zamo namiji ko mace ita NEUTRAL CE kowa na bukatar ta bashi (X’).

Shiyasa:

  • Idan mace ta saki copy na (X’) kai kuma namiji ka saki kwafi na (Y’)  abunda za’a haifa zai zamo (XY) wato ɗa namiji irin ka. 
  • Idan ta saki copy na (X) shima namiji ya saki copy na (X) daga cikin (XY) ɗinsa abunda za’a haifa zai zamo (XX) wato mace.
  •  Idan kuma akai dace cikin maniyyi da kasaki chromosomes ƙwaya 2 ne suka wuce suka barbari ƙwan acmen..wato ubangiji ya nufaci halittar ƴan biyu (twins) shine: idan copy na (X) namijin ya saki, sannan na biyu ma ya zamo copy na (X) ne ya wuce to duk yan biyun sai su zamo (xxxx) wato ƴaƴa mata.
  • Toh idan kuma copy na (X) namijin ya saki a sperm cell din farko, sannan na biyu ya zamto ya saki copy na (Y’) toh ƴan biyun sai su zamo mace da namiji.hakazalik idan kuma copy na (Y’) ya saki a farko, sannan na biyu ya zamto ya kuma sakin copy na (Y’) toh ƴan biyun sai su zamo maza baki ɗaya.wannan shine duk abinda zaita faruwa koda ƴaƴa nawa Allah ya nufa za’a haifa.
Idan Har Kun Fahinta Da Kyau

7)-Zaku ga kenan ita mace standard (XX) ce babu ruwanta ko laifinta ga me da rashin haihuwar maza inma dame laifi toh kaine dake sakin copy ɗin (X) maimakon (Y). 

Inko ka yadda kaima ba laifinka bane domin ba ikon ka bane ikon sanin wanne copy ka saki na Allah ne toh ya dace ka hakura ka yadda kuma ka gamsu kai godiya da abinda Allah ya baka,wasu haihuwar ma kwata-kwata suke nema ma sun rasa, duk wani asibiti da ya amsa sunansa sun je abin yaci tira. 

Duk Da Haka Wani Zaice Taya Wannan Sakin Copy Din Ke Faruwa 

8)-Wani ka iya tambaya shin taya wannan copy din ke faruwa? Shin ko akwai yadda mutum zai yi tunda yanzu angano namiji ne keda tasirin sakin copy ɗin samar da mace (X) ta yadda inya kama zai iyayin wani abu dazai ƙara masa chance din sakin copy ɗin (Y’) Namijin ?

Abin da nakeso kowa ya fahimta anan shine; duk da abayanin baya nace ko dai namiji ya saki copy na (X) ko kuma ya saki (Y’)…… Hakan fa baya nufin copy guda-guda kurum namijin ke saki ba,a’ah akalla X da Y namijin na sakin kwaya 23, itama macen ta saki 23 wanda total ke kamawa 46 a acikin kowanne kwayar maniyyi wanda akalla namiji na sakin maniyyi kwaya milyan 30 a release ɗaya da yai tak kuma kowanne na iya ƙyanƙyashe ƙwan mace ya zamo ɗa ko ƴa,

Wani me wadataccen ruwan maniyyin har milyan 200, 120, 100, 80, 70 yana saki, wanda rankatakaf inda duk zasu shiga su ƙyanƙyashe ƙwan macen to mace zata haifo ƴaƴa milyan 120 ne a haihuwa 1 tak lokaci guda,domin a milyan 120 ko 100 din nan kowanne guda yana da chromosomes 23 kaga ya kama kwaya milyan 2760 kenan.

Baka iya yiwa mace ciki sai kana iya samar da akalla kwayoyin ruwan maniyyi Milyan 25, duk da ƙwaya 1 ne tak zai bada ciki.Duk Maniyyin da yai kasa da milyan 15 ya zama low sperm count bazai iya ma mace ciki ba sai antaimaka masa.Duk golo daya na samar da maniyyi milyan 60 kullum Total 120, shiyasa 120/4 = 30million, namiji na iya yiwa mata 4 ciki dare daya, hikimar a auri mata 4 ta fita. 

Namiji ko ƴaƴan Maraina (golo) 1 garesa zai iya ma mace ciki normal, kamar yadda mace me follopian tube 1 ke iya haihuwa.

Amma hikima ta Ubangiji sai yasa koda namiji ya saki wannan milyoyin na (X da Y) chromosomes cikin Sperm cells ɗin iya wanda akai rige-rige ya fara zuwa ya tarar da ƙwan macen acikin mahaifa bayan tai ovulating shine zai zama wanda zatai fertilising ta haifa,. 

Wato de duk namijin na sakin X&Y copy amma idan copy na (X) ya riga shiga cikin ƙwan mace toh abinda za’a haifa mace ne, idan kuma (Y’) ne ya riga toh zai zamo namiji.

9)-Sannan wani abu da nake so ku hararo hikimar Allah shine yayin da namiji ya saki kwayoyin maniyyin sa me kunshe da chromosomes ɗin kada ku kalli abin a matsayin tseren gudu tsakanin X&Y chromosomes kurum a’a ku ɗauka tsere ne tsakanin rukunonin mutanen da muke rayuwa dasu da muƙamansu ko irin aikin su ayau cikin al’umma kamar:

 Wani Gwamna ne in ya riga shiga,wani police,wani soja,wani malamin addini,wata ƴar sanda,wani shugaban kasa,wata matar shugabar kasa,wani minister,wata director,wani likita,wata ma’aikaciyar lafiya,wani record officer,wani dan kasuwa,wani laboratory scientists, wani marubuci,wani me ilimin haɗa magunguna,wani preventive health officer,wani ɗan film, wani ɓarawo,wani ɗan kidnapping,wani kafiri,wani musulmi… Toh haka dai tseren yake based on abubuwan da muka suffanta dasu. 

Idan (X) na mace malamar makaranta ya riga (X) na macen da zata zamo Likita shikenan sai ubangiji ya lalata Copy din mace likitar tunda na malamar makaranta ya riga shine zaka ga duk wanda ya taso kowa burinsa daban,ba lallai kowa yaso course ɗin da wannan keso domin Allah ya raba.

Wannan yasa dole ka godewa Allah domin akalla inma baka da wadatar ruwan maniyyi ingantacce dai kana iya samar da milyan 30,kaga kenan ya kashe sama da copy milyan 29 da dubu 900 da 99 domin a haifoka kai kaɗai, ko kuwa a haifo ma abinda kake raina wa. kaga ko lallai akwai hikima ba haka banza ba, bai kuma dace ka saɓamasa ba inda kasan alfarmar da yaima musamman da yayoka cikin musulunci.

Ya Suffufin [X&Y] Ɗin Su Ke

10)-Bisa suffa su wannan copy na (X) & (Y) chromosomes sun bambanta.

  • Copy na (Y) me wakiltar namiji ya kasance mara nauyi saboda baida kwayoyin gado masu yawa,gajere,me gudu ko ince sauri,amma kuma yana da saurin mutuwa,saurin lalacewa domin baya iya jure mawuyacin hali yakan mutu nan da nan saɓanin (X).  
  • Yayin da copy na (X) me wakiltar mace keda tsayi da nauyi, da juriya gami da girma domin ya ninka Y sau 5,yana da kwayoyin gado sama da sau 10 na Y wannan tasa baida saurin lalacewa,saidai  baida gudu kamar (Y) amma saurin sarewar da (Y) keda shi da saurin lalacewa shine yasa (X) galibi ke penetrating din ƙwan mace idan namiji yai release.Juriyar da (X) keda ita fiye da(Y) yasa kaga kana ta haihuwar mata,yakan iya jure awa 24 zuwa kwana 3,mahakurci mawadaci, koda farji ya zama acidic X zai rayu, yayin da Y shi malalaci sai ya sami farjin dake jiƙa sosai da majina bakin mahaifa sannan zai sliding ya riga. 

Wannan kuma nufin Allah ne da yasa kai dake ta haihuwar mata copy din (X) ɗinka keta fin (Y) wanda  hakan bata faruwa toh kila zama ka tashi ne baka da haihuwar ,eh mana tunda Y yana saurin lalacewa shima X ya zama haka kaga bakai ba iya yin ciki kenan.

Saide ko a likitanci ƙwai tarin abubuwa masu yawa da Allah bai kai ga samu mun fahimci me yasa da kuma yadda suke faruwa ba saide muce (UNKNOWN CAUSE) amma ga wasu abubuwa da sukan taimaka hakan ta faru wato risk factors da ke ɓata tafiyar (Y). 

11)-Babban abinda yakan taka rawa wanda mutane basa ganinsa a komi yau shine ORAL SEX, da yawa basa shayin doɓana baki suce zasu tsotsi farjin mace wajen saduwa,saidai abomination ɗin dake faruwa anan shine: farji ba muhalli ne sinadarin zafi ko ince guba ba wato Acidic Environment, shi farji alƙaline  ba zafi ba sanyi madaidaici yanayi wannan tasa ko an zuba maniyyi yake tafiya lafiya batare da ya lalace ba.

Yayin da shi kuma miyau (saliva) dake fitowa daga baki kunga acid ne yana da guba da sauran sinadaran enzymes dake taimakawa wajen narkar da abinci… Toh miyau din da kake samata dalilin tsotse-tsotsenka wajen jima’i yana taka mahimmiyar rawa wajen lalata quality wato ingancin ruwan maniyyinka inkazo jima’i kwarai da gaske,domin ka canza farjin daga pure alkaline ya zama combination na more acid environment wanda musamman (Y) chromosomes yadda yake da saurin lalacewa,ga rashin nauyi,ke shiga wani hali ya zamto ya mutu sai (X) me juriya ne zai amfana sakamakon nauyinsa da juriya wato shi (Thick, heavy, longer and sluggish) ne 

Domin karanta bayani akan Idan Kaji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan

12)-Wannan tasa ayau ansami ci gaban da a maimakon zaman ɓacin rai ga wanda suke son su zaɓi gender na yaran da suke so anyi cigaban da mutum na iya zuwa asibiti inyaso sai a dau sample na Maniyyin sa azaɓi chromosomes din da akeso ƙwan mace ya ƙyanƙyashe abinda ake kira (Pre-implantation genetic diagnosis sex selection) shikenan sai a haifo namijin da kake so duk da Allah na iya ikonsa amma 100% na zamowa namijin.

Toh saide tunda dai musulmai nake magana ita wannan hanya malamai na musulunci sun saɓani kan amfani da gender selection haka kurum, domin ko baya bayan nan anyi debates me zafi tsakanin malaman addini a jami’ar Oxford dake England inda kaso mai yawa sun tafi kan haramcinta duba da hakan zai iya kawo yawaita wani jinsi tare da ɗaƙile wani, wanda hakan zai kuma maida mutane rayuwa irinta jahiliyya abaya wato tsanar wani jinsi, wanda shi yasa ayau inba kasar India ba babu wata kasa da kusan zaka samu Maza sunfi mata yawa amma ai kwai hikima hakan.

13)-Saide duk da haka malamai sun gamsu akan amfani da wata hanyar wacce ba waccan ba ta hanyar amfani da natural selection da ba wata na’ura kamar:

  • Yin jima’i a wani keɓantaccen lokaci irin (nan da nan sanda mace tai ovulating kasa da awa 12 ko yini guda ko kuma dab a sanda takeyin) kamar yadda ake ganin hakan nasa (Y) amfani da saurin sa ya riga (X) a irin wannan lokaci saboda mace hatta sha’awarta ƙaruwa take, jikin ta na canzawa,nonuwa sui nauyi, taji tana fitar da ruwan majina-majina fari me yauki wanda wannan yanayin (Y) ya keso yanzu yacewa X naga a yai gaba.
  • Kamar yadda nasha faɗa Ovulation na faruwa sati 2 da gama haila galibi. Idan cycle dinki kwana 28 ne ovulation kan kasance kwana 14 da gama haila, me kwana 21 wato sati uku (yakan fado rana ta 10 da kammala haila, ko kuma mace tai amfani da ovulation kit tai tracing. Inde ana son namiji wannan shine perfect time. 
  • Ko ta hanyar zuwa asibiti wanke mahaifar mace da ake gab da ovulation (irrigation) domin rage ACIDITY na cikin mahaifa wanda zai ba (Y) chromosome damar saurin fertilising egg.
  • Ko rika cin wani abu na daga abinci: wato cin abinci me yawan gishiri da sinadarin kanwa-kanwa (High sodium & potassium) tare da kuma cin abinci me karancin sinadarin calcium da magnesium wato dai ana son cin irinsu: (bananas,cherries, grapes,oranges,plums,watermelon,broad beans,cabbage,celery,tomatoesand corn)
  • Ko salon kwanciya musamman missionary position idan akai amfani da flow daidai ƙugun mace aka san ɗaga hips din yadda da zarar namiji yai release zai ƙwarara bakin mahaifa wanda Y zai amfani da saurin sa ya riga (X) 

14)-Don haka malamai sun halatta waɗannan hanyoyi toh amma ko su ɗin sunce su na halasta ne ga mutum muddin ba tsanar haihuwar Ƴa macen ko jinsin ta yasa haka ba,wato dai sun kafa hujja da ayar da tazo cikin ƙur’ani dake nuna Annabi Ibrahim da Annabi Zakariyya (RA) duk sun roki haihuwa kuma addu’a anji ɗa suka nema wanda yafi nuna rinjayen addu’ar ga namiji ba mace ba,amma kuma basuyi hakan don basason mace ba. 

Sannan malaman suka ce dole kuma in namijin bai samu ba nan ma baza a zubar da cikin ba don mace ce, haka zalika ya zamto dole maniyyin namijin da mace ke aure ne domin su sauran waɗancan mutanen aboki na iya ba aboki ko ɗan uwa kyautar ruwan maniyyi shi inyana da matsala asawa matarsa don su haihu bayan sun zabi gender amma mu wannan haramun ne a musulunci. 

Amma kuma zaɓen ya halasta idan ya zamto angaji wasu cuttuka a dangi da ƴaƴa mata kurum suke farwa (x-linked recessive disorders) da sauransu.

Domin karanta Bayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation} Danna nan

labarin da ya wuceBayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation}
Labarin na GabaLarurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma)