Tambaya
Asslamu alaikum Malam. Lokacin sallah ne ya yi, na je na yi alwala na tayar da sallah, to, ina cikin sallah sai na tuna akwai najasa a zanina, don Allah yaya zan yi, zan sake sallar ne ko yaya?
Amsa:
Wa’alaikumus salam Warahmatullah, irin wannan tambayar an yi wa SHEIKH ABDLH IBN ABDIRRAHMAN AL-JIBRIN ga amsar da ya bayar.
Wanda ya yi salla da najasa kuma da saninsa, sallarsa ta ɓaci, in kuma bai sani ba, sai bayan ya sallame to sallarsa ta yi, ba a lazimta masa biya ba.
Amma in yana kan sallar, sai ya san akwai najasa a tufarsa, in zai yiwu ya cire ta da wuri, ya ci gaba da sallarsa, to ya halatta, domin ya tabbata ANNABI (S.A.W) yana salla watarana da takalmi sai Mala’ika JIBRIL ya sanar da shi akwai najasa a takalman.
Nan take ya cire takalman, ya ci gaba da sallarsa, ba tare da cewa farkon sallar da yayin da takalmin ya lalace ba, haka ma in ya tuna najasar yana jikin rawaninsa sai ya cire rawanin ya ci gaba da sallar.
Amma idan cire abin da yake ɗauke da najasar, yana buƙatar dogon aiki, kamar kwaɓe riga ko wando ko makamancin haka, to bayan ya kwaɓe ya fara salla daga farko.
Don haka, baiwar ALLAH kin ga cire zani da sauya wani zanin a daura dogon aiki ne, sai ki canza ki fara salla daga farko,
BARAKALLAHU FEEK.
Domin sanin Nasabar Manzon Allah danna koren rubutun nan