Hucewar Zazzaɓi (HERPES SIMPLEX)

0
17

Hucewar zazzaɓi ko kuma wucewar zazzɓi ana kiranta “fever blisters” ko “cold sore” a likitance. Fever blisters wasu ‘yan ƙananan ƙuraje ne a cure a wuri ɗaya kuma suna gundar ruwa. Suna fitowa a gefen baki ne. Wasu ƙwayoyin cuta da ake kira herpes simplex virus (HSV) ne suke haddasa shi. Virus ɗin sun rabu gida biyu:

1. Herpes simplex virus type 1 shi ne wanda yake haddasa fitowar hucewar zazzaɓi a baki, kuma ana iya ɗaukarsa ta hanyar sumba (kiss).

2. Herpes simplex virus type 2 shi ne wanda yake haddasa fitowar hucewar zazzaɓi a al’aura, kuma yana ɗaya daga cikin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i (sexually transmitted diseases).

Herpes simplex virus type 1 da type 2 sukan warkar da kansu ba sai an yi amfani da magani ba. Amma idan abin ya ta’azzara, to, sai a tuntuɓi likita domin ɗaukar matakin da ya dace.

Bincike ya nuna cewa akwai ƙwayoyin herpes simplex virus type 1 a cikin bakin mutum, sai dai ba su da wani tasiri (inactive). Amma a lokacin da mutum ya yi fama da wata jinya kamar zazzaɓi ko mura, to, garkuwar jikinsa za ta yi rauni. Daga nan fever blisters za su iya fito masa.

Amma ya kamata mu fahimci cewa abubuwan da suke sanya fever blisters sun bambanta daga mutum zuwa mutum, kamar haka:

1. Raunin garkuwar jiki (weak body immune system) ko da kuwa a zahiri mutum bai ji alamar wata rashin lafiya ba. A lokacin da garkuwar jikinsa take da ƙarfi, takan yaƙi dukkan wasu ƙwayoyin cuta. Amma idan ta yi rauni saboda kamuwa da wata rashin lafiya, kamar mura ko zazzaɓi, to, herpes simplex zai iya tasowa. Shi yasa ma ake kiransa hucewar zazzaɓi.

2. Sauye-sauyen zubar sinadarai (hormonal changes). Mace, takan fuskanci sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a lokacin al’ada, ko saka ƙwan haihuwa, juna biyu, ko shayarwa. Sa’annan idan mace tana fama da matsalar kumburin jakar ƙwan haihuwa (polycystic ovarian syndrome – PCOS) za ta fuskanci sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai a cikin jikinta. A waɗannan lokutan, za ta iya fuskantar herpes simplex. Shi kuwa namiji, zai iya samun herpes simplex ne idan ya sami sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran testosterone, ko cortisol, ko thyroid.

3. Yanayin muhalli (environmental factors), yana iya tayar da herpes simplex, kamar tsananin zafin bazara, ko tsananin sanyin hunturu. Sa’annan gurɓacewar yanayin muhalli da ƙwayoyin cuta, ko ƙura duk suna iya tayar da shi.

4. Gajiya (fatigue), sakamakon yin ayyukan wahala, ko rashin barci zai iya rage ƙarfin garkuwar jiki, kuma ya bayar da damar tasowar herpes simplex.

5. Damuwa (stress), sakamakon matsalolin tattalin arziƙi, ko rashin zaman lafiya da iyali, ko rashin wani muhimmin abu a rayuwa duk za su iya haddasa raunin garkuwar jiki da kuma tasowar herpes simplex.

6. Laulayin magunguna (side effect of drugs), domin wasu magungunan suna iya jirkita daidaiton zubar ruwan sinadaran jiki kuma su raunana ƙarfin garkuwar jiki. Daga nan sai herpes simplex ya taso. Misalinsu shi ne magungunan hana kumburi (corticosteroids) kamar prednisone da methotrexate, ko magungunan cutar cancer (chemotherapy drugs) kamar cyclophosphamide da doxorubicin da methotrexate, ko magungunan kashe cututtuka (antibiotics) kamar tetracyclines, ko magungunan dashen sassan jiki (antirejection drugs for transplant) kamar cyclosporine da tacrolimus.

Babban maganin fever blisters shi ne mutum ya yi ƙoƙarin lura da abubuwan da idan suka same shi suke haifar masa da su, domin kauce musu.
Danna nan don karanta Fitowar Haƙora Ga Yara, Faɗuwarsu Da Sake Fitowarsu

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFalalar Tasbihi
Labarin na GabaYadda Ake Biskit Cikin Sauƙi