Hatsarin Yin Wasa-rere Da Hawan Jini

0
20

Kamar yadda kwanaki kuka ji na yi bayani kan ciwon sugar cewa shi ne kan gaba wajen haddasa chronic kidney failure toh Hawan jini shi ne a matsayi na biyu da ke take masa baya wajen lalata ƙoda.

Nephr(o)tic syndrome shi ne abinda ciwon suga ke jawo wa wanda nace muku in an yi gwajin fitsari ga wanda ƙodar ta fara taɓuwa za a ga sinadrin Protein ko Albumin a ciki ba ya ga hauhawar serum Creatinine da kumburi a ƙafafu ko ciki a wasu lokutan in ya yi ƙamari.

To a masu Hawan jini kuma Nephr(i)tic Syndrome shi ke faruwa. Su kuma a fitsarin abinda ake gani shi ne jini wato cast na Red blood cell. Wani ƙila zai ce ai fitsarina koyaushe yellow ne ko kuwa fari tas don haka babu alamar jini. Ina ba haka abin yake ba.

Akwai jinin da in abin ya yi ƙamari kai da kanka za ka ke ganin fitsarinka ya canza wannan shi muke kira GROSS HEMATURIA toh amma akwai wanda ba za ka taɓa gani ba sai an yi urinalysis, gwajin fitsari an sa High field microscope shi ne muke kira MICROSCOPIC HEMATURIA. To wannan fa shi ke nuna cewa hawan jini ya fara cin ƙodar mutum dole ne ya yi wani abu, in kuwa sai bayan abu ya ɓaci aka farga toh gaskiya in dai ya fara shiga Chronic sai dai a yi management ai ta ƙoƙari. Amma in yana Acute Kidney disease akan yi nasarar ƙwato ƙodar ta hanyar control na hawan jinin da sauran maganin da zai aiki a ƙodar da kuma canza abincin mutum zuwa KETO DIET

Hawan jini abu ne mai hatsari idan aka yi sake da shi to fa ba ƙoda ba a hankali zai lalata ƙwaƙwalwa, yana motse jijiyoyin jini ta kai ga haddasa shanyewar ɓarin jiki, cutar mantuwa, lalata ido yadda mutum zai sami Retinopathy ya makance, da uwa uba bugun zuciya ko heart attack ko heart failure ko Coronary artery disease wanda duk sanda aka kai haka musamman zuciya, to fa mutum ba shi ba kuma yin duk wani aiki da ya saba sai dai a ƙiyama domin ya nakasa abin da yake jira shi ne mutuwa.

Yawanci ciwon zuciyar ya fi faruwa bayan an ba shekaru 50 baya. To amma fa yanzu ga shi hawan jini da sai an ba shekara 40 baya aka fi samu amma yanzu har yara ƙanana masu ƙananun shekaru fama suke.

‘Yan Shekara 20 da wani abu ko ‘yan goma sha sai ka gan su da hawan jini. Wasu kuma basu ma san suna da shi ba har yau. Babbar illar hawan jini shi ne ba za ka taɓa jin alamun rashin daɗi a jika ko kana da shi alhalin cikin jikinka yana ta maka illa, shi yasa ake kiransa da silent killer.

A sabon jadawalin da AMERICAN HEART ASSOCIATION ta fitar yanzu kafin tabbatar da hawan jini sai an auna mutum a lokuta 2 zuwa 3 mabambanta na rana guda idan har an sami Bp ɗinsa sama da 140 to tabbata yana da hawan jini. Wajibi a ɗora shi kan magani.

Amma yawanci akwai wani abu da nake musamman ƙananun ma’aikatan lafiya su sani duk inda kuka ga mutum ɗan ƙasa da shekaru 10, ko 20 ko ƙasa da 30 ɗauke da hawan jini kai ko da ya ba wa 30 baya da kaɗan toh ku yi hanzarin tura shi ya yi KIDNEY FUNCTION TEST musamman a yara ‘yan goma sha yawanci ciwon ƙoda ne ke haddasa hawan jininsu.

Da an je an yi gwajin fitsari da Blood chemistry za ka samu CREATININE ɗinsu ya yi High ana fara ba su magani insha Allahu shike nan za su sami lafiya, ciwon ƙodar zai kau sannan hawan jinin ma zai tafi dama ciwon ƙodar ne ya kawo shi. Wanda in kuwa ka fara ɗora mutum a maganin hawan jini to fa kullum a magani zai tafi alhalin an bar tushen matsalar ƙarshen complications ɗin ya kashe shi.

Na faɗa muku da yawa ciwon ƙoda sai ya yi muni ake jin alamu. Sai dai a yara masu High Bp idan ƙodar ta taɓu wasu ana ganin kumburin fuska da ƙafafu kai tsaye.

Akwai wani bawan Allah da ya rasu a Kano satin da ya wuce sakamakon ciwon ƙoda na ga labarinsa inda aka riƙa neman milyan 15 don kai shi India a yi masa dashe. A bayanin da ya yi farkon matsalar hawan jini ne tun a 2001 yace bai sani ba sai da aka duba jininsa lokaci har 220 ya je. Tuni ya ɓata ƙodar amma saboda in pressure ta yi pressure ƙwaƙwalwa ma daina kai saƙo take shi yasa wani za ka ga jininsa a 160 ko 180 amma yace shi ai ƙalau yake jinsa ba abin da yake damunsa.

Shi ma ɗin to zuwa 2006 shekara 5 kaɗai duk ƙodojinsa biyun suka kasa, a nan ne ya samu aka masa dashen ƙoda ɗaya, aka cire ɗayar Allah sarki zuwa 2010 shekara 4 kacal saboda na faɗa muku in aka sama Organ ɗin wani ba kurum sawar ba akwai Rikicin Rejection da garkuwar jikinka za take yaƙar organ ɗin toh shi ma ya sami CHRONIC REJECTION shekaru huɗu ƙodar da aka sama ta mutu, shi ne fa yake ta fama har zuwa yanzu da Allah ya karɓi ransa.

Yace daga wannan lokaci zuwa sanda yake kwance yana neman taimako an masa wankin ƙoda sama da sau dubu ɗaya da ɗari huɗu da sabain da uku, inalillahi wa’inna ilayhir rajiun. Ya sha wahala ban da ciwon cancer na ƙoda da za ka iya haɗuwa da shi a sakamakon dialysis ɗin kanshi tare da ƙarancin jini.

Don haka kuskuren da ƙananun ma’aikatan lafiya kuke ku gyara, kukan rubutawa me hawan jini maganin sha na kwana 10 ya tafi kurum shikenan ko ya aka duba aka ga jini ya yo kasa, ba kwa kuma faɗawa mutum me ya dace ya yi ko ya kiyaye. To ku sani da maganin ciwon sugar da na hawan jini shan su ba ya ƙarewa har ƙarshen rayuwa kullum ne kuma ko da jini ya dawo normal level in dai ba ƙasa da 90 aka ga ya tafi ba, ba za a taɓa cewa ka ɗaga ƙafa ba. Sannan wajibi ne kafin ka ba mutum kowanne irin maganin hawan jini ya zamto kana da masaniya a kai da side effect, dose ɗin da ya dace da kuma HALF LIFE na maganin wannan wajibi ne.

Wani combination wani kuma magani ɗaya ne. Don haka a ƙalla ka rubutawa mutum maganin wata 3 wato kwana 90 in ya kare a kuma ƙara masa haka za a yi ta tafiya, kuma za a ci gaba da bibiyarsa, shi yasa muke cewa a sayi abin gwajin mutum ya riƙa recording a littafi duk sanda zai zo asibiti ya zo muna da shi muke ganin progress ɗin.

Don haka kar ku yi sake da hawan jini ku kiyayi gishiri; yawancin maiƙo da su chocolates. Kar don kuna shan magani ku ɗauka za ku ci komai musamman mu baƙaƙen fata da hawan jinin mu bai fiye jin magani ba sai an yi da gaske abu kaɗan na sa shi ya hau.

Idan ka kula da kanka za ka rayu cikin aminci kamar kowa kuma hawan jini ba zai ma illar can ba. In ko kai wasa toh sai dai Allah ya tsare. Allah ka yaye mana abinda ya dame mu amin.

Domin karanta Hawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu danna nan

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAzumin Watan Ramadan 2
Labarin na GabaYadda Za Ka Haddace Al-ƙur’ani Cikin Sauƙi Daki-Daki