Yan uwa sai mu kula a duk lokacin da muka ga an jirkita ayar Alƙur’ani ko an haɗa ta da najasa ko wata ƙazanta.
Ko an ce mu yanka wata dabba mai siffa kaza, ko mu rubuta wasu alƙaluma da haruffa; ko sunaye marasa ma’ana. Ko an ce mu binne a wuri kaza, ko mu ƙona abu kaza ko; kuma a ce mu je wuri kaza, lokaci kaza, mu yi wani abu.
To wannan alama ce da ke nuna amsa umarnin aljannu da neman biyan buƙata daga wanin Ubangiji Maɗaukakin Sarki; kuma shi ne shirka. Yin hakan kuwa kafirci ne.
To ka ga ya zama haramtaccen laƙani ko asiri ko ma kai tsaye mu kira shi tsafi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Shin Me Ne Ne Tsafi Ko Sihiri? danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Shin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya? danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr.Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.