HARAMCIN DAKE CIKIN ƊAUKAR HOTO KAFIN AURE

0
91

Daga Huzaifa Mukhtar Muhammad

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

Wata babbar matsala da al’ummarmu musamman matasa suke fuskanta a zamanin yau shi ne ta’adar yin hoton kafin aure. Wanda mutane suka ɗauke shi a matsayin kwalliya ko burgewa da kuma wayewar zamani. Hotunan kafin aure ɗabi’a ce ta Turawa wadda muka kwaikwayo kuma haramun ne.

Biyan sadaki kaɗai ba ya tabbatar da halaccin aure idan babu siga da kuma shaidu. Duba da haka don mutum ya biya sadaki ba shi da damar ɗaukar hoto kafin aure da wacce zai aura,har ta kai ga riƙe hannu ko runguma, wanda addini ya haramta hakan matuƙar babu aure.

Idanunmu sun rufe da kwaikwayon salon Turawa, mun sauka kuma mun manta da koyarwa ta addini da tarbiyya ta al’adarmu.

Allah maɗaukakin sarki yana cewa a cikin Qur’an: “Su (matayenku) suturarku ne haka zalika kuma suturarsu ne”. (Qur’an 2:187)

Wannan ayar ta sama ta nuna ƙarara matsayin miji ga matarsa ba a ce saurayi da budurwa ba. Tunda Allah ya ce ma’aurata suturar junansu ne, to babu dalilin da zai sa mutum ya je yana ɗaukar hoto da matar da ba tashi ba har da riƙe ta da kuma rungumar ta, ƙarshe a yaɗa shi a kafafen sada zumunta da sunan gayyatar ɗaurin aure.

Allah maɗaukakin sarki ya sake faɗa a cikin Qur’ani cewar:”Duk matar kirki mai tsananin biyayya ce (ga Allah da kuma mijinta) kuma mai tsayawa ce ga mijinta a kan duk abinda Allah ya yi umarni”. Misali mai kare masa mutuncinsa da kuma dukiyarsa ( Surah_An-nisa’i 4:34).

Ɗaukar hotunan aure tsakanin miji da mata da kuma yaɗa su a shafukan sada zumunta bai kamata ba kuma bayyana sirrin aure ne. Hakan yana zama kamar tsokanar Allah ne wanda zai janyo rashin zaman lafiya da rushewar zaman gidan aure.

Ku jira a ce kun zama ma’aurata sai ku ɗauki hoto iya son ranku sannan ku ajiye su a wajenku ku kaɗai.

Allah ya ganar da mu ya kuma ɗora mu a kan tafarki madaidaici.

labarin da ya wuceRAYUWA
Labarin na GabaGUZURIN RAMADANA DAGA RAYUWAR SAHABBAI DA MAGABATA NA GARI.