1. An haifi Mazon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) a garin Makkah ranar litinin, sha biyu ga watan rabiyul-auwal (12) Shekarar Giwaye.
2. An ambaci shekarar haihuwarsa Giwaye, Saboda sarkin Habasha, ya aika sojoji a shekarar haihuwarsa zuwa garin Makkah, domin su rushe Ka’aba, ya kasance a cikinsa akwai Giwa mai mai girma, sai Allah (Subhanahu wata’ala) ya hallaka rundunar (sojojin), domin (saboda) girmama shekarar haihuwar annabi (Sallallahu alaihi wasallam).
3. Suwaibatul-Assalamiyya ta shayar da shi, bayan mahaifiyarsa, wacce take yi ma babansa hidima Abu-Lahabi, sannan sai Halimatu-Sa’adiyya, har sai da ya kai shekaru huɗu (4) na daga rayuwarsa.
Sharhi;
An haifi manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ne a ranar litinin sha biyu (12) ga watan rabbiyul-Auwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ranar sha bakwai ne (17) ga watan rabbiyul-Auwal, a garin Makka, a shekarar da ake kira da shekarar Giwaye . Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara shi ne wani gwamnan sarkin Habasha mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa, bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa ɗakin Ka’aba da sauya alƙiblar mutane zuwa San’a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka’aba).
Inda dama tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna tasa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye ɗauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinƙa jefo waɗannan tsakuwoyi a kan waɗannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah ya yi maganin wannan azzalumi da mutanensa.
Mahaifinsa dai shi ne Abdullah ɗan Abdul-Muɗallib ɗan Hashim; Mahaifiyarsa kuwa ita ce Amina ‘yar Wahbu, Kakansa kuwa shi ne Abdul-muɗallibi, wanda ya kasance yana da ‘ya’yaye da yawa, amma Abdullahi (mahaifin Annabi) da Abu-ɗalib (mahaifin Imam Ali) mahaifiyarsu guda ne. Don haka ya fito ne daga cikin tsatson Banu-Hashim, su kuma daga ƙabilar ƙuraishawa, waɗanda ke da dangantaka da annabi Isma’il (A.S) ɗan annabi Ibrahim (A.S).
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) dai ya tashi ne a matsayin maraya, saboda kasancewar mahaifinsa ya rasu yayin da ya kai ziyara Yathrib (Madina) watanni uku kafin haihuwar manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam). Tattare da baƙin cikin rasuwar Abdullah, amma haihuwarsa ta sanya iyalansa, Amina da Abdul-Muɗallib, cikin farin ciki da ba shi da iyaka.
Sun shirya gagarumar walima ga ‘yan uwa da maƙwabta, inda aka yi yanka don murnar wannan haihuwa. A sakamakon haka duk Makka ta ɗauki murna, inda mutane suka yi ta zuwa gidan Abdul-Muɗallib don miƙa saƙon taya murna gare shi.
A bisa al’adar mutanen makka, sukan kai ‘ya’yayensu shayarwa ƙauye, saboda samun kyawawan halaye da kuma yanayi mai kyau da dai sauransu, don haka an aika da Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) wajen da Halima ‘yar Abi-zu’aib a ƙauye, don shayar da shi. Haƙiƙa Halima ta sadu da alhairai masu yawa daga abin shayarwarta Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam).
Har ila yau, al’adace ta Labarawa idan sun haihu, sai su nemi mace wacce za ta shayar masu da ‘ya’yansu a cikin ƙauyukan garin, saboda ‘ya’yansu su taso da hikima da dabaru iri-iri na harkar rayuwa, sannan kuma da Juriya na wahal-halun duniya daban-daban, saboda mutane da suka saba da jin daɗin rayuwar birni, za ka iya samun su da lalaci haɗi da rashin hikima na yau da kullum.
Domin karanta sunayen baffanni ƙwarori da gwaggonnin Annabi SAW danna nan
Amma mutumin da ya saba da shan wahala da jin daɗi na rayuwa, to za ka same shi da hikimomi haɗi da kaifin basira da jajircewa akan ayyuka na yau da kullum, sannan ba ya raina sana’a ko ɗan yaya take. Saboda haka, an san ƙabilar Banu-Sa’ad sukan fito neman yaran da za su shayar da su, sai Halimatu ‘yar Abi-zu’aibin ‘yar ƙabilar Banu-Sa’ad ta ɗauke shi za ta shayar da shi (sallallahu alaihi wasallam).
Sannan suka yi wa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) laƙabi da suna ɗan kabshata, a lokacin da yake yi masu wa’azi akan su bar bautar gumaka, su dawo bautar Allah (Subhanahu wata’ala), sai suke cewa ka ji ɗan Kabasha! Yana cewa wai “yana da wanin abin bauta, ana yi masa magana daga Sama!, wato Allah yanayi masa wahayi, ba irin Allolin da muke bautawa ba, sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) Na sama ba a ganinsa” da dai sauransu.
Halima Sadiya ta shayar da Shi tsawon shekaru huɗu (4), wanda yake a lokacin da take shayar da shi akwai abubuwa da yawa waɗanda suka faru, kaɗan daga cikin akwai: magana da zaki a lokacin da annabi da wasu mutane suka fita waje lokacin yana ƙarami sai ga wani karkeci (zaki) babba, sai sauran mutanen suka fita da gudu, sai annabi ya tsaya ya yi magana da zakin har zuwa ƙarshen labarin.
Sannan mala’iku guda biyu (2) sun zo wajen sa da siffar tsuntsu suka tsaga ƙirjinsa shi ma har zuwa ƙarshen labarin. Sannan kuma akwai wani lokaci da annabi ya tashi cikin dare zai yi fitsari, ga shi Halimatu tana bacci a ƙofar ɗakin, sai ya ji tsoro wucewa ta gabanta, saboda kadda ta farka daga bacci, ta hana shi fita waje, saboda wancan abin da ya faru na mala’ikun can, sai annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ɗauki taska ya yi fitsarin a cikinta, sannan ya koma ya kwanta bacci, can sai Halimatu ta tashi daga baccci tana jin ƙishir ruwa, sai ta ga wancan taska, ta ɗauka ruwa ne sai ta shanye ba ki ɗaya.
Bayan gari yawaye, sai annabi yana neman wancan taskar zai zubar da abin da yake cikinta, sai ya duba inda ya ajiye ta, amma bai ganta ba, sai ya tambayi Halimatu, tace ai na ɗauka ruwa ne har ma na shanye, sai annabi yace da ita tun da kin sha wannan, to zai yi miki maganin cututtuka da yawa sosai a jikin ki.
Sannan ya yi wa tsuntsaye addu’o’i a lokacin da Halimatu za ta dawo da shi gida, da dai sauransu. Lokacin da annabi ya cika shekaru shida da haihuwa sai Halima ta dawo da shi zuwa Makka, yayin da ya sami kakansa Abdul-muɗallibi a matsayin mafi alherin mai raino gare shi; domin ya kasance yana ba shi duk abin da yake buƙata na tausayi da ƙauna irin ta iyaye masu lura. Ya kasance yana ba shi matsanancin kulawa fiye da duk iyalansa.
A shekara ta shida da haihuwarsa, sai mahaifiyarsa ta tafi da shi ziyarar danginsa na nono, wato Banu-Uɗayyu bin Najjar a Yasrib (Madina), a tare da su akwai Ummu Aiman. Sai suka saura a can har na tsawon wata ɗaya, sannan sai suka juyo suka kama hanyar dawowa Makka. A hanya ne ajali ya samu mahaifyarsa Amina, aka binne ta a Abwa’i, wanda wani gari ne da ke tsakanin Makka da Yathrib (Madina).
Sai Ummu Aiman ta dawo da shi wajen kakansa, yayin da ita kuma ta ɗauki nauyin aikin uwa, kamar yadda kakansa Abdul-muɗallibi ya ɗauki aikin uba. Wannan kulawa dai ba ta jima sosai ba don shi ma wannan kakan nasa Allah Ya ɗauki ransa a lokacin Annabi na ɗan shekara takwas da haihuwa. Daga nan sai kulawarsa ta koma hannun Baffansa Abu-ɗalib, wanda ya yi mu’amala da shi da ƙauna, sassauci da lura irin ta iyaye, ta yadda babu wani daga ‘ya’yansa da ya samu irin hakan.
Ya kasance yana bacci a shimfiɗar Baffansa, yana zama gefen sa, yana cin abinci tare da shi, yana fita tare da shi duk lokacin da ya fita daga gidansa; da wasun waɗannan na daga nau’o’in lura da so waɗanda irin su ke da wuyan samu.
Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana girma a hannun Baffansa da halayensa na girma tare da shi, ta yadda har sai da ya keɓantu da wasu siffofi na nagarta a tsakaninsa da mutanensa da suka haɗa da gaskiya, riƙon amana, waɗannan siffofi dai sun keɓanta da shi ne ban da waninsa; har ma ta kai ma mutanen suna kiransa da “mai gaskiya da riƙon amana”.
Ganin cewa dai ya fara girma kuma don kada ya zauna haka, sai annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya fara aiki a lokacin yana matashi. Aikin da ya fara yi shi ne kiwon tumaki/awaki (dabbobi). Sannan sai ya bi Baffansa Abu-ɗalib zuwa Sham don kasuwanci. A wannan lokaci ma dai manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya nuna fasaha, ƙwazo, gaskiya da kuma riƙon amana a wannan fage.
Lamarin da ya jawo hankalin wata hamshaƙiyar attijira mai suna Khadijah ‘yar Khuwailid zuwa gare shi. Don haka sai ta neme shi da ya kula mata da wani sashi na kasuwancinta, ta ba shi wasu dukiya mai yawan gaske don gudanar da kasuwanci, wanda daga ƙarshe ta samu riba mai girman gaske da ba ta taba samu ba a baya.
A shekarar da aka haifi Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam), an ga abububuwa iri-iri waɗanda suka faru. Kaɗan daga cikinsu su ne: Mutuwar wutar Kisra, wacce mutanen gari suke bautawa wadda ta ɗauki shekara da yawa ba ta mutuwa, sannan sama ta yi haske, gari ya yi tsit ba hayaniya, da dai sauransu.
Haka kuma dalilin da yasa aka ambaci shekarar haihuwarsa da shekarr giwaye shi ne, a wannnan shekara ne sarkin Habasha ya tura giwaye da yawa sosai, domin su zo rushe ɗakin Ka’abah, wanda yake a wannan lokacin akwai gumaka guda ɗari uku da sittin (360) wanda ake bautawa, bayan gumaka na Ugunwanni da na kasuwanni haɗi da na gidaje.
Danna nan don karanta sunayen annabi SAW
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu