Haƙƙoƙin Ƙananan Yara A Musulunci

0
857

Sarakan karaɗi da surutun duniya suna ta murgina kai, suna jin cewa wai su ne suka tabbatar da haƙƙoƙin kananan yara. Ba su sani ba ko sun sani ko sun mance cewa tuni addinin Musulunci ya yi gaba wajen kafa dokoki da tabbatar da aiki da su don kare haƙƙoƙin ƙananan yara.

A nan a taƙaice za a kawo su kafin a samu wata damar ta yin bayani filla-filla insha Allah:
1. Ƙananan yara suna da haƙƙin a zaɓa musu uwa da uba na gari
2. Kula da ladabin mu’amala da iyali, domin a samu ‘ya’ya masu albarka.
3. Wajibi ne a kula sosai da mai ciki, ita ma ta kula da kanta.
4. Ba a yi wa mai ciki haddi saboda abinda take ɗauke da shi.
5. Wajibi ne a ciyar da mai ciki a kula da lafiyarta koda kuwa an sake ta ne, haka kuma a lokacin da take shayarwa.
6. An halattawa mai ciki da mai shayarwa su sha azumi idan suna tsoron ɗansu zai shiga wani yanayi.
7. Zubar da ciki haramun ne.
8. An haramta yin ta’addanci ga jaririn da yake ciki. Wato haramun ne a daki mai ciki ko a firgita ta yadda ɗan cikin zai samu wata lalura ko ma ya mutu.
9. Ba a raba gado in dai akwai ciki, saboda shi ma yana da gado. Sai a bari sai an haihu an ga abinda aka samu Sannan a raba a fitar masa da rabonsa, a ajiye masa har sai ya girma.
10. Ana yi wa ɓari da halittarsa ta cika komai da ake yi wa gawar babban mutum wato a yi masa wanka a sa masa likkafani a yi masa salla a binne shi.
11. An hana dakatar da haihuwa ba tare da wata lalura ba.
12. Yara suna da haƙƙin a sa musu sunaye na gari, kyawawa.
13. Suna da haƙƙin a yi musu yanka ranar suna(haƙika).
14. Suna da haƙƙin a yi musu aski.
15. Suna da haƙƙin a yi musu kaciya(shayi).
16. Suna da haƙƙin a kula da lafiyarsu, tun suna ciki har su girma.
17. Suna da haƙƙin a kula da cikakkiyar tarbiyyarsu tun suna ciki har zuwa girmansu da balagarsu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Hukunce-hukuncen Ƙananan Yara danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHaƙƙin Da Suke Kan Mahaifiya.
Labarin na GabaHukunce-hukuncen Ƙananan Yara