Gudunmawar Mawadata Da Ɗaiɗaikun Jama’a Ga Tsangayu

0
44

Sanin kowa ne cewa ba kasafai gwamnatoci ko al’umma kan samu isassun kuɗaɗen da za su iya gamsar da buƙatun jama’ar da ke ƙarƙashinsu ba. Wannan wani al’amari ne da za a iya cewa ruwan-dare-gama-duniya.

Koda ƙasashen Turai da suka shahara wajen cigaba, ba duka ne ke da irin wannan wadata ba. Kodayake mu mutanen Najeriya mun ginu bisa tunanin komai sai hukuma ta yi mana. Ta kai ta kawo abubuwan da za mu iya haɗa hannu da juna mu yi wa kanmu maganinsu; ba ma yi sai dai mu zauna har matsalar ta illata mu.

Bisa wannan ne na ke son bayyana wa mai karatu wani abin ban sha’awa game da; yadda al’umar ƙasashen Sudan da na Gambiya suke sharewa tsangayunsu hawaye. Ta yadda babu wata tsangaya a ƙasar Sudan da ke zaune cikin gini ruguzajje ko ka ga wani almajiri na bara a faɗin ƙasar. Wani abin mamaki game da ƙasar Gambiya kuwa shi ne; jama’arsu da ƙasarsu ba su kama ƙafar Najeriya da ‘Yan Najeriya wadata da arziki ba.

Amma duk da haka suna samar wa da tsangayunsu buƙatunsu na yau da kullum. Mawadaci ɗaya a irin waɗannan ƙasashe kan gina ilahirin tsangaya daga aljihunsa; gini irin wanda za ka ce wata hamshaƙiyar ma’aikata ce ta gwamnati. Ashe da abin a zuci yake. Tsangayar Wadil Fadni da tsangayar Umadawwanban ko tsangayar Shiekh Ɗaha da ke Umdurman sun isa misali.

Domin suna da gidan gona kamar wani katafaren kamfani ga shanu ga amfani tsibi-tsibi, ga Alaramma kamar wani Sarki.

Binkice ya nuna cewa kaso arba’in cikin ɗari na tallafin da tsangayunsu ke samu na zuwa ne daga jama’ar gari; kaso talatin zuwa arba’in kuma na zuwa daga gwamnati.

Don haka ya zama wajibi gare mu da mawadatanmu da ma’aikatanmu da ‘yan kasuwarmu da mazanmu da matanmu, yaranmu da manyanmu mu kwaikwayi mutanen ƙasashen Sudan da Gambiya wajen jiɓintar al’amarin tsangayu da almajirai ta hanyar:-
– Ciyar da su
– Gina musu wuraren kwana
– Girmama su da karrama su.

Domin karanta cikakken bayani akan Koyo Da Koyar Da Alƙur’ani Zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Da Sahabbai danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ɗabi’un Annabi (S.A.W) Suke danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceWa Ya Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu)?
Labarin na GabaSunnonin Ranar Juma’a