Aminu Bashir
Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai alfarma:21 Safar 1447
15 August 2025
Mai huɗuba: Sheikh Dr. Bandar bin Abdul-Aziz Badila
Mai fassara: Dr. Usman Muhammad Ahmad
Shugaban sashi: Dr. Abdulkarim Tahir Abdullahi
Huɗuba ta farko:
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ya halicci halittu kuma Ya ƙaddara ƙaddarori, Ya rarraba arziki kuma Ya rubuta ajali, muna yaba masa tsarki ya tabbata a gare Shi kuma muna gode masa, Ya fari halittar rayuwa kuma Ya gudanar da ƙoramu, Ya shimfiɗa ƙasa kuma Ya tsaga tekuna.
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ya hore rana da wata, da dare da yini. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa, kuma zaɓaɓɓen Annabinsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da alayensa tsarkaka, da sahabbansa nagartattu, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa a dukkan darare da yini.
Bayan haka:
Ya ku mutane! Ina muku wasici da ni kaina da tsoron Allah, ku ji tsoron Allah, Allah Ya muku rahama, kuma ku sani cewa babu abin da ke faruwa a cikin wannan rayuwa face sai da ƙaddarar Allah da kuma nufinsa, da hikimarsa da iradarsa; na dare da yini, da iska da ruwan sama, da sanyi mai tsanani da zafi, da sauye-sauyen yanayi da maimaituwarsa, abin da zai sa mumini ya tabbatar da cewa wannan duniya ba gidan dawwama ba ce.
Kuma wannan gaba ɗayansa yana daga cikin ayoyin Allah na halitta masu nuna girman ƙarfinsa da ikonsa, da yalwar iliminsa da hikimarsa, da zurfin nufinsa da rahamarsa, da kuma cewa kowane abu a wurinsa tsarki ya tabbata a gare Shi yana da iyaka.
((Lallai a cikin halittar sammai da ƙasa da sassaɓawar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma’abota hankula Su ne waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingiɗe, suna kuma tunani a kan halittar sammai da ƙasa (suna cewa: “Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata gare Ka, Ka tsare mu daga azabar wuta)).
Ya ku bayin Allah!
Waye a cikinmu da zafin rani bai taɓa cutar da shi ba? Kuma waye a cikinmu da ƙunar rana ba ta taɓa ƙona fuskarsa ba? Dukanmu mun samu rabonmu daga wannan, ko dai kaɗan ko ko dayawa, lallai wannan shi ne zafin rani, mai wa’azin nan da Allah Yake tunatar da bayinsa zafin taron alƙiyama da azabar wuta da shi.
An rawaito daga Miƙdad ɗan Aswad Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (Za a kusanto da rana ga halittu a ranar alƙiyama har ta kasance kamar tazarar mil daga gare su). Sulaim ɗan ‘Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san me yake nufi da mil ba, yana nufin na tazarar ƙasa, ko ko mil da ake amfani da shi wajen sanya kwalli a ido? Ya ce: (Sai mutane su kasance cikin zufa gwargwadon ayyukansu; daga cikinsu akwai wanda zufa za ta kai masa idanuwan sawu, akwai kuma wanda za ta kai masa gwiwoyi, akwai wanda za ta kai masa zuwa ga kwuiɓinsa, akwai kuma wanda zufa za ta yi wa bakinsa linzami sosai). Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi nuni zuwa ga bakinsa da hannunsa. Muslim ne ya rawaito shi.
Ya ku musulmi!
Lallai tsananin zafi yana daga cikin ayoyin da Allah yake aiko wa bayinsa don tsoratarwa da tunatarwa, da zama wa’azi da ɗaukan izina, kamar yadda Allah Ya ce: ((Kuma ba Ma aiko da ayoyi sai don tsoratarwa)).
An rawaito aga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Wuta ta kai kokenta ga Ubangijinta, ta ce: Ya Ubangiji, sashina na cin sashi, sai Ya ba ta izinin numfasawa sau biyu; numfasawa a lokacin sanyi, da numfasawa a lokacin zafi, to wannan shi ne mafi tsananin zafin da kuke ji a lokacin rani, da kuma mafi tsananin sanyi da kuke ji a lokacin hunturu). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
To, ya ku muminai! Mai rabo, shi ne wanda ya yi guzuri daga zafin duniya domin kuɓuta daga zafin lahira, da kuma wanda ya yi haƙuri da ibada a lokacin tsananin zafi, domin ya more ni’imar da ba ta ƙarewa a ranar da za a tona ɓoyayyun sirrikan zukata.
((Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku kare kanku da iyalanku daga wuta, wacce makamashinta mutane ne da duwatsu, masu kula da ita mala’iku ne masu kaushin hali, masu tsananin gaske, ba sa saɓa wa Allah abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abin da aka umarce su da aikata shi)).
An rawaito daga Abu Sa’id Alkhudri Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (Duk wanda ya yi azumin yini ɗaya saboda Allah, Allah zai nesanta fuskarsa daga wuta na tsawon shekara saba’in). Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Kuma Abu Darda Allah ya ƙara masa yarda ya kasance yana cewa: “Ku azumci yini mai tsananin zafin rana saboda kuɓuta daga zafin ranar tashin alƙiyama, kuma ku yi raka’a biyu cikin duhun dare saboda ku kuɓuta daga duhun ƙaburbura”. Abu Nu’aim ne ya rawaito shi a Hilya.
Kuma ku sani Allah Ya jiƙan ku cewa dukkan abin da zai samu mumini a cikin zafi na tsanani da wahala, da gajiya da ƙosawa, to, dukkansu za a rubuta su, za a kiyaye su kuma za a ƙididdige su, a wajen Wanda ayyukan ƙwarai ba sa tozarta a wajensa, kuma ba a rasa ayyukan ɗa’a a wajensa, da su za a kankare zunubai, kuma a ninka kyawawa, kuma a ɗaga darajoji.
An rawaito daga Abu Sa’id da Abu Huraira Allah Ya ƙara musu yarda, sun ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Babu wani abu da zai samu musulmi, na ciwo, ko wahala, ko jinya, ko bakin ciki, har ma da damuwa da za ta sauko masa, face sai an kankare masa zunubansa da shi). Muslim ne ya rawaito shi.
Kuma lallai ayyuka ana ninninka ladansu, kuma ana ƙara sakamakonsu, kuma ma’auninsu na nauyaya, da gwargwadon abin da ya tabbata na niyya da ikhlasi da juriya da haƙuri a zukatan ma’abotansu. Ibnul Asir Allah Ya yi masa rahama ya ce: “Kuma neman lada a cikin ayyuka nagartattu da kuma lokacin da ake ƙi, shi ne gaugawa zuwa ga neman lada da kuma samun sa ta hanyar miƙa wuya da haƙuri”. Ƙarshen maganarsa kenan.
Kuma yana daga cikin rahamar Allah ga bayinsa shar’anta musu abin da za su iya yi na ayyuka da ya yi, kuma bai ɗaura musu abin da zai wahalar da su ba, an rawaito daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda, daga Annabi tsirda da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Idan zafi ya tsananta, to ku sanyaya sallarku, saboda tsananin zafi daga hucin Jahannama yake). Bukhari da Muslim ne suka rawaito. Abin da ake nufi da sanyaya salla, shi ne jinkirta ta zuwa ƙarshen lokacinta, lokacin da zafin garji zai yi sauƙi, kafin shigar lokacin sallar da za ta biyo bayanta.
Kuma za a gwama dukkan wata ibada da ke cikin jinsinta da ita, cikin abin da ya halatta a jinkirta shi, don haka, duk wanda ake bin shi azumi na watan Ramadan, ko kuma kaffara ta azumi ko makamancin haka, to, ya halatta a gare shi ya jinkirta shi zuwa ga lokutan sanyi, idan biyansa a lokacin zafi zai ba shi wahala, akwai hadisin A’isha Allah Ya ƙara mata yarda da yake nuni a kan haka, ta ce: “a kan samu wani lokaci da ake bi na azumi da na sha tun a watan Ramadan, amma na kasa samun daman biya sai a watan Sha’aban”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito. Amma gaggauta biya shi ya fi,
Don haka, ya ku bayin Allah!
Ku gode wa Allah a bisa dukkan hali da yanayi, kuma ku gade masa a kan abin da Ya tanada muku na hanyoyi da sabuba, waɗanda Ya sauƙaƙe muku wahalar zafi da tsananinsa da su, da ƙunarsa da hucinsa, da na’urorin sanyayawa da wuraren hutu a lokacin zafin rani, kuma ku riƙa bincikan halin ‘yan uwanku talakawa da marasa abin hannu, kuma ku sauƙaƙa musu abin da suke fama da shi na tsananin zafi da ƙunar rana, kowa ya yi dai dai ƙarfinsa da ikonsa, kuma daga cikin haka akwai shayar da ruwa mai sanyi a waɗannan lokuta na zafi, saboda hakan yana daga cikin sadokoki mafiya falala, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba mu labarin hakan.
Kuma ku riƙa tunawa da wasu ‘yan’uwanku a Addini, waɗanda raɗaɗin rashi da tawaya ta dukiya da rayuka da ‘ya’yan itacuwa suka ƙaru a gare su a kan abin da suke fama da shi na tsananin zafi, ya Allah Ka yaye musu abin da ya sauko musu, ya Allah Ka sauya tsoronsu da aminci, biƙin cikinsu da farin ciki, yunwarsu da ƙoshi, kuma Ka taimake su a kan maƙiyanka kuma maƙiyansu ya Mai ƙarfi ya Mabuwayi.
Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina nema wa kaina gafarar Allah, da ku da sauran musulmi, daga kowane zunubi, don haka ku nemi gafararsa, lallai Shi Mai yawan gafara ne kuma Mai jinƙai.
Huɗuba ta biyu:
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Wanda dukkan al’amura suke samuwa daga aikinsa da nufinsa, muna yaba masa tsarki ya tabbata a gare Shi kuma muna gode masa a bisa falalarsa mai yalwa da ni’imominsa, da kyakkyawar afuwarsa da gafararsa, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga mafificin Manzanninsa kuma zaɓɓaɓensa, da alayensa, da sahabbansa da tabi’ai, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar rarrabewa da tashin alƙiyama.
Bayan haka: Ku sani, Allah Ya muku rahama, cewa lallai bayyana fushi da raki don tsananin zafi yana daga cikin suka ga hukuncin Allah da ƙaddararsa, da nufinsa da ganin damansa, da kuma cewa lallai babu abin da zai auku a wannan duniya face sai da wata hikima da maslaha da fa’ida da amfani, daga cikin haka akwai yadda muke ganin dayawa daga cikin shukoki da ‘ya’yan itatuwa ba sa yin daɗi kuma ba sa daidaituwa har sai lokacin da rani ya kai maƙurarsa, haka kuma dayawa daga cikin cututtuka da annoba ba sa ɓacewa har sai lokacin da zafi ya kai ƙololuwar matakinsa, Ibnul Ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce:
“A lokacin rani, iska na rikiɗewa ta yi zafi sosai, sai ‘ya’yan itatuwa su nuna, kuma sauran ababe marasa amfani da ababen da suka cakuɗu da jiki su gushe a lokacin hunturu, kuma sai sanyi ya kutsa ya shiga cikkuna, don haka ne ma maramaren ruwa da rijiyoyi suke yin sanyi”. Ƙarshen maganarsa kenan.
Saboda haka, ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah, kuma ku kiyaye zukatanku da harsunanku daga dukkan abin da zai rage imaninku, ya lalata tauhidinku, domin yana daga cikin cikar tauhidi yarda da kuma miƙa wuya ga dokokin Allah na shari’a da tsarinsa na gudanar da duniya.
Sannan ku yi salati da sallama ga mafi alherin halittun Allah, Muhammadu bin Abdullahi, domin Ubangijinku Ya umarce ku da hakan, sai Ya ce: ((Lallai Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi; ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).
Ya Allah, Ka yi salati da sallama, da ƙarin daraja da albarka ga bawanka kuma ManzonKa, Annabinmu Muhammadu, kuma ka ƙara yarda da sahabbai baki ɗaya, da tabi’ai, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya Allah, ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai, Ka kiyaye shingen addini, Ka taimaki bayinka muminai masu tauhidi.
Ya Allah, ka yaye damuwar masu damuwa daga cikin musulmai, ka kwaranye baƙin cikin masu baƙin ciki, Ka biya bashin wadanda ake bi bashi, Ka warkar da marasa lafiya daga cikinmu da na sauran musulmai.
Ya Allah Ka amintar da mu a ƙasashenmu, Ka shiryar da shugabanninmu kuma jagororinmu, Ka ƙarfafi Shugabanmu kuma jagoranmu Hadimin Masallatai Biyu Masu alfarma da gaskiya da dace da gamonkatar, Ya Allah, ka tsawaita rayuwarsa cikin waraka da ƙoshin lafiya, da ni’ima mai yalwa kuma cikakkiya, kuma Ka datar da shi da magajinsa amintacce ga abin da alheri ne ga ƙasa da mutane, da ɗaukaka ga Musulunci da musulmi ya Ubangijin talikai.
Ya Allah Ka kasance Mai ƙarfafawa da kawo ɗauki da agazawa da taimako ga ’yan’uwanmu masu rauni, ya Allah, Ka taimake su a ƙasar Falasɗinu a kan yahudawa ‘yan ƙwace, ya Allah, Ka ƙididdige adadin yahudawa, Ka halaka su ɗaya bayan ɗaya, kuma kada Ka bar ko ɗaya daga cikinsu.
Ya Allah Ka kiyaye dakarunmu masu dako a kan iyakoki da fagage, Ya Allah, Ka kiyaye su da idonka da ba ya barci, Ka tsare su da ƙarfinka da ba a iya rinjayarsa ya Ubangijin talikai.
Ya Allah Ka azurta mu da haƙuri akan jarrabawa, da yarda da ƙaddara, da godiya a lokacin yalwa, kada Ka ɗora mana abin da ya fi ƙarfinmu, domin aminci daga gare Ka shi ya fi yalwa a gare mu ya Mafi tausayin masu tausayi.
Ya Allah Ka tsare mu daga azabarka a ranar da Za Ka tashi bayinka, ya Allah Ka tsare mu daga azabarka a ranar da Za Ka tashi bayinka.
((Ubangijinmu, Ka ba mu alheri a duniya, da alheri a lahira, kuma Ka tsare mu daga azabar wuta))
((Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buya daga abin da suke sifantaShi da shi () Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni () Kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai)).
Karanta Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya 1st August 2025
Edita@rumasau-kallamu