Duhun Matse-Matsi [DARKNESS OF INNER THIGH]

0
10

Duhun matse-matsi ko tsakankanin cinyoyi kai wani lokacin har ma da mazaunai wannan kusan abu ne da mutane da yawa cikin mata da maza kan fuskance shi. wasu kan ji kunya ma su kasa tattauna matsalar, musamman masu fama da matsalar haɗe da stretch marks a ɗuwawu kaca kaca.

Toh sai dai stretch marks galibi yau da kullum ce kama daga yawan zama, kwanciya, da sanya matsi a game da fata wato kamar juna biyu duk yakan haddasa shi. Sai dai dangane da duhun wanda shi ne zan bayani kansa akwai mabambantan dalilan da ke jawo shi kama daga:

  • Ƙiba
  •  Tangaɗar sinadaran halitta (imbalance)
  • Wani magani da mutum ke sha
  • Ciwon sugar
  • Ciwon fata
  • Fitar sinadarin da ke sanya duhun fata fiye da kima
  • Ƙarancin lura da tsaftar al’aura

Dukkansu na iya haifar da wannan yanayin a fata. Toh sai dai akwai wani abu da ya ɗan bambanta; Ga masu fama da duhu sosai wanda za ka gani a wuya, haɓar wuya, hammata, da cinya duk lokaci 1 galibi wannan ACANTHOSIS Nigricans muke kiransa da wuya ka samu ba su da larurar ciwon sugar ta Diabetes.

Wannan yasa masu acanthosis ko sun sai mai sun shafe-shafe sun gyara gurin, a hankali zai ƙara komawa baƙiƙƙirin domin maganin kurum shi ne; su yi control ɗin sugar ɗin, toh sai dai galibi ba su san suna da ciwon sugar ba, tunda ba ta ba su wani canji a jika matakin farko. Sai ka shekara 5 da ciwon sugar ba ka sani ba, sai a ƙarshe ta soma lalata ma ƙoda jikinka ya rikice lokaci guda.

Wannan tasa koyaushe ake son check up domin a asibiti ne kaɗai za a iya gano haka su masu sai da maya-mayen gyaran jiki kasuwancinsu kurum suke ba su san menene ba, kai ne za ka ga kana da tsafta amma gashi sai fama kake.

Toh sai dai ga masu irin wancan duhun na matse-matsi da in sun je wanka wani lokacin in suna dirza fatar suke ganin kamar datti a duƙunƙule na fita. Galibi hakan na faruwa ne a mutanen da jikinsu ke sakin sinadarin (melanin) da yawa wanda sinadari ne da ke sanya duhun fata domin ba ta kala ɗinta, da kuma kare ta daga zafin rana da sauransu.

Sai dai a wasu sinadarin kan fi yawa wajen matse matsi da hammata saboda ba gurare ne da iska ke ratsasu ba ko yaushe. Wannan wasu tasa su yi ta mamaki su ga koyaushe suna wanka amma ga datti su yi ta zargin tsaftarsu.

Duk da hakan in ya haɗu da ƙarancin tsafta to duhun kan yi muni ya ɗau lokaci ana fama. Don haka mu a LIKITANCE ba ma kallonsa a matsayin larura shi yasa ma babu maganin sa a likitance sama da mu ƙarfafe ka ƙara kula da tsafta. Ba ƙazanta ba ce dead skin ce da melanin.

Mukan ba mutum shawara ya ruɓanya lura da tsafta musamman a maza wata hanya shi ne; Sanda kuka yi gudu ko irin wasan ƙwallo ku ka yi zufa! Da za ku je tsuguno ko ya kuka dirza cinyarku za ku ga dattin haɗe da matacciyar fatar ya taso ko da hannu da farce za ku ga kuna ta kankaro shi saboda ya jiƙa da zufa.

Hakan yasa nakan ba masu shi shawara duk wanda ya yi irin motsa jikin kuma yasan yana da abun to kar ya jinkirta wanke cinyoyinsa. Ba a son wanka sanda ake zufa domin da shi da babu duk ɗaya ne a lokacin to amma koda za a jinkirta wanka,  ka daure ka shiga banɗaki lokacin da ka taso ka wanke cinyoyin ko da hannunka mutum zai ga yana durzo matacciyar fatar me duhun wacce ta macen domin in ka sha iska ko ka je wanka ba za ta fita haka ba.

Amma wanda suke da swimming pool galibi ba su da wannan matsalar domin suna jiƙa sosai su shafe dogayen mintuna a ruwa shi yasa duk dead skin ɗinsu sai ta taso sama sun wanke suke fita.

Toh kuma da ba ku da swimming pool za ku iya zuba ruwan a babban bowl in kun je wanka ku shiga ku zauna kurum ku shafe mintoci zaune sai kun jiƙa sosai sannan ku fara wankewar koda kuna amfani da man gyara jikin za ku fi ganin tasirinsa. Kamar yadda nace a likitance ba wani magani da zan iya cemuku ga shi Guarantee saboda larurar amma galibi wasu:

  • Kan yi amfani da man shafawa na ALOE VERA koma ruwan aloe vera ɗin kai tsaye shi ma mutanen da suka gwada sun ce yana fitarwa. Idan aka shasshafe cinyoyin da mazaunen sai a cigaba da harkoki kar a wanke sai bayan awa 1 ko fiye, kullum mutum ya riƙa hakan kafin wanka sau biyu a yini sun ce yana taimakawa.
  • Ko amfani da Aloe vera da lemon tsami haɗe a riƙa shafawa
  • Ko amfani da Baking powder da man Olive. Toh amma dai kamar yadda nace wannan duk ba binkice a likitance ba ne yace.

Sai dai a likitancen Creams irin su; Ellagic acid cream, Hydroquinone, Lignin peroxidase, Isotretinion ko Niacinamide cream mun san suna da Lighting property. Toh amma dai kafin ka yi komai ya dace in abun na damunka ka nemi shawarar likita, saboda fatar kowa ta bambanta wajen ɗaukar saƙo, abin da ya yi ma wani bai zama dole ya yi aiki a wani ba.

TO AMMA BAKI ƊAYA NAKAN CE

1. Mutum ya riƙa amfani da ruwan ɗumi yana zama a ciki mintuna 15 zuwa 30 kullum kafin ya soma wanka koda ya shafa waɗancan abubuwan hakan zai sa ya jiƙu, kai koda aski za ku yi ku tsaftace kanku in kuna zama cikin ruwan ɗumi minti 10 zuwa 15 kafin gabanku ba zai dinga ƙuraje ba abunda muke kira FOLLICULITIS.

2. Sannan mutum ya ƙara adadin yawan wankansa! Galibi maza sau 1 suke wanka a yini, ka sani kana buƙatar fiye da haka, in da za ka iya har da rana sanda ka yi zufa ka riƙa yi da kuma kafin kwanciya bacci.

3. Sannan a riƙa canza gajeren wandon ciki kullum, tare da Aski a kai a kai shi ne ma mahimmi a ƙalla duk sati 2 ko 3 mutum ya tsaya ya tsaftace kansa. Kada ka ga matarka ba ta ƙorafi amma dai akwai tozarta kai gaskiya ka zauna haka kaca-kaca. Rashin lura da tsaftar matse matsi da hammata na hana jin daɗin Jima’i kansa.

4. Ga masu sayar da maya-mayai nan na gyaran duhun fata duk za ku iya samun su ku jaraba ba sai mata kaɗai ba.

5. Duk sanda ka yi zufa ka ji matse-matsinka ya jiƙa har kana iya turzo fatar to tsaya ka sami ruwa musamman na ɗumi ka shiga banɗaki ka tsaftace kanka, in ta kama ko dutsen goge kaushi za ka sa ka dirza in dai yana fita ba kuma ka jin zafi to tsaya ka yi direct za ka ga yana haske debris ɗin na fita.

6. Idan ƙiba gareka saboda cinyoyinka na gogar juna suna iska ratsawa toh kai/ki ƙoƙarin rage ƙibar.

7. In ka ga kayi-kayi duhun bai tafi ba, ko kuma in ya tafi yana dawowa toh ka daure ka je ka ga likitan fata, ta yiwu akwai wata larura a jikinka da ba ta bayyana ba tukun amma zuwan zai sa a gano ta. Allah yasa mudace.

Domin karanta Motsin Jariri danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAlaƙar Hausa Da Fulatanci
Labarin na GabaZubar Jini A Cikin Wata Uku Na Farkon Samun Juna Biyu (FIRST TRIMESTER HAEMORRHAGE)