Damakwaraɗiyya A Tsakanin Dabbobi

0
26

Wannan hoton da kake gani a ƙasa, kuraye ne guda biyu da ɗan tinkiya tsakiya, za a jefa ƙuri’a a kan zaɓar wanda za a yi kalacin dare da shi. Ai kai ma ka san ba sai an fada ba, ɗan tinkiya shi ne amsa. 

Ko da kuwa yana da yawa. Balle an fi shi yawa. To haka damakwaraɗiyya take ko ga ‘yan Adam Talakan nan dai shi ne a ƙasa. 

  1. Tana Sa Karkata ga ayyukan raya Ƙasa: (Public infrastructure) kamar su: Gina hanyoyi, wutar lantarki, ruwan sha, hanyoyin sadarwa, gina makarantu da sauransu. 

Maimakon tun daga farko, a fara da gyara shi ɗan Adam ɗin, wajen kyautata alaƙarsa da Ubangijinsa (tarbiyyar aƙidarsa), kyautata alaƙarsa da jama`a (kyan dabi’arsa da halayensa), Inganta ƙwaƙwalwarsa (ba shi ilimi na tsoron Allah mai nagarta), wanda zai amfane shi duniya da lahira.

Ba wai muna cewa Musulunci ba ruwansa da ayyukan raya ƙasa ba ne kwata-kwata. Abin da muke cewa shi ne, a tsarin gwamnati ta Musulunci, shugaba kowanne iri ne, lallai ya fara kula da shi ɗan Adam ɗin, kafin ayyukan raya ƙasa. 

Ayyukan shugaba na farko su ne: Gyaran aƙidar mutane. (Watau kare addininsu). Kare rayukan jama’a. Kare hankulansu (watau kada su faɗa shaye-shaye). Kare dukiyoyinsu. (watau hana sace-sace, fashi da makami, da sauransu). Da kare nasabarsu. (watau hana yaɗuwar zina da luwaɗi da maɗigo da toshe hanyoyin yaɗuwarsu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)ya ce: 

“Ku saurara ku ji! Kowannenku mai kiwo ne, kuma kowannenku za a tambaye shi abin da aka damƙa masa kiwo: Shugaba, wanda yake shugabantar mutane, mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi abin da aka danƙa masa kiwo. 

Domin karanta bayani akan Ma’anar Damokuraɗiyya Danna nan

Mutum mai kiwo ne na mutanen gidansa, za a tambaye shi game da abin da aka danƙa masa kiwo. Mace mai kiwo ce a gidan mijinta da ‘ya ‘yansa. Za a tambaye ta game da su. Bawa mai kiwo ne game da dukiyar ubangidansa, kuma za a tambaye shi game da ita. Ku saurara kuji! Kowannenku mai kiwo ne, kuma kowanncnku za a tambaye shi abinda aka danƙa masa kiwo (Bukhari da Muslim suka ruwaito). 

Daga Hasan (al Basari) ya ce: “Ubaidullahi bin Ziyad13 ya je duba Ma ‘aƙil bin Yasar al Muzni a rashin lafiyarsa wadda ya rasu a cikinta. Sai Ma’aƙil ya ce masa: “Zan ba ka labari wanda na ji daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). 

Idan da na san akwai ragowar rayuwa a gare ni da ba zan gaya maka ba. Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Babu wani bawa, wanda Allah zai ba shi kiwon talakawa, ya zama sanda zai mutu, ya mutu yana mai yi musu algus (watau bai shiryar da su ga abinda shi ne alheri a gare su ba, ya kuma kawar da su ga barin sharri), face Allah ya haramta masa aljanna'(Bukhari da Muslim suka ruwaito).

  1. Tana Ɗaukar Mutane Kowa Da Kowa Ɗaya. Babu Wanda Ya Fi Wani. (All people are Equal & Same

A musulunci, Allah ya ce masu ɗa’a a gare shi (watau Musulmi), su ne masu daraja a gare shi. Haka kuma waɗanda Suke da ilimin saninsa da biyayya a gare Shi daga cikin Musulmin suna da ƙarin daraja a kan sauran, inda (Subahanahu Wata’ala) yake cewa: 

“Yanzu ma sanya Musulmi da fajirai su zama ɗàya? Me ya same ku? Wane irin hukunci kuke yi?” (Suratul Ƙalam, aya ta: 35-36). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Shin za mu sanya waɗanda suka yi imani suka yi aiki na gari su zama kamar masu ɓarna a bayan ƙasa. Ko za mu sanya masu taƙawa su zama daidai da fajirai? (Suratu Saad, aya ta: 28). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Gaya musu, shin masu ilimi sa yi daidai da marasa ilimi? Masu hankali ne kaɗai, suke gargaɗuwa” (Suratuz Zumur, aya ta: 9). 

Domin karanta tarihin damokuraɗiyya a Najeriya danna nan

Wannan yana nuna cewa, a tsarin Musulunci mutane ba ɗaya suke ba, a wajen Allah, da ma zamantakewarsu ta duniya a tsakaninsu. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Kuma shi ne ya sanya ku masu maye wa juna a bayan ƙasa, kuma ya ɗaukaka wasunku a kan wasu, darajoji. Domin ya jarrabe ku cikin abin da ya ba Ku” (Suratul An ‘ami, aya ta:165). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Muna ɗaga wanda muka ga dama, darajoji. Kuma a sama da kowane masani akwai wani masanin (Suratu Yusufa, aya ta: 76). 

Kuma Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce:

Shin su ne suke raba arzikin Ubangijinka. Mu ne muka raba arzikinsu tsakaninsu a rayuwar duniya. Kuma muka ɗaukaka wasunsu a kan wasu, darajoji, domin wasunsu su riƙi wasu ababan horewa” (Suratuz Zukhrufi, aya ta 32). 

  1. Yin Amfani Da Tasirin Kafofin Yaɗa Labarai: (Influence of the Media) 

A tsarin damakwaraɗiyya kafofin yaɗa labarai suna da tasiri matuƙa, wajen ɓata abu ko gyara shi. Idan ɗan takara yana da kuɗi, yana iya biyan kuɗaɗe masu yawa, kafafen yaɗa labarai su yi ta koɗa shi, suna ƙawata shi ga jama’a. Ta wan nan hanyar sai ya kayar da wanda ba shi da kuɗi, komai nagartarsa. 

  1. Biyan Wasu Kuɗaɗe Kafin Zama Ɗan Takara: (Money required for Candidature) 

A tsarin damakwaraɗiyya kowane ɗan takara sai ya biya wasu kuɗi na tsayawa takara, (A Najeriya sun sa masa suna: Na gani ina so). 

Gwargwadon girman muƙamin da ɗan takara zai tsaya, gwagwadon yawan kuɗin da zai bayar. Na shugaban ƙasa ya fi na gwamna yawa, Na gwamna ya fi na shugaban ƙaramar hukuma. Na ƙasan su, shi ne na kansila. 

Tun daga nan, Zamu gane Cewa, shugabanci a tsarin damakwaraɗiyya sai mai kuɗi. Ko kuma wanda masu kuɗi suka tsaya masa. Wan nan ya nuna cewa damakwaraɗiyya tsari ne na Yahudu. Domin wannan shi ne abin da Banu Isra ila suka faɗa a sanda Allah ya naɗa musu Ɗaaluta ya zama sarki a tsakaninsu: 

“Suka ce, ta yaya zai kasance yana mulki a kan mu, alhali mu muka fishi cancanta da mulki, kuma ba a ba shi yawan dukiya ba?” (Suratul Baƙarah, aya ta: 247) 

Wannan fa ba a nan ta tsaya ba, dole ɗan takara ya tanadi kuɗaɗen da zai ba wa masu jefa ƙuri’a da masu yi masa farfaganda. Ka ga ke nan tun daga alwala sallar ta riga ta ɓaci.

  1. Ɓarnar Kuɗin Jama’a (Wasteful spending). 

Daga cikin illolin wannan tsarin akwai ɓarnar dukiyar ƙasa. Duk sanda shekara huɗu ta cika za a rushe wannan gwamnatin, a kafa wata, komai adalcinta. Haka kuma a duk inda aka sami matsala za a sake yin zaɓe a cikin waɗannan shekarun. Haka za a yi ta kashe kuɗaɗen jama’a, maimakon ma a ce an yi musu ayyukan raya kasa (kamar yadda suke cewa). 

Mu sani cewa a tsarin Musulunci, mutum shi a kan kansa, haramun ne ya ɓarnatar da dukiyarsa balle dukiyar jama’ a. Wan nan shi ake kira ‘almubazzaranci (ɓarnar dukiya). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Kuma ka bai wa makusanci haƙƙinsa da miskini da ɗan hanya. Kada ka yi almubazzaranci. Haƙiƙa masu yin almubazzaranci sun kasance yan uwan Sheɗan. Shi kuwa Sheɗan ya Kasance mai kafirce wa ubangijinsa ne (Suratul Is ‘ra’i, aya ta: 26-27). 

To ina kuma ma a ce dukiyar ta jama’a ce, ba wadda mutum ya nema ya samu ta kyakkyawar hanya ba? 

  1. Kashi Saba’in Cikin Ɗari Na Yan Najeriya Ba Sa Yin Zaɓe: 

Wani abin da yake nuna cewa talakawan Najeriya sun gaji da damakwaraɗiyya (saboda illolinta) shi ne, tun daga zaɓen shekarar 2003, yawan masu jefa ƙuri’a raguwa yake yi. 

Misali: A cikin yawan ‘yan Najeriya kimanin miliyan ɗari biyu (200,000,000) mutum miliyan tamanin da biyar ne suka yi rijista a zaɓen shekarar 2019. A cikin wan nan adadin sai ga shi mutum miliyan goma sha biyar da dubu ɗari biyu (15,200,000) ne suka jefa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa. 

Idan muka duba masu fitowa zaɓe a ƙiyasunsu cikin ɗari a shekarun mulkin damakwaraɗiyya a Najeriya, za mu gan su kamar haka:

A shekarar 2011 kashi hamsin da huɗu (54%) cikin ɗari ne suka fito jefa ƙuri’a. 

A shekarar 2015 kashi arba’ in da huɗu (44%) ne suka fito. 

Sai ga shi a shekarar 2019 kashi talatin da biyar (35%) ne kaɗai suka fito14

Wannan ya nuna ɓaro-ɓaro, irin yadda yan Najeriya suke ƙin damakwaraɗiyya, amma ina! Sai daɗa ƙoƙarin ƙaƙaba musu ita ake yi. 

  1. Zaɓe Yakan Nuna Jam’iyyar Da Ta Fi Yawan Kuri’u, Amma Mafi Yawan Jama’a Ba Sa Son Ta: 

Wannan ma wata illa ce a cikin damakwaraɗiyya, wadda take nuna cewa waɗanda suka shirya wannan tsarin sun wautar da hankulan mutane. 

Yadda lamarin yake shi ne, misali: Idan aka sami jam`iyyu uku a cikin ƙasa, sai jam’iyya A ta sami ƙuri’ a kashi arba’ in cikin ɗari (40%), jam`iyya B ba ta sami kashi talatin cikin ɗari (30%), jam’iyya C ita ma ta sami kashi talatin cikin ɗari (30%), a nan sai kawai a ce jam’iyya A, ita ta cinye zaɓe. Alhali abin da zaɓen ya nuna shi ne, kashi sittin cikin ɗari (60%) na waɗanda ma suka kaɗa ƙuri’a, ba sa ƙaunar ita jam`iyya A ɗin, wadda aka ce ita ce ta ci. 

Ka ga a nan, ita kanta maganar bin ra’ayin mafi rinjaye (watau agalabiyya), an ajiye shi waje ɗaya, saboda tsabar wautar da hankalin jama’a. 

  1. Tana Sa wa A Ci Zaɓe Da Ƙasa Da Kashi Hamsin Cikin Dari Na Kuri’ un Da Aka kaɗa. 

Wannan ma wani raina hankalin ne wanda yake cikin wan nan tsarin. Misali: Idan aka sami jam iyyu huɗu sun tsaya zaɓe, sai jam’iyya A ta sami kashi talatin (30%) cikin ɗari, jam’ iyya B ta sami kashi ashirin (20%) cikin ɗari, jam’iyya C ta sami kashi ashirin (20%) cikin ɗari. Ita ma jam iyya D ta sami kasha ashirin (20%) cikin ɗari, sai jam’iyya A ta ci zaɓe.

Kuma ka ga talatin ta samu cikin ɗari. Kai ko da ma a ce arba’in da biyar ta samu cikin ɗari, ai ba su kai rabi ba. Kuma dai har yau za mu ga bai kamata a ce fiye da rabin masu jefa ƙuri’a sun nuna ƙin su ga wannan jam’iyyar, amma sai a ce ita ce ta ci zaɓe. Ba wai muna cewa wan nan haka yake a ko ‘ina ba, amma dai ana yi. 

  1. Tana Sa wa A Zaɓi Shugaba Domin Ya Bayar Da Cin Hanci

Haramun ne a Musulunci ka zaɓi mutum domin ya ba ka abin duniya, ko domin ya yi alƙawarin zai ba ka. 

Daga abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: 

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mutum uku, Allah ba zai yi Magana da su ba ranar alƙiyama. Ba zai kalle su ba. Kuma ba zai tsarkake su ba. Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a gare su: Mutumin da ya hana ɗan hanya ruwan da, shi ya riga ya gama tasa buƙatar da shi. Da mutumin da ya sayar wa da wani abin sayarwa bayan La’asar, yana mai yi masa rantsuwa da Allah, cewa shi ma kan kaza da kaza take a wajensa, ya gasgata shi, alhali ba hakan ba ne. Da mutumin da ya goyi bayan shugaba, bai goyi bayansa ba sai kawai domin zai bashi abin duniya. Idan ya bashi, sai ya cika masa alƙawarin (daya yi masa). Idan kuwa bai bashi ba, ba zai cika masa wannan alƙawari ba” (Bukhari da Muslim Suka ruwaito). 

  1. Tana Samar Da Shugabanni Maƙaryata: 

Kasancewar shi tsarin damakwaraɗiyya an ɗora shi ne a kan cewa, shugabanni za su yi wa talakawa alƙawuran abin da za su yi musu a lokacin neman zaɓe; wannan yana sanya shugabanni su rinƙa yin alƙawuran ƙarya. 

Mun dai faɗa a baya cewa, a tsarin siyasar Musulunci alƙawarin da Shugaba zai yi wa talakawa shi ne, tafiyar da su a kan tsarin Al-Ƙur’ani da Sunnah.Su kuma sun yarda cewa tsarin Allah zai ba su duk wani jin daɗi, na duniya da lahira. 

Mu sani cewa a Musulunci, ƙarya tana daga cikin kaba’irai, (watau babban zunubi ce). Duk wanda aka san shi da ita bai ma halatta ya zama shugaba ba.

Daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: 

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Mutum uku Allah ba zai yi magana da su ba ranar al ƙiyama. Ba zai tsarkake su ba. Ba zai kalle su ba. Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a gare su: Tsoho mazinaci da shugaba maƙaryaci da matalauci mai girman kai” (Muslim ne ya ruwaito). 

  1. Mace Za Ta Iya Zama Shugaba: 

Malaman Musulunci gaba ɗaya sun haɗu a kan rashin halaccin shugabancin mace. Saboda Hadisin Abu Bakrata, wanda ya rawaito kamar haka: 

“Yayin da labari ya isa ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa, mutanen Farisa sun shugabantar da ‘yar Kisira (watau ‘yar shugabansu), sai ya ce: “Duk mutanen da suka shugabantar da mace a lamarinsu ba za su rabauta ba (Bukhari ne ya ruwaito). 

Mu sani fa cewa addinin Musulunci shi ne ya ƙwato ‘ya mace daga ƙangin wulaƙancin da ta sha a tsakanin al’umomin Girkawa da Farisawa da Larabawa da sauransu, da ƙyamar da addinin Yahudanci da na Kiristanci suka yi mata. 

A addinin Yahudanci an samu suna ƙyamar mace idan tana haila. Akan nisanta ta da mutane. Ko da mazubin da ta ci abinci ba a taɓawa. A tsarin Kiristanci kuwa, a da, ba su yarda mace tana da rai ba, sai bayan wani lokaci aka ƙwato mata wan nan ‘yancin. 

Wajibi ne mata musulmi da ƙungiyoyin mata su karanta Tarihin ‘ya mace a waɗancan al’umomi da waɗannan addinai. Wannan zai sa mu gane cewa Musulunci ba wulaƙanta ‘ya mace ya yi ba, da ya hana ta shugabanci da alƙalanci. 

Abin da ya sa Musulunci ya hana ‘ya mace waɗannan ayyuka shi ne, ayyuka ne na gwamutsi da maza. Sannan kuma yanayin halittarta, kasancewa Allah ya ƙaddara mata yin haila duk wata, da daukar ciki da shayarwa da raino; Waɗan nan ayyukan da Allah ya ɗora mata abin dubawa ne.

Don haka a sake ɗora mata waɗancan manyan ayyuka na Jama’a akwai cutarwa. Sai a yi biyu babu. Sannan kuma ai kasancewar shugabanmu Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ƙyamaci abu, ya kamata mu ƙyamace shi, matuƙar mun yarda shi shugabanmu ne, kuma Manzan Allah ne. 

  1. Tana Sa wa A Naɗa Mutane A Muƙaman Da Ba Su Da Ƙwarewa A Kai. Sai Saboda Biyan Buƙatar Siyasa. 

Musulunci bai yarda a naɗa mutum a wani muƙami na gwamnati ba, sai mai amana da ƙwarewa a wannan fagen. Al-ƙur`ani ne ya koyar da mu haka a Suratu Yusufa da Suratul Ƙasas. 

A Suratu Yusufa al-ƙur’ani yana gaya mana abinda Annabi Yusufa (Alaihissalam) ya ce wa sarkin Masar: 

“Ya ce “Sanya ni a (ɓangaren kula da) taskokin ƙasa. Ni mai kula da amana ne, kuma mai ilimi ne (a wan nan ɓangaren)” (Suratu Yusufa, aya ta: 55) 

A suratul ƙasas kuma ‘yar annabi Shu’aibu ce take shawartar mahaifinta, ya ɗauki Annabi Musa aiki, sabo da siffofin da ta lura da su a tattare da shi. Inda take cewa: 

“Ya babana ka ɗauke shi aiki. Mafificin wanda za ka ɗauka aiki, shi ne ƙaƙƙarfa, mai amana (Suratul Kasas, aya ta: 26.) 

Wan nan ya nuna mana cewa, duk aikin da za a ɗauki mutum, bayan amana, dole Sai ya zama yana da ƙwarewa a wannan fagen, ƙwarewa ta ilimi ko ta ƙarfi. 

Wani abin da ya fi ban tsoro shi ne, Hadisin da aka ruwaito daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) game da naɗa mutum a wani ofishi, domin biyan buƙata ta son rai.

An ruwaito daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: 

“Wanda duk ya shugabanci wani abu na Musulmi, (kamar a ce, ya zama Shugaban ƙasa, ko ya zama gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma ko sarki), sai ya naɗa mutum, alhali ya sami wanda ya fi shi nagarta ga Musulmi, to ya ha ‘inci Allah da Manzonsa. A wata ruwayar, 

“Wanda duk ya rataya ragamar wani aiki ga wani mutum a wata jama ‘a, alhali a cikin wannan jama`ar ya sami wanda ya fi soyuwa a wajen Allah, to haƙiƙa ya ha`inci Allah. Ya ha’inci Manzonsa. Ya ha’inci Muminai” (Hakim ne ya ruwaito). 

Idan muka duba sai mu ga a ita tsarin damakwaraɗiyya galibi jam’iyya ake dubawa ko wani kusanci na son zuciya. Ba a cika duba nagarta ba. 

  1. Tana Janyo Rashin Ɗorewar Ayyuka Da Tsare-Tsare. 

Babu shakka sanin kowa ne cewa, mu dai a Najeriya, komai kyan tsarin da wani Shugaba ko gwamna ya zo da shi, kuma komai amfaninsa, idan bai yi wa magajinsa daidai ba, sai kawai ya dakatar da shi, ko ma ya rushe shi. 

A nan za mu ga cewa, hatta ita kanta damakwaraɗiyyar ana saɓa mata. Domin da kamata ya yi a lura da amfanin aikin ga mutane ko rashin amfaninsa. 

To dai a taƙaice Musulunci bai yarda da ɓarnar dukiya ba, ko da kuwa ta mutum ce, balle dukiyar jama’a. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: 

“Haƙiƙa Allah ba ya son abu uku a gare ku: “Wane ya ce, wane ya ce. Da lalata dukiya. Da yawan roƙo (Bukhari da Muslim suka ruwaito).

Domin karanta cikekken littafin  Danna nan
labarin da ya wuceAibukan Damakwaraɗiyya Guda Ashirin Da Ɗaya (21) A Mahangar Musulunci
Labarin na GabaMENE NE KISHI?