Dalilan Da Ke Sa Kaurin Bangon Mahaifa Da Hanyoyin Magance Su

0
11

Endometrial hyperplasia yanayi ne wanda yake faruwa ga mace ta hanyar sanya bangon mahaifarta (endometrium) ya yi kauri fiye da kima. Abinda yake haddasa shi shi ne yawan hayayyafar ƙwayoyin halittar bangon mahaifa (overgrowth of endometrial lining cells). Endometrial hyperplasia ba cutar cancer ba ne. Amma wani lokacin idan ya yi tsanani, kuma ba a ɗauki matakin magance shi ba, zai iya rikiɗewa ya zamo cancer.

Babban abinda yake haddasa endometrial hyperplasia shi ne rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace (estrogen and progesterone imbalance). Waɗannan sinadaran su ne suke sarrafa yanayin zubar jinin al’ada da kuma girma ko kaurin bangon mahaifa. Ma’ana, abubuwan da suke haddasa endometrial hyperplasia su ne:

  1. Rashin daidaito tsakanin sinadaran estrogen da progesterone (imbalance of estrogen and progesterone): idan sinadarin estrogen ya fi sinadarin progesterone yawa a jikin mace, to, hakan zai sanya cells ɗin bangon mahaifarta su yi ta hayayyafa fiye da kima. Daga nan sai bangon mahaifar ya yi kauri sosai, kuma a sami matsalar endometrial hyperplasia. Abubuwan da suke sanya rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone ɗin su ne ƙibar jiki (obesity), kamuwa da cutar polycystic ovarian syndrome – PCOS, ko kuma ɗora mace akan magunguna masu haɓaka zubar ruwan sinadarai a cikin jikinta domin wata matsalar rashin lafiya da ta yi fama da ita.
  2. Gabatowar ɗaukewar al’ada (menopause): macen da ɗaukewar al’adarta ya gabato, za ta iya samun sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinta. Hakan zai iya haifar da zubar sinadarin estrogen fiye da progesterone.
  3. Matsalar rashin saka ƙwan haihuwa na lokaci mai tsawo (chronic anovulation): idan wani dalili ya sanya mace ba ta saka ƙwan haihuwa kuma ta daɗe a cikin wannan yanayin, to, za ta samu ƙarancin sinadarin progesterone a jikinta. Ma’ana ba ta da progesterone amma tana da estrogen. Hakan zai sanya cells ɗin bangon mahaifarta su yi ta hayayyafa fiye da kima kuma su sanya bangon mahaifar ya yi kauri.
  4. Teɓa ko ƙiba (obesity): kamar yadda na faɗa a sama, ƙibar jiki ga mace tana da alaƙa da hauhawar sinadarin estrogen, wanda shi kuma zai iya haifar da endometrial hyperplasia. Da wannan ne muke ganin beken matan da suke haukacewa wajen ganin cewa sun yi ƙibar karfi-da-yaji ta hanyar shaye-shayen magunguna.

Idan mace ta sami matsalar endometrial hyperplasia, to, matakan da za a iya ɗauka domin magance shi sun danganta ne da tsananinsa (severity) da kuma wanzuwar cancer cells a cikinsa (atypical cells). Saboda haka, za a iya magance endometrial hyperplasia ta hanyoyi kamar haka:

  1. Ɗora mace akan magungunan haɓaka zubar ruwan sinadarin progesterone a jikinta (progesterone therapy): tunda bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa samuwar sinadarin estrogen fiye da progesterone ne yake haddasa endometrial hyperplasia, to, za a iya ɗora mace akan maganin progestin mai haɓaka progesterone. An fi yin amfani da magungunan progestin ne idan endometrial hyperplasia ɗin ba a ga cancer cells a cikinsa ba (non-atypical hyperplasia).
  1. Yin tiyatar yayyanke tsiron bangon mahaifar (dilation and curettage – D&C procedure): ita ma wannan hanyar ana yin amfani da ita idan ba a ga cancer cells a cikinsa ba.
  1. Cire mahaifa gaba-ɗaya (hysterectomy): wannan hanyar ana yin amfani da ita ne ga macen da ta wuce shekarun haihuwa, sa’annan kuma aka ga akwai cancer cells a cikin endometrial hyperplasia ɗin. Likita yana bayar da shawarar yin wannan tiyatar ne domin mace ta kauce ma hatsarin kamuwa da cutar cancer ta mahaifa (uterine cancer).
  1. Canza tsarin rayuwa (lifestyle changes): idan endometrial hyperplasia bai yi tsanani ba, to, mace za ta iya magance shi ta hanyar canza tsarin rayuwarta. Ma’ana ta ɗauki matakin rage ƙiba ta hanyar daina ci da shan duk abubuwan da suke haddasa ƙiba, tare da yin ayyukan motsa jiki (physical exercises).
  1. Zuwa asibiti akai-akai domin a duba lafiyarta (regular medical check ups): yin wannan zai taimaka ƙwarai wajen gane cewa endometrial hyperplasia ɗin zai zamo mai hatsari ga lafiyarta ko kuwa a a.

    Domin karanta bayani akan sankarar bakin mahaifa danna nan

Edita: Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceHaihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)
Labarin na GabaSunayen Annabi Muhammad (S.A.W)