1. Wajen shuka
Dukkanin wanda zai noma irin wannan masara, don samun masara mai inganci, to ya kamata ya yi la’akari da;
a. Ƙasar wajen da zai yi shuka ta kasance ba ta ajiye ruwa sosai, kuma wajen bai da alaƙa da kan hanyar ruwa mai ƙarfi, kamar kogi ko dam.
b. Ƙasar wajen ta kasance tana da kyau sosai, wato tana ɗauke da takin gargajiya.
c. Rage wajen ƙona ciyayi a cikin gonar.
d. Yin huɗa da garma mai kyau.
2. Iri (abin da za a shuka)
a. A tabbatar da irin da za a shuka mai kyau ne kuma mai inganci.
b. Bayar da tazara tsakanin shuka da shuka da takun ƙafa ɗaya (25 cm) da kuma tazarar ƙafa uku a tsakanin kunya zuwa kunya (75 cm).
c. Idan kuma mutum zai shuka wani abu a cikin masarar, to ana buƙatar ya bayar da tazarar ƙafa ɗaya da rabi zuwa biyu (40cm-50cm) kamar wake, dawa, gero da sauransu.
d. A tabbatar an tona rami sosai, ta yadda shukar za ta zauna a cikin ƙasa sosai.
e. Za a iya sanya irin a cikin ruwan ɗumi, don kashe ƙwarukan da suke cikin irin.
3. Taki
a. A tabbatar takin da za a sanya ma shukar, yana da inganci sosai.
b. A binne takin a jikin jijiyoyin shukar, maimakon watsawa da ake yi gona.
c. A tabbatar an yi amfani da wadataccen taki a gona, misali a yi amfani da takin kamfa 15-15-15 ko 20-10-10 buhuna biyar da kuma buhuna uku na yuriya (Urea) ga shukar da ta kai hekta ɗaya.
d. Ana fara amfani da takin kamfa ne a shuka, bayan an samu kamar sati biyu da shuka, sai kuma bayan sati huɗu, sai a yi amfani da takin yuriya.
4. Hanyoyin magance ciyawa da ƙwari
a. Manomi, ya tabbatar ya nome ko feshe dukkanin wata ciyawa da take cikin gonarsa.
b. A yanzu ana amfani da maganin ƙone ciyawa a gona, wanda shi ne ma ya fi sauƙi ga manomi, sai dai ana buƙatar manomi ya nemi shawarar malamin gona, kafin ya yi amfani da maganin ƙone ciyawa, don kaucewa asarar abin da ya shuka a gonarsa.
c. Manomi, ya dinga ziyartar gonarsa akai-akai, don lura da halin da shukarsa take ciki, idan ya ga wani abu a gonarsa kamar ƙwari ko shukarsa ta canza launinta, to ya tuntuɓi malamin gona.
5. Dabarun girbin masara
a. Manomi, ya tabbatar masararsa ta bushe sosai, tun kafin ya girbe ta.
b. A yi amfani da waje mai tsabta, don casa abin da aka noma kamar buhu, tanfal da sauran su.
c. A samu mazubi mai kyau, don adana abin da aka casa, idan kuma ajiye ta za a yi zuwa wani lokaci mai tsawo, to a sanya mata maganin ƙwari a ciki, don kaucewa asara.
d. A tabbatar an raba masarar da kan ƙasa, wato a samu wani abu a ɗora buhuna masarar a kai.
Danna nan don karanta dabarun noman zamani
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu