Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

0
190

PID: wata cuta ce wacce ta ke addabar ɓangaren da ta shafi mahaifar mace, mutane da dama a Nahiyan Afirka suna fama da wannan ciwon.

Wasu ƙwayoyin cututtuka né, idan sun samu sun shiga mahaifar mace (uterus, fallopian Tubs, ovaries ) sai su haifar da Cutan PID.

Daga cikin alomaminta akwai:


1- Ciwon ƙasan cibi (ciwon mara).
2- fitar da ruwa mai wari a gaban mace.
3- Ganin jini a gaban mace musamman lokacin jima’i da bayan jima’i.
4- Zafi lokacin jima’i.
5- Zazzaɓi da jin sanyi.
6- Zafi lokacin fitsari ko wahalar fitsari.
7- Ƙaiƙayin gaba.
8- Rashin daidaitawar jinin haila.
9- Tashin zuciya
10- Ciwo lokacin jima’i
11- Ciwon baya.

Hanyoyin da ake ɗaukar wannan ciwon sun haɗa da:


1- Jima’i da namiji mai ɗauke da cutar gonorrhea ko clymadia.
2- Amfani da kayan karɓar haihuwa waɗanda ba su da tsafta.
3- Yawan kai ɗan yatsa cikin farji.
4- Amfani ni da wando (fant) wanda mai ɗauke da wannan cutar ta yi amfani da shi.
5- Rashin amfani da condom lokacin jima’i.
6- Yawan tsaftace gaba da sabulu musamman masu ɗauke da sinadaran kashe ƙwayoyin cuta.
7- Yawan amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta irin su: Ampiclox da muka dabi’untu da shan su kullum.

PID idan ba a magance shi da wuri ba, yana sabbaba waɗannan matsalolin kamar haka:


1-Rashin haihuwa
2-Zaman ciki wajen mahaifa(entopic pregnancy).
3-Yakan kawo ɓari (abotion ko Miscarriage)
4-Ciwon mara da baya mara jin magani.

Hanyoyin kariya daga waɗannan cututtuka sun haɗa da:


1- Amfani da Condom lokacin jima’i, yana rage yaɗuwar PID kashi 95%.
2- Mace ta tsaya a kan namiji guda ɗaya, kuma a tabbata an yi gwaji kafin saduwa ko sun yi aure.
3- A kiyaye yawan saka hannu a farji.
4- A tsaftace wandon sakawa musamman pant, kuma a kiyaye amfani da pant na wata.
5- A dinga tsaftace kayan karɓar haihuwa da kuma wanke ciki.

Wannan ciwo na PID yana da magani idan aka bi hanyoyi masu kyau:

1- Da Zarar mace ta ga alamun da muka lissafa a sama, ta gaggauta zuwa asibiti

Daga nan likita zai yi gwaje-gwajen da ya kamata a yi, an tabbatar an gano matsalar, sannan a bada magani.

2- Idan kina da miji shi ma, ya kamata ya je a gwada shi; a ba ku magani tare.

3- Daga nan sai a ƙaurecewa jima’i sai likita ya tabbatar muku kun warke.

GARGAƊI

Idan mace tana tare da wannan cutar kuma ta yi shiru ta zauna saboda kunya ko makamancin haka, yakan jawo mata matsala a mahaifarta, daga nan za ta fara somawa da matsalar zubar da ciki (miscarriage) zaman ciki wajen mahaifa (Ectopic pregnancy) ko kuma rashin ɗaukar ciki gabaki ɗaya. karanta yadda jinin Haila yake ko Yadda ake gwajin juna biyu

Lafiya Uwar Jiki.

labarin da ya wuceMatsalar Fata Dake ɓangaren Ido (CONJUNCTIVITIS)
Labarin na GabaAlamomin Shigar Ciki (Juna Biyu)