Great Britain, Ingila ke nan duk da yake ita ta zama ta fi kowacce cin ribar cinikin Bayi, ba ta soke bauta ba da wuri, sai bayan an ɗauki lokaci, inda sauran ƙasashen Turai suka ce sun haramta cinikin Bayi.
Ƙasar da ta fara yin doka ita ce, Denmark a shekara ta 1804, Ingila ta yi a shekara ta 1807, sai Amerika ta yi a shekara ta 1808, sai Sweden a shekara ta 1817, sai Holand a shekara ta 1814, an ba da dalilin da yasa su Turawa ba su damu da cinikin Bayi ba da azabar bautar da mutane da ake yi saboda su ma a ƙasar su ana azabtar da mutane da suka yi ɗan laifi kaɗan, sai ka ga mutum ana bin sa kuma a ƙarshe an zo an kashe shi, ko an tsire shi, ko an ɗauke shi an jefar da shi a wata ƙasa.
Duk wannan zaluncin su ma ya dame su sai ya zamanto ma ba sa ganin zaluntar da ake yi wa Bayin, sai da abubuwa suka fara kankama tukunna, aka fara sanin cewa lallai fa Bayi suna shan wuya, wani lauya ana ce masa Grandba Shap ne ya fara ƙoqarin maganar ‘yantar da Bayi, ya taimakawa wani Bawa da ya gudu ana ce masa Somaset.
Wannan Bawan ya gudu aka je aka kamo shi za a dawo da shi, sa ya shigar da ƙara a gaban alƙali wato Lord…. inda aka yi wani abu da ake ce masa Read of Habees copus cewa lallai a kawo shi wannan bawa kotu, kawo shi kotu da hukuncin da shi Lord Chief Mans… ya bayar ne ya fara jawo mutane su san cewa lallai akwai azaba a harkar cinikin Bayi. Kuma abin ya samu karɓuwa, cewa a san yadda za a yi a hana wannan.
Bayan shekara goma sha biyar ana ta wannan gwagwarmaya da mutane irin su Williams Wilberforce da wannan Grandba Shap da Thomas Clascis suka yi wata ƙungiya suka kira ta da Society for the Revolution of Slave Trade, kuma shi Willberforce ya zama shi ne mai magana da yawun su a majalisa, har yasa dai aka yi wannann doka ta shekarar 1907.
Amma dai sun ci gaba da yin gwagwarmaya da sauran mutane da yin wannan, inda daga baya Ingila ta ce lallai za ta hana wannan cinikin, amma dai ba wai sun hana ne don tausayi kaɗai ba, akwai maganar tattalin arziki da maganar sun samu ci gaban masana’antu (Industrial revolution). Bayin dai buƙatar su ta ragu a ɓangaren tattalin arziki a Ingila, tunda Ingila ta ci gaba kuma suna ganin cewa, gwanda mutane a ƙyale su a Afrika su dinga yin noma don a samu wanda ake yin amfani da shi a masana’antu (Factories).
Ingila da sojojin ta na Ruwa suka ɗauki gabaran hana wannan ciniki tunda ta fi kowa ƙarfi a ruwa, su za su yi maganin cinikin Bayin nan. Duk da haka dai abin ya ba su wahala yadda mutane suke ta ƙoƙarin su kauce mu su, sun fito da dabaru da yawa na kaucewa inda za a kama su, duk da dai an kama jirage da yawa.
A cikin shekara 20 daga 1818-1838 an kama jirage 280 da wani abu, haka dai kullum jiragen da ake kamawa ƙaruwa suke inda a shekarar 1845 ma an kama jirage 30, amma duk da haka sun ci gaba da yin dabaru su masu ɗiban Bayin nan domin su kaucewa sojojin ruwa na Ingila, domin duk jirgin da suka kama saisu kai shi Freetown Sierra Leon a nan a ke yi masa hukunci.
Wani lokacin ma su masu cinikin Bayin sai su ɓoye su ko su zubar da su a ruwa domin kada a kama su, sai da aka canja dokar aka ce idan an ga wasu abubuwa da suka yi kama da kayan cinikin Bayi a kama jirgin shi ma a yi masa shari’a.
Wasu idan an kama su an kai su Sierra Leon ɗin nan to sai a saki Bayin tun da wannan gari ana ce masa Freetown, wasu idan an sake su Mishan suna ɗaukan su su koya mu su karatu su mayar da su Kirista da sauransu. Har ma aka samu wani babban Kirista da aka taɓa yi a Najeriya ana ace masa Bishop Samuel Ajayi Crowther wanda shi ma aka sace shi aka mayar da shi Bawa a shekarar 1821.
Haka aka ɗauke su daga wannan hannu zuwa wannan tun da yana da rabon zai tsira aka kai shi Sierra Leon daga nan kuma dai ya samu ya kuɓuta tunda an kama jirgin da yake ɗauke su, aka mayar da shi Kirista a shekarar 1825 aka yi baptizing ɗinsa ya zama Samuel Crowther, wanda yasa aka sa masa wannan su na shi ne shugaban Cochi a nan Sierra Leon.
Kowa ya san gwagwarmayar da ya yi wajen kawo addinin Kirista Najeriya, shi ne ɗan Afrika na farko ɗan asalin Najeriya da ya zama Bishop na Angalican kuma ya shahara, yana ɗaya daga cikin mutanen da aka kuɓutar da su daga hannun masu cinikin Bayi.
Haka dai suka yi da aka gama cinikin Bayin nan sai ya zama cewa, Mishan sun duƙufa sosai wurin yaɗa addinin kirista, saboda su wanke laifukan su da suka yi wa mutanen Afrika su kawo mu su addinin kirista. Wannan abu ya yi tasiri da yadda su Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da Mishan don su tabbatar da mulkin su a Afrika ta yin amfani da Mishan da cinikayya da dabaru da sauran su har suka zo suka tabbata, tun da an gama cinikin Bayi an shiga wata marhala ta danniya daban (mulkin mallaka).
Don karanta tarihin Afrika danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu