Baɗi Ba Rai Kashi Na Ɗaya

0
113

A short story by
Sakina Yazid (Innar su Amal)

Kamar duk lokacin da irin wannan abun ya faru yau ɗin ma haka ta shiga gidan cike da tashin hankali; duk da dai ta daina kukan ta share hawayenta. Hawayen iya na fuskarta ne kawai ta share amma tabbas ta san ba za ta iya daina kukan zuciya ba, ko za ta daina to ba ta san lokacin da za ta daina ɗin ba.

Parlor ɗin shiru, da alama Umma da kuma su Maimuna suna ɗaki; wataƙila suna sallar la’asar domin lokacin sallar ne. Kai tsaye ta wuce ɗakin Umman ta tura ƙofar ta shiga da sallama.

A kan dadduma ta hango Umman tana zaune tana azkar. Kallon da Umman ta yi mata ya sa duk wani karsashi da ta taho da shi ya zube kafin ta ƙarasa gabanta. Ta riga ta san amsar da Umman za ta ba ta guda ɗaya ce; wato wadda ta saba bata. Zuwa yanzu ma gani take yi gaba ɗaya kamar Umman nata ta ƙosa kuma ta gundura da jin matsalolinta.

To amma idan ba wajen Umman ba ina za ta? Da wa za ta yi magana ta ji sanyi a ranta? Duk da dai yin maganar bai taɓa samar mata mafita ba. An riga an hane ta da yin ƙawaye tun lokacin da aka yi mata aure, don haka ta fita harkar ƙawayen har su ma suka rabu da ita. Mutum biyu ne a rayuwarta iyayenta da kuma mijinta Misbahu; su suka fi mata kowa muhimmanci a rayuwarta kuma su ne suke neman tura cikin halaka.

Cikin sanyin jiki ta ƙarasa gaban Umman ta sauke goyon Adnan ta zaunar da shi; nan da nan kuwa ya rarrafa yana dariya ya haye jikin Umman wadda ta ɗauke shi tana dariya.‘Umma ina wuni.’ Ta faɗa cikin sanyin murya. Ta harareta sannan ta amsa ‘Lafiya ƙalau. Yanzu kuma me aka yi na ganki fuska duk a koɗe?’

Ta sunkuyar da kai ta yunƙura ta haɗiye malolon da ya tokare mata ƙirji, ta buɗe baki da ƙyar tace ‘Umma duka na ya yi, kuma ya gaya min maganganu na wulaƙanci fiye da yanda ya saba gaya min. Ga neman mata Umma, a gabana zai yi waya da budurwa ya saka a loudspeaker wai na ko yi soyayya.’

Cikin damuwa Umman ta sauke Adnan wanda ya kama rarrafe a tsakar ɗakin, ta dube ta cikin natsuwa kamar me nazari sannan tace ‘To in dai maganganu ne menene ba ki ji ba a bakin Misbahu? Ai tuntuni nace ki fita harkarsa ki mayar da hankali wajen wannan yaron da Allah ya ba ki. Kuma yau ya aka yi kika biye masa har ya kai miki duka?’

Ta share hawayen da ya gangaro a kan fuskarta, ta yi ajiyar zuciya a karo na babu iyaka sannan tace ‘Hayaniyarsa ya gama yi ya shiga ɗaki ya kwanta shi ne na shiga maƙota dubiya. Shi ne ina dawowa ya hau zagina, kuma na ce ya yi haƙuri shi ne ya mammare ni yace wai zuwa na yi maƙota na kai gulmarsa.’

Nan da nan ta sake fusata tace ‘To ke me ya kai ki maƙota kin riga kin san halin mutumin nan? Na riga na gaya miki ki fita harkarsa ki bar shi da mugun halinsa. Idan ba ya son shiga maƙota to ai sai ki bari. Umma bai taɓa hana ni shiga ba wallahi. Kuma na gaya miki idan ya tashi wulaƙancinsa bana ma sanin me na yi masa, tunda ko na saba yin abu wataran sai kawai ya hau zagina a kai.’

‘To ai sai ki kiyaye, tunda kin ga dai mahaifinki da kansa ya yi masa magana kuma yace ya daina. Ki je ki cigaba da lallaɓa shi ki mayar da hankali kan ɗanki. Bawa ba ya wuce ƙaddararsa, wata ƙila ke taki ƙaddarar kenan.’

Suka yi shiru na ɗan lokaci; Farida tana ta faman share hawaye yayin da Ummanta take faman hidima da Adnan. Jimawa kaɗan tace ‘Umma na gaji da auren mutumin nan wallahi, son shi ya fice min daga rai. Bana son zaman gidansa; idan ina cikin gidan ji nake kamar an saka zuciyata a keji kuma an kunna wuta a cikin kejin. Wallahi Umma wulaƙancin da yake min ya ishe ni.’

Ta kawar da kai tare da haɗe fuska sannan tace ‘Haƙuri za ki je ki yi, tunda dai mutumin nan babu abinda ya rage ki da shi; ci, sha sutura da sauransu. Ko muma nan kullum cikin hidima yake da mu. Kina kallo ga ƙannenki can a gidajensu amma ke kullum kina tafe kawo ƙara. Ni kaina da kika gani idan da ban yi haƙuri da ubanku ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.

Kuma ma idan dai maza ne na yanzu duk haka suke kowanne da tashi matsalar musamman neman matan; idan kin fito ba ki san gidan wanda za ki koma ba. Idan ma kin sami mijin kenan.’

Haka dai Umma ta ƙare mata faɗa da nasiha sannan ta tursasata ta koma gidan; domin a faɗarta ba ta ma so a ɗaga maganar balle mahaifinta ya ji don ita ma sai ya yi mata faɗa. Don haka cikin matsananciyar damuwa ta goya Adnan suka kama hanya.

Ƙwaƙwalwarta ta cushe gaba ɗaya; wace irin rayuwa ce wannan? Auren soyayya suka yi da Misbahu amma yanzu ba shi da aiki sai cuzguna mata; duk da dai ba wai kullum ba ne yake mata hakan. Sai suna zamansu lafiya kamar kowanne ma’aurata laifi kaɗan sai ya gaya mata maganganu masu zafi watarana ma ya mammare ta.

Ga shi ba ta sanin wanne laifi ne za ta yi ya haifar da hakan don haka kullum a ɗari-ɗari take a gidan. In dai haka maza suke to idan ta samu ta rabu da Misbahu ma babu wani auren da za ta sake balle a ce ba a san wa za ta aura ba; tana ji a jikinta zawarci zai fi mata sauƙi da wannan rayuwar da take yi yanzu.

Tana hango gidan bugun zuciyarta ya ƙara sauri, wata sabuwar fargaba ta shige ta. To amma idan ba nan ba ina za ta? Gidansu ne kawai ragowar gatanta kuma can ta je aka koro ta. Haka ta ƙarasa ta shiga gidan tana fatan idan dai har mutuwa ce za ta raba ta da Misbahu to tabbas ta shirya mutuwa don tana da yaƙinin Allah zai ji tausayin ta.

Yana kashingiɗe a parlor ɗin a kan 3-seater ta tura ƙofar ta shiga; ƙasa-ƙasa ta yi sallama ta shige ba tare da ta saurari amsa ba. Tana jin ƙwayar idonsa yana bin ta da kallo na wulaƙanci irin wanda ya saba. Sai da ta kai tsakiyar parlor ɗin tana daf da shiga ɗakinta ya daka mata tsawa.

‘Daga ina kike? Akuya sarkin yawo.’ Ta ɗan diririce tana shirin komawa da gudu sannan ta dage ta lalubo nutsuwarta cikin in-ina tace ‘Gidanmu na je. Ya sake ƙare mata harara yana jan dogon tsaki ‘Mtsewww!’ Ta bi bango ta shige ɗakin ta turo ƙofar tana fatan kada ya zo yace zai doke ta.

Haka ta lallaɓa ta yi sallar magriba sannan ta fito ta ɗora abincin dare tun kafin ya nema ya ɗaga mata hankali. Ya riga ya san babu abinda za ayi duk da kai ƙarar tasa da ta yi, don haka da ya fita ma bai dawo gidan ba sai da sha biyun dare ta gota; lokacin ta daɗe da yin bacci.

A hankali suka ɗan shirya kamar yanda suka saba, sai dai ita duk a firgice take. Zama take na ɗari-ɗari a gidan saboda ba ta san me za ta yi ta tsokano shi ba. A bayan layinsu aka yi haihuwa, kuma da yake ya san maigidan tun jiya ya ba ta izinin zuwa suna da ake yi yau Asabar.

Wajen 12pm maƙociyarta ta yi mata sallama a kan ta zo su je sunan don ita daga can za ta wuce cikin gari. Nan suka haɗu su uku maƙota suka wuce. Tun da suka shiga layin gabanta yake faɗuwa; akwai gidaje na ƴan jami’a a layin inda wasu ƴan mata ne suke zaman kansu wasu kuma samari.

Akwai wata yarinya Shahida wadda Misbahu yake nema; ba ta taɓa ganin yarinyar ba amma an tabbatar mata a nan layin gidan yarinyar yake. Don matan layinsu ma sun sha gaya mata sun gan shi da yarinyar ya sauke ta nesa da unguwar. Sun yi magana sau babu iyaka har ma ta gaji; tunda yanzu ma a yanda ake ya gaya mata idan ta ƙara yi masa maganar wata daga cikin ƴan matansa sai ya kora ta gida ya kawo matan gidan ya ga idan akwai wanda ya isa ya hana shi.

Haka dai ta dafe zuciyarta suka ƙarasa cikin gidan sunan; nan da nan kuma da suka haɗu da matan unguwa ta manta da komai aka ci gaba da hira cikin walwala. Sun kai kimanin awa ɗaya, ‘ƴan matan suka shigo gidan; da yake ba wani sosai aka cika tsakar gidan ba sai da suka tsallake suka zo kusa da Farida sannan suka zauna.

Suka gaggaisa da mutane da alama wasu daga cikin matan da suke zaune a wajen sun san su. Ita ma Farida ta waiga ta gaisa da su. Suka tambayi maijego aka ce musu yanzu ta shiga canza kaya don haka suka zauna nan aka cigaba da hira.

Jimawa kaɗan suka jiyo muryar maijego daga parlor tana magana da wasu matan. Ɗaya daga cikin ‘ƴan matan nan wadda take zaune kusa da Farida ta buɗe baki ta ƙwala mata kira bayan ta amsa tace ‘Da Allah ki zo ki nuna min matar masoyina na yi mata kallon ala tsine uwar mai ƙarya; ko da yake dai ya gaya min kalarta.’

Ta fito daga parlor ɗin tana dariya ta nuna yarinyar tana cewa ‘Shahida ba fa na son wulaƙanci, duka nan babu sa’anki ƴar rainin hankali.’ Aka sheƙe da dariya gaba ɗaya wajen. Farida tana jin an ambaci Shahida ta sha jinin jikinta; ta juya ta kalle ta suka haɗa ido yayin da yarinyar ta tintsire da dariya. Maƙociyarta wadda suka zo tare ta taɓa ta tace ‘Tashi mu tafi Maman Adnan.’

Suka miƙe a tare, ita ma Shahida ta miƙe tana dariya da kallon raini tana cewa ‘Ashe ma kusa dake na zauna, sannu fa. Mai jego tace ‘Ke Shahida ba fa na son raini… A a ku fa uwayen gidan nan haka kuke wallahi, ba ku iya kula da miji ba sai ikon tsiya. To komai baƙin cikinku sai mun shigo.’ Ta faɗa da shaƙiyanci tana dariya.

Farida ta ja tsaki, ta raɓa ta gefenta ta wuce, maƙociyarta Anti Amina tana biye da ita. Ta ƙyalƙyale da dariya tace ‘A a fa kada ki bangaje ni idan ba haka ba wallahi na sa a baki red card a daren nan ki kwana gidan father ɗinki. Farida ta shammaci mutanen da suke wajen ta juya ta yi taku ɗaya ta ƙarasa gaban Shahida ta sauke mata mari a kumatunta.

Nan take wajen ya yi tsit yayinda Shahida ta dafe kumatunta tana fitar da hawaye. Farida ta nuna ta da yatsa tana cewa ‘Idan ke ‘ƴar halak ce ki ba shi umarni kada ya bar ni na kwana a gidan yau.’ Ta sauke yatsan sannan ta cigaba ‘Ko da yake ba zan yi mamaki ba idan ke ɗin ba ‘ƴar halaka ba ce tunda ga shi nan kin mayar da kanki kamar public toilet.

Kowa ya tashi juyen ƙazantarsa sai ya zo ya haye kanki. Ki bashi umarni yau kada ya bari na kwana a duniyar ba ma a gidansa ba. Ta juya ta fice ba tare da ta saurari kowa ba Anti Amina tana biye da ita. Nan ragowar matan da ke tsakar gidan suka haɗu da maijego suka fara ba wa Shahida haƙuri.

Ta share hawayenta ta zauna, ta zari wayarta tana cewa ‘Wallahi sai ta gane kurenta, sai na saka ya ci ubanta tunda ta mare ni. Kuma wallahi ita da zaman lafiya da Misbahu har abada, sai na yi ajalin wannan auren nata.’

Suka cigaba da ba ta haƙuri maijego tana cewa ‘Ki dai yi haƙuri ki bar maganar nan tunda kin ga kece ba ki da gaskiya, Please ki fita harkar ta.’ Ta goge fuskarta ta dubi matan tace ‘Ku yi shiru zan yi waya da Allah.’ Nan da nan suka yi shiru saboda son jin gulma.

Ta lalubi lambar Misbahu ta danna masa kira; bugu ɗaya kuwa ya amsa yana cewa ‘Ƴan matana ya aka yi ne, har kin…’ Nan take ta rushe da kuka; abinda ya saka shi ya ruɗe ya shiga jero mata tambayoyi ‘Babe me ya faru? Kina ina ne? Ko accident kika yi ne?’
Ta sassauta da kukan tace ‘Matarka ce ta mareni kuma ta zazzage ni a cikin mutane.’

Cikin ƙosawa yace ‘Ban gane ba, Farida? A ina kuka haɗu? Ko gidan kika je? Ta sheƙe majina irin na me kuka tace ‘A gidan suna muka haɗu nan kusa da gidanmu, shi ne ƙawarta ta nuna mata ni suka haɗu suka yi min wulaƙanci a cikin mutane kuma ta mammare ni.

Dole sai fitowa muka yi ni da Ikram saboda kunya. Wai ni take kira public toilet har da cewa ni ba ƴar halaka ba ce. ‘Ya isa, ki daina kukan mana. Kina ina ne na zo yanzu? Sai na ji yanda aka yi, kema kin san ba zan ƙyale ta ba.’ ‘Ni kada ka zo inda nake, ai duk kai ka janyo tunda kai ne kake zuwa kana ba ta labari na har ta sami damar yi min wulaƙanci.’

Ta tsinke wayar ba tare da ta saurari amsar shi ba, ta mayar da wayar cikin jakarta ta kama hannun ƙawarta suka fice.

Cike da damuwa Farida ta koma gida; ba ta nadamar marin da ta yi wa Shahida, amma dai tana fargabar haɗuwarta da Misbahu. Don ta san tabbas idan bai mammare ta ba to sai ya yi mata zagi na ƙasƙanci; idan ba ta yi wasa ba ma to sai ya ba ta red card kamar yanda budurwar tasa ta faɗa.

Haka Anti Amina ta ɗauki lokaci tana ba ta haƙuri sannan ta bar ta ita ma ta wuce nata gidan. Ba ta jima da shiga gidan ba Maryam yarinyar da take mata aiki ta shigo; tunda dama tace mata ta zo bayan 2pm. Ta ji daɗin shigowar tata saboda ta san ko da Misbahu zai shigo yanzun to zai ƙyale ta a ƙalla zuwa lokacin da Maryam ɗin za ta tafi; kafin nan ta samu ta shirya yanda za ta ƙwaci kanta.

A fusace ya shigo gidan wajen 2:30pm; tunda sai da ya tsaya a wajen Shahida ya lallaɓa ta yayin da ita kuma ta ƙara yi masa fanfo sannan ya huto gidan. A lokacin da ya shiga gidan Maryam tana kitchen tana aikinta yayin da ita kuma Farida take ɗaki tana kwantar da Adnan wanda ya yi barci.

Ba ta rufe ƙofar ɗakin sosai ba don haka bai ma kula da mutum a kitchen ba ya shige ɗakin. Tana ƙoƙarin yi masa sannu da zuwa ya kama hannunta ya janyo ta daga ɗakin tana turjewa tana tambaya ‘Abban Adnan lafiya kake ja na haka? Ka bari na gyara masa kwanciya mana.’

Bai saurare ta ba kuma bai fasa jan nata ba, har sai da suka fito ƙofar ɗakin sannan ta samu ta fincike hannunta. Cikin ƙarfin hali tace ‘Wai meye haka Misbahu, ya za ka kama ja na kamar wata yarinya.’

Ya ɗan ja baya yana mata kallo na takaici da mamaki saboda bai taɓa zaton za ta iya yi masa magana haka ba. Ita kanta ba ta san ina ta samu ƙwarin gwiwar ba amma tabbas tana jin yau ba za ta saurara masa ba.

Cikin huci yace ‘Ni za ki yi wa rashin kunya saboda ba ki da mutunci ko? Saboda kin haɗu da ƴan iskan ƙawayenki sun hure miki kunne ko?’ Ta sun kunyar da kai tana ja da baya saboda yanda yake nufo ta, sai dai kafin ta yi wani yunƙuri ya kwaɗa mata mari. Tana ƙoƙarin dafe kumatun ya sake kwaɗa mata a ɗayan sannan yace ‘Wace shegiyar ce tace ki mari Shahida? Kuma sannan ki zage ta?’

Nan da nan hawaye ya wanke mata fuska, cikin ƙunan rai tace ‘Ita ba ta gaya maka abinda ta yi min ba kafin na mare tan, ko kuwa nice wadda ba ni da gata da za ka zo kana mari na saboda karuwa? Ya yi wata ‘ƴar dariyar mugunta sannan yace ‘An mare ki ɗin, ko akwai abinda za ki iya yi a kai? Shashasha kawai.’

Cikin kuka tace ‘Babu abinda zan iya yi amma zan cigaba da kai ƙara wajen Allah. Duk wanda ya zalunce ni Allah ya isa ba zan taɓa yafewa ba.’

A fusace ya fara ƙoƙarin kwance belt ɗinsa yana cewa ‘Lallai yau za ki gane kurenki, ni kike yi wa Allah ya isa saboda ba ki da mutunci? Jikinki zai gaya miki. Kafin ta yi wani yunƙuri ya zabga mata belt ɗin wanda ya bi ta wuyanta ya sauka a saman bayanta. Ta gantsare ta saki wata ƴar ƙara tana ƙoƙarin sosa wajen dukan; wanda tuni ya riga ya yi ja zur ya tashi.

Ya sake ɗaga belt ɗin ya zabga mata. Ta ja baya kamar za ta faɗi bango ya tare ta; ƙoƙari take ta shiga ɗakinta ta turo ƙofa amma sai da ta wuce ƙofar sannan bangon ya tare ta. A nan ta sulale ta zube saboda zafin dukan da kuma gigicewa. Ya gyara belt ɗin ya riƙe ƙasan yanda ƙarfen belt ɗin zai sauka a jikinta; a daidai lokacin kuma Adnan wanda ya riga ya tashi daga bacci har ya sauko daga kan gadon ya rarrafo ya nufi jikin mamansa yana kuka.

A lokacin Misbahu ya riga ya ɗaga belt ɗin zai zuba mata; tana ƙoƙarin ɗauke Adnan belt ɗin ya sauka a ƙeyarsa. Nan take jini ya wanke mata jiki yayin da Adnan ɗin ya yi wata gajeriyar ƙara ya faɗa ƙirjinta kamar wanda aka jefa.

Ta jijjiga shi cikin matsananciyar firgita tana kiran sunansa; a dai-dai lokacin Misbahu ya saki belt ɗin ya nufo kanta yana ƙoƙarin karɓar Adnan ɗin yana cewa ‘Me kika yi masa? Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un!’

Maryam wadda take tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon su tana share hawaye ita ma ta zuba ihu ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un!’ Kafin su yi wani yunƙuri ta zura da gudu ta yi waje ta ƙofar kitchen tana faman ihu tana kiran mutane.

Nan da nan jikin Misbahu ya hau rawa suka miƙe tare da Farida wadda ita ma jikinta yake rawa tana ta wani gunji ta ƙanƙame Adnan saboda yanda hawayenta ya bushe ta kasa kuka. Kai tsaye waje Farida ta nufo rungume da Adnan yayin da shi kuma Misbahu ya juya kan center table inda ya ajiye mukullin motarsa yana cewa ‘Ki tsaya na fito mu kai shi asibiti.’

Kusan a lokaci guda suka ƙaraso tsakar gidan inda suka ci karo da Maryam mutum uku sune biye da ita; maƙocinsu Dr. Abdul da wani mutum tare da shi sannan kuma da maigadin gidan. Dr. ya sha gaban Farida wadda ko ɗankwali babu a kanta yana cewa ‘Subhanallah! Me ya sami Adnan ɗin?’

Cikin rawar baki tana waigawa tana kallon Misbahu tace ‘Ya fasa masa kai da belt, ya kashe min yaro. Maryam wadda take share hawaye ta tsomi baki tana cewa ‘Dukanta yake yi da belt ɗinsa wallahi yana ɗagawa ya kwaɗawa yaron, dukansa ya yi da belt ɗin. Shi ne baban nasa.’

Dr ya ja su suka koma kan baranda sannan ya ba ta umarni ta kwantar da Adnan. Nan ta shimfiɗe shi ta janyo gefen rigar ta ta fara goge fuska ba tare da ta damu da jinin da yake jikinta ba. Ya dudduba shi sannan ya juya ya dubi mutumin da suka zo tare da shi yace ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Wannan sai dai a yi haƙuri Allah ya karɓi kayansa.’

Nan take Farida ta juya ta cakume Misbahu tana cewa ‘Ka kashe min yaro, sai ka kashe ni ni ma. Da ƙyar ya samu ya haɗa hannuwanta ya riƙe tana faman kuka. A hankali kuma kamar wadda aka zarewa laka ta sulale ta zauna kamar me zaman tahiya ta haɗa hannuwanta guda biyu ta rike tana fitar da numfashi a hankali.

Maryam ta ƙaraso ta zauna a kusa da ita suka yi jugum suna bin mutane da kallo. Mutumin da suka shigo da Dr ya dube shi yace ‘Ai sai an kirawo police tunda ya zama case ɗin accident kenan. Ba tare da ɓata lokaci ba ya fidda wayarsa ya kirawo ‘ƴan sanda, a lokacin ne kuma Misbahu ya sami dama ya koma gefe ya kirawo mahaifiyarsa.

Jimawa kaɗan ita ma Maryam ta miƙe ta koma cikin gidan ta ɗaukowa Farida hijab ta zo ta saka mata sannan ta kama hannunta ta dangwala a wayarta ta buɗe ta lalubo lambar Ummanta ta kirawo ta. Abinda kawai ta iya gayawa Umman Farida shi ne Adnan ya rasu, ta katse wayar ta riƙe a hannunta suka cigaba da kallon ikon Allah.

Kusan a lokaci ɗaya ƴan sandan suka iso da mutanen gidan su Adnan, kafin wani lokaci kuma mutanen gidansu Farida suka iso. Mahaifin Adnan shi ya ja ƴan sandan ya sallame su, kusan ma babu wanda ya kula da lokacin da suka sulale suka fice.

Tunda Umman Farida ta iso take fama da Farida a kan ta shiga cikin gidan su zauna amma ta ƙi, kuma ta ƙi yi wa kowa magana. Don haka suna nan tsaye aka yi wa Adnan sutura aka yi masa sallah yayin da Umma da Maman Adnan suke tsaye sun saka Farida a tsakiya suna lallashinta.

Ana fita da gawar mata suka fara shigowa gidan domin ta’aziyya, sai dai har zuwa lokacin Farida ta ƙi shiga cikin gidan ga shi magriba ta fara kawo kai. Da yake maƙabartar babu nisa nan da nan aka kai shi aka dawo. Babu wanda ya kula da lokacin da Farida ta sulale ta fice daga gidan ta kama bin hanya.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Gamuwa Da Abokan Gaba Ko Wani Mai Iko 
Labarin na GabaBaɗi Ba Rai Kashi Na Biyu
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.