MOHAMMED BALA GARBA
Wasu sun san garuruwan da ake kira ‘Hausa Bakwai’ da ‘Banza Bakwai’ amma ba su san dalilin da ya sa ake kiransu da waɗannan sunayen ba. Wannan ne ya sa na ga dacewar yin wannan ɗan takaitaccen bayanin kamar yadda na taɓa karantawa a littafin ‘Kano Ta Dabo Cigari’ na Marigayi Wazirin Kano Alhaji Abubakar.
Bayan Bayajidda ya gudo daga ƙasar Borno shi da matarsa mai suna Magaram saboda yunƙurin kashe shi da Sarkin (Shehu) Borno ya yi, sai suka zo wani gari da ake kira Garun Gabas a ƙasar Haɗeja. A nan ya bar matarsa saboda tsohon cikin da take ɗauke da shi ya wuce Daura.
Bayan ya isa Daura cikin dare, ya sauka a gidan wata tsohuwa, sai ya nemi ruwa amma bai samu ba. Tsohuwar take faɗa masa dalilin da ya sa ba sa samun ruwa sai sau ɗaya a sati saboda wata macijiya da take hana ɗibar ruwan. Da Bayajidda ya ji haka, sai ya karɓi guga a wajen tsohuwar, ya nufi rijiyar Kusugu inda macijiyar take ciki, ya kashe ta ya ɗebi ruwa.
Da gari ya waye, Sarauniya Kabara (wacce take mulkin Daura) ta ji labari, sai ta sa aka yi bincike aka gano Bayajidda ne ya kashe macijiyar. Ta kira shi ta ce za ta basa rabin mulkinta. Amma ya ƙi amincewa, ya ce mata sai dai a ɗaura musu aure da ita idan ta amince. Sarauniya ta yarda, aka ɗaura musu aure da Bayajidda.
Sai jama’ar garin suka fara kiransa da ‘Makas-Sarki.’ Daga baya kuma suka koma ce masa ‘Sarki’ kawai. To daga nan ne aka samo kalmar Sarki da ake faɗawa wasu sarakuna a yau. Da Sarauniya Kabara ta haifi ɗa namiji, sai aka sanyawa yaron suna Bawo.
A lokacin da Bawo yake mulkin Daura, an yi wata masifaffiyar yunwa a ƙasar Hausa, wacce ta zama babu inda ake samun abincin mai yalwa sai a wani wuri wanda shi ne Kano a yanzu. Don haka ƙabilu suka riƙa ƙaura zuwa wurare masu ɗan yalwan abinci domin su tsira da rayuwarsu.
Bayan jama’a sun fita kowa ya samu in da ya fake, sai ya zamana babu shugabanci kowa zaman kansa yake. Daga nan sai zalunci ya yawaita a tsakanin jama’a. Masu ƙarfi su ƙwace kayan raunana. Wannan ne ya sa raunana suka fara kai kukansu Daura wajen Sarkin Bawo.
Da ƙararraki suka yawaita, sai Sarki Bawo ya yi shawarar kafa shuwagabanci a dukan waɗannan wuraren da abin ya dama. Sai ya tura ɗansa Bagauda zuwa Kano, ya tura ɗansa Gunguma zuwa Zariya, ya tura ɗansa Duma zuwa Gobir, ya tura ɗansa Kumayo zuwa Katsina, ya ba wa ɗansa Gazori riƙon Daura, ya ba wa ɗansa Zamna Biram, ya tura ɗansa Kogo zuwa Rano. Waɗannan garuruwa da Sarki Bawa ya ba wa ‘ya’yansa ko ya tura su, su ake kiran Hausa Bakwai.
Akwai kuma Banza Bakwai, wanda Sarki Bawo ya sake tura wasu ‘ya’yan nasa bakwai zuwa can. Sai dai kuma wasu masana sun ce ba ‘ya’yansa na cikinsa ba ne, ‘ya’yan ɗan uwansa mai suna Karaf-da-gari ne wanda Bayajidda ya haifa da wata baiwarsa mai suna Bagwariya. Waɗannan garuruwa bakwai da aka tura ‘ya’yan su ne: Zamfara da Gwari da Nupe da Yaruba (ilori) da Kwarrafa da Kebbi da Yawuri. Su ne ake kira Banza Bakwai.
Wannan shi ne asalin yadda aka samo sunan ‘Hausa Bakwai’ da kuma ‘Banza Bakwai’.
Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
08098331260.
Karanta Ta’aziyyar Hauwa Ƙamshi
Edita@rumasau-kallamu