Ga abinda yazo daga littafin tarihin Katsina
(Kitabu Taarikh Ummaratu Hazihil Qaryatu Al-mashhuratu bi- Katsina min binaaiha ila yaumina haza”
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinƙai, godiya ta tabbata ga Sarkin Sarakuna. Mun faɗa, Amma Allah ne mafi sani. Tabbas, wannan ne tarihin wannan shahararren birni Mai suna Katsina tun daga kafuwarsa kawo yanzu.
Wasu masanan tarihin sun ruwaito cewa tsohon birnin ya gabaci Adaamus (an ce wani shahararren Sarki ne da aka taɓa yi a Ƙasar Hausa) da shekaru 4. Sannan masanan sun tafi a kan cewa BAGANI JARGO wanda ya Gina ganuwar birnin ya sarauci Katsina tare da zuriyarsa har tsawon shekaru dubu uku da hamsin kafin zuwan SANAWU (Wanda a zamaninsa Musulunci ya shigo Katsina) wanda ya ɗauki gabarar sarautar birnin.
To Amma, Sanawu, da Bagawu da Katsina, sun kasance shahararrun ‘ya’yan Bawo ne, Kuma sun wanzu a mulkin Katsina na tsawon lokaci. Sun yi mulki na tsawon shekaru ɗari Tara. Daga nan sai MUHAMMADU JANHAZO, da shi da zuriyarsa sun shimfiɗa mulki na tsawon shekaru ɗari biyu da ashirin.
Har ila yau, an ruwaito cewa TSAGA RANA ya shafe shekaru hamsin da bakwai (Masani Dr Yusufu Bala Usman ya ambace shi a matsayin Sarki na bakwai, ya yi sarauta a wuraren 1767-68). Sa’annan ya bai wa babban ɗansa mulki, sunan sa WARI MAI-KYERAAYI, wanda ya shafe shekaru goma Sha uku Yana sarauta (ya mulki Katsina daga 1649-1660.
(A zamanin mulkinsa ne ya yaƙi Kano, Abdullahi yana sarautarta. An ce sai da ya taɓa rarakar Kanawa har sai da ya tuƙe da su zuwa ƙofar Kansakali ta birnin Kano sannan ya juyo). Sannan ya miƙa mulki ga GIMA da ga Daƙaasariy, shi ma ya shafe shekaru talatin da biyar yana sarauta, daga Nan sai AGWARAGI ya karɓa wanda ya yi mulki tsawon shekaru arba’in da biyu.
(An ce shi ne Sarkin Katsina na takwas, ya yi mulki a wajajen 1778-96. Tarihi ya KIYAYE cewa Agwaragi shahararren Sarki ne, a zamanin sa ne Katsina ta kwaci wata takobi daga hannun Sarkin Gobir a zamanin da ake karin battar yaƙi tsakanin Katsina da Gobir ɗin, sunan takobin Bee-bee.
Har yanzu, nasarar Katsinawa a kan Gobirawa na ɗaya daga ababen alfaharin Katsinawa; a duba KATSINA: a historical document wanda Centre Regional de Documentation Pour la Tradition Orale Niamey ta wallafa a 1970.)
Daga shi sai GWOZO, maruwaitan tarihi sun ce ya shafe shekaru talatin da bakwai yana sarauta. Sauran shekaru sha ukun da suka rage, sarakuna irinsu MUHAMMADU AL-ZAAHID wanda bai jima kan sarautar ba, har manya nesanta kansa daga abubuwan duniya har ma daga ƙarshe ya yanke shawarar yin murabus daga sarauta, wataƙila shi ne silar laƙaba masa suna Al-Zaahid (Mai gudun duniya).
Akwai da yawansu waɗanda muka manta sunayensu tare da lokutan da suka yi mulki kafin tukewarsu zuwa ga Mallam Umar (Ummarun Dallaje Wanda ya kafa tutar Shehu Usmanu a Katsina, kuma wanda aka wallafa littafin a zamanin sa 1807-1835). Ƙarshe! (Godiya ga SALISU BALA Wanda ya alkinta mana shi)
Asalin Sunan Katsina
Labari mafi inganci shi ne, sunan tsohon birnin Katsina ‘DURƁI TA KUSHEYI’. Sunan mutanenta Durɓawa. Wasu na cewa asalin Durɓawa maguzawa ne tsatson mutanen NOK da Kwatarkwashi duba da kaburburansu da aka samo masu tsayi kamar falwaya, amma waɗansu na cewa asalinsu Mallawa ne daga Mali suke.
Da akwai mabambantan ra’ayoyi dangane da ASALIN inda aka samo Sunan KATSINA
1. Ra’ayi na farko na cewa, an samo sunan ne a zamanin Sarki MUHAMMADU Korao, a lokacin da ya sanya wani makusancinsa mai suna Katsina ya ringa duba yadda ake gina ganuwar birnin a madadinsa.
2. Ra’ayi na biyu: Aka ce sunan Katsina ya samo asali ne daga sunan wata mace mai suna matar sarki mai suna KATSI wadda ta fito daga Durbawa, mazaunan birnin na farko. An ce ta bar tsohon garin Katsina ne zuwa inda sabon birnin yake, a lokacin yana matsayin ƙaramin ƙauye, ba tare da an sani ba, da aka bazama nemanta sai aka riske ta, shi ne mazaunan garin suke cewa ‘Ai KATSI NA NAN’.
3. Ra’ayi na uku na cewa sunan Katsina ya samo ne daga wani Sarki da aka taɓa yi mai suna Katsina Ɗan Bawo. Amma marubuci Tijjani Lawal Ingawa yace Sarki Katsina ɗan Kumayo ne a wani rubutunsa.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Danna nan don karanta Yadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka
Edita@rumasau-kallamu










