Bahaushe shi ne mutumin qabilar Hausawa masu magana da harshen Hausa. Hausa harshe ce da take cikin rukunin harsunan yankin tafkin Chadi (Chadic) masu rassa daga ‘Afroasiatic’ da suka haxa da Larabci, Yahudanci da Buzanci, Habashanci, Somali da Kanuri (Encarta, 2009 & Greenberg, 1963).
A halitta Bahaushe baqar fata ne, da yake zaune a yankin Sahara, shi ya sa ake qiran yankin da Bilal Sudan (qasar baqaqen fata, ko Negro a Turance). Sai dai ana samu farare a cikin Hausawa jefi-jefi saboda auratayya tsakanin wasu qabilun Fulani, Shuwa da Auzunawa waxanda suke farare a halitta (Malumfashi, 2018).
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
Qasar Hausa, ita ce muhalli da Hausa ke rayuwa. Saboda da qaura, ba za a iya iyakance qasar Hausa ba a yanzu (Alhassan, 1982). Yankin da Bahaushe ke rayuwa na asali, shi ne yankin da ke tsakanin layi na 15N zuwa na 18N (Arewa da Ikwaita), da kuma tsakanin layi na 8E da na 12E gabas da ayin Girinwic. Wannan yankin na tsakanin Asodu ta qasar Agadas ta Nijar, kudu da qasar Sudan daga Arewa. Daga gabas yankin ya yi iyaka da tsohuwar Daular Borno, yamma da tafkin Chadi, daga yamma qasar Benin da gavar kogin Kwara, daga kudu kuma qasar Gwari (Kwalli, 1996 & Adamu, 1997).
Sanin haqiqanin asalin Bahaushe yana da givi sosai, saboda abin da aka fi labartawa na tarihin Bahaushe ‘tarihihi’2ya fi ‘tarihi’ yawa a ciki, kasancewar an sami lokaci mai tsayi, ba tare da sahihin tarihin a rubuce ba, saidai labarin baka na kunne-ya-girmi-kaka. Bahaushe mutum ne, mai tsatso tun daga kakanmu Annabi Adamu السالم عليه. Asalin Bahaushe a Afrika ya fara tun shekaru 30,000 zuwa 2 Tarihihi shi ne tarihi yake a jirkice, gurvatacce da har ba a iya gaskiya daqare-qare a cikinsa (Yahaya da wasu, 1992).
60,000 baya da wasu mutane suka yada zango a Nahiyar Afrika daga cikin qabilun Ham ta Kibxawa, Sudaniyawa da Babas (Malumfashi, 2018).
Dr. Yusuf Maitama (1929 – 2017) ya ce, ‚asalin Bahaushe mutumin qasar Habasha ne (Ethiopia, Afrika ta Arewa maso gabas). Daga kalmar Habasha, aka samu ‘Habsha’ zuwa ‘Hausa’.‛ Asalin mutanen Habasha su kuma, sun taso ne daga Asiya, daga cikin qabilun Labarawa da Kivxawa. Bahaushe ya taso daga Habasha ya nufo Afrika ta yamma.
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Bahaushe ya fara kafa gari daga yada zango domin kiwo, farauta, fatauci, zuwa gina gidajen noma, har ya fara samar da qauyuka, da unguwanni, zuwa birane, har aka kafa masarautu da faxaxa qasa (Gusau, 2008).
A wata ruwayar, a qarnin baya an yi wasu yankuna cikin daular Songhai ta Mali da ake qira da Guber ko Gobir3da Ausa. Wasu na ganin, ta iyu daga kalmar Ausa aka sami (H)ausa (Malumfashi, 2018).