Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu

0
91
  • Zubar jini daga mara.
  •  Cizon harshe da yawan mika.
  •  Ciwon kai da rashin gani ko gani dishi dishi.
  •  Zazzabi da ciwon jiki.
  •  Ciwon ciki
  •  Karanci ko yawan numfashi.
  •  Yawan ciwo.
  • Kumburin kafa,yatsu,da kuma fuska.

Idan mace taga alamomin tsorota (alamomi masu hatsari  to tayi gaggawar zuwa asibiti koda lokocin awun ta baiyi ba.

Wadan Su Abubuwa Da Mai Juna Biyu Za Ta Kiyaye

{1} Ya kamata mai juna biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya,ana so mai juna biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.

{2} Ya kamata mai juna biyu ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar ƙwaƙwalwa, wanda gajiyar ƙwaƙwalwa na haifar da gajiyar jiki,yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba ta da lafiya (queasy ko nausea).

{3} Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa,sannan ta rika motsa jiki a hankali.

{4} A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida.,yakamata mai juna biyu ta guji:

  • Kusantar sinadarai masu cutarwa.
  • Daukar lokaci wajen aiki.
  • Dadewa a tsaye.
  • Daga abu mai nauyi.
  • Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.
  • Zama a wurin da akwai injina masu kara.
  • Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa,ya kamata mai juna biyu ta guji shan ruwa mai sanyi,ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon lokaci.
  • Zama a muhallin da ke da tsananin zafi.

Domin karanta Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa Danna nan

labarin da ya wuceKo Kunsan Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa
Labarin na GabaCiwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo