Adabin Kasuwa Na Onitsha A Nijeriya

0
21

Kamar yadda wannan fasali na adabin kasuwa ya samu karɓuwa da watsuwa a sassan Turai da Amurka da ƙasashen Larabawa, haka ma inda Turawan suka yi mulkin mallaka fasalin ya samu zaunuwa, ko dai a cikin harshen ‘yan gida ko kuma cikin harshen baƙin da suka zo cikin Afirkawa.

Misalin da za a iya kawowa a nan shi ne na Adabin Kasuwar Onitsha da ya wanzu cikin harshen Ingilishi, masana da dama sun bayyana yadda wannan fasali ya samu ya kuma wanzu. Haka kuma kamar yadda Okoro (2002) ya bayyana, adabin Kasuwar Onisha an yi shi ne a wani zamani a farkon ƙarni na 20 a ƙasar Inyamurai a Nijeriya da ya kasance, wanda a lokacin an sami al’ummar Igbo da ba su da isasshen ilmin boko.

Wasu sun kammala Elementare, suka sami aikin malanta ko suka zama masinjoji ko sakatarori a ofisoshin gwamnati a Onitsha, sai dai da yawa daga cikinsu sun fahimci cewa ba za su iya rayuwa da irin wannan aiki ba, domin ba albashin ƙwarai, wasu kuma da ba su sami aikin ba, bayan sun kammala karatu, sai abubuwa suka cunkushe musu, domin waɗanda suka yi karatun ma ya suka ƙare, su kuma masu aikin suna aiki, ga shi ƙaro karatun na da matsala a wannan lokaci.

Wannan ya sa wasu da dama suka fantsama cikin kasuwar Onisha ko dai a matsayin ‘yan tireda ko masu koyon sana’ar hannu ta kafinta ko teloli ko magina ko maƙera. Da yake yawancinsu, sun yi boko to ba su son su zauna haka nan ba abin karatu, ga shi kuma ayyukan adabin Ingilishi da ke makarantu ya fi ƙarfin aljihunsu, sai suka shiga rubuta abin da ya zo ga ransu domin su karanta tsakaninsu; ire-iren waɗannan rubuce-rubuce ne aka kira da Adabin Kasuwar Onitsha.

Ke nan, kamar yadda Obiechina (1973) da Okoro (2002) da Malumfashi (2005) suka yi bayani daga nasu binciken ba wani abu ba ne Adabin Kasuwar Onitsha sai ƙananan littatafan nan da aka samu da yawan gaske a kasuwar ta Onitsha da wasu sassa na Kudancin Nijeriya a tsakiyar shekarun ƙarni na 20, suka ce, an tsara da shirya da kuma sayar da su domin talakawan Onisha da ba su yi zurfin karatu ba.

Wannan adabin na Kasuwar Onitsha, wanda shi ne za a iya kira da wanda ya fara samar da wurin buga litattafai, garin Onitsha dai yana kudancin Nijeriya, mutanen wurin waɗanda Igbo ne sun shahara wurin kasuwanci, a wani lokaci ma ana iya cewa kasuwar ta Onitsha ita ce mafi shahara a Afirka.

An fara samar da littafin adabi a wannan wuri cikin shekarar 1947, babu wani tsari ko fasali da aka bi domin samar da waɗannan litattafan, hasali ma dai an fara samar da su ne domin cike wani giɓi da aka samu na karatu da ko rubutu, saboda a lokacin samuwar addinin kirista da `yan mulkin mallaka sun taimaka wurin samar da makaranta a garin Onitsha domin su yi aiki, ko kasuwanci ko kuma su samu wata damar ta ci gaba.

Wannan shi ya haifar da masu buga litattafai na bakin hanya ko na kasuwa da suka fara samar da wannan adabi. Wanda za a fara cewa ya fara samar da waɗannan litattafan na kasuwar Onitsha ba wai kawai ya yi fice ba ne, a lokacin, mutum ne kuma wanda daga baya ya shahara ta fuskar ilimin boko, wanda kuma yana ma daga cikin waɗanda suka wakilci jama`arsu, kuma ƙwararre wurin haɗa magunguna (Pharmacist), wato Cyprian Ekwensi, wanda ya tashi daga wallafa littattafan adabin kasuwa ko yayi zuwa wallafa gangariyar adabi.

Littafin da aka fara samarwa a lokacin shi ne; Ikolo Wrestler na Cyprian Ekwensi, an samar da shi ne daga tatsuniyoyin Igbo, wanda aka buga a wurin sai da litattafai na Tabansi  Bookshop da kuma ɗayan, When Love Whispers na soyayya. An sake samar da wasu bayan shekara biyu wato; Tragic Niger Tales, mawallafin litattafan wani malamin makaranta ne, yana ba da labarin aure ne ko ma’aurata.

Su dai irin waɗannan litattafai da aka samar sun yi tashe da suna a duk faɗin garin Onitsha da kewaye, musamman a wurin matasa ‘yan makaranta, maza da mata. Wannan ya sanya wasu marubutan suka biyo baya, don ganin irin amsuwar da waɗannan litattafai suka yi.

Wannan kuma shi ya sanya aka shiga samar da sababbin masu buga litattafan na bakin hanya, da kuma na cikin kasuwa, shi ya sanya har zuwa shekarar 1960 abin ya haɓaka, wanda ya sanya masu buga litattafan suka watsu har zuwa garuruwan Aba da Fatakwal da Inugu da sauran manyan garuruwan gabashin Nijeriya.

Akwai dalilai da dama da suka sanya aka samu wannan bunƙasuwar a garin Onitsha kamar yadda Obiechina (1973) ya bayyana. Wasu daga cikin dalilan kuwa har da kasancewar kasuwar garin Onitsha ta yi fice ba a gabashin Nijeriya ko Najeriyar ba, kai har faɗin Yammacin Afirka.

Saboda haka idan aka lura za a ga cewa Adabin Kasuwar Onitsha ya kasance da siffofi da alamu da dama, waɗanda suka yi kama da waɗanda aka gani a ƙasar Ingila, ko a Jamus ko na ƙasar Larabawa, domin dai an yi shi ne saboda masu ƙaramin ƙarfi su samu abin karantawa, ke nan ba ya da tsada, sannan yana da saurin fahimta, ma`ana harshen da aka yi amfani da shi mai sauƙin fahimta ne, kuma an yi shi ne musamman saboda talakawa ko waɗanda ba su tare da gangariyar adabi.

Haka kuma ba su maganar komai sai labaran soyayya da tatsunniyoyi da rayuwar aure da kuma bunƙasuwar kasuwanci. Sai dai wannan bai zama abin mamaki ba, domin suna yin la’akari ne da buƙatun masu karatun su.

Matakan Gane Adabin Kasuwa

Abin lura a nan shi ne, irin wannan fasali da Adabin Kasuwar Onitsha ya ɗauka shi ne Adabin Elizabeth a Ingila ko kuma na Kitsch a Jamus, da na Larabawa ya ɗauka. Ke nan babban matsugunin kowane aikin adabi da aka yi wa laƙabi da na kasuwa ko na yayi bai wuce irin fasalin da ya tashi da shi ba, ko dai mai arha ne ko kayan da aka yi amfani da su wajen samar da shi ba su da inganci ko kuma masu yin sa da karanta shi wasu gungun jama’a ne, ba na kowa da kowa ba ne.

Gungun mutanen na iya kasancewa masu kuɗi ko talakawa ko iyayen gari, sannan uwa uba kuma wannan adabi na da lokacin da yake rayuwa, ya kuma mutu (Malumfashi,2005:8).

Domin gane wannan fasali na adabin kasuwa bari mu dubi adabin Elizabeth na Ingila da kyau, ya dai yi tashensa ne cikin shekara 45, wato daga 1558 zuwa 1603, shi kuma na Kitsch da ke a Jamus, ya rayu ne daga 1860 zuwa 1870, wato shekara 10 ya yi a duniya ko kuma na Onisha daga 1947 zuwa 1975, ya shekara 28 ke nan a raye.

Saboda haka, fasalin adabin kasuwa yana zuwa da siffofi da kamannu masu yawa. Sai dai domin taƙaitawa muna iya cewa shi ne adabin da ake samu a cikin kasuwa, ba wai ana nufin kasuwar dole ta kasance irin wadda muke tunani ba, duk inda jama’a suke hada-hadar saye da sayarwa, shi ake nufi da kasuwa a nan.

Idan ana son a gane shi da kyau sai a dube shi da waɗannan fasalce-fasalcen :

  • Adabin kasuwa zai iya kasancewa mai sauƙin karantawa, wato mai jimloli marasa sarƙaƙiya.
  • Haka kuma nahawunsa zai kasance sassauƙa, ba mai nauyi ba.
  • Haka yawancin wannan adabin yakan kasance bai da yawan shafuka, ma`ana, bai ɗaukar lokaci za a iya karance shi.
  • Ga shi kuma yana da arha, kusan kowa zai iya sanya kuɗi ya saya ba tare da wani tarnaƙi ba (Obiechina, 1973:12).

Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

Danna nan dan karanta Adabin Kasuwar Kitsch A Jamus 

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAdabin Kasuwar Kitsch A Jamus
Labarin na GabaJigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.