Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

0
39

A wannan babin an yi ƙoƙarin bin yadda aka samar da adabin kasuwa a ƙasar Hausa. Abin nufi, bayan ganin yadda fasalin adabin kasuwa ya kasance a sassan duniya daban-daban, da kuma ganin irin yadda ya samu ga maƙwabtanmu, Inyamurai, sai kuma mu gangaro domin ganin yadda ya samu a ƙasar Hausa.

Don haka, a wannan babin an dubi irin zangunan da Adabin Kasuwar Kano ya shiga a ƙasar Hausa, da kuma irin rawar da ya taka wajen ginuwar wani ɓangare na ƙagaggun labaran Hausa.

Samuwar Adabin Kasuwar Kano

Daga abubuwan da aka gani a babin da ya gabata ke nan ba abin mamaki ba ne idan aka ci karo da Adabin Kasuwa a Amurka ko Turai ko Rasha ko cikin ƙasashen Asiya ko Larabawa, kai ko ma ina ne a cikin duniya.

Hakan na faruwa ne ganin cewa ai ba ƙasashen Turawa ko waɗanda suka ci gaba ne ke da damar su samar da adabin kasuwa su kaɗai ba, haka kuma ba dole sai harshen Ingilishi ko wani harshen da ya sami ci gaba kaɗai ne zai iya samar da shi ba; kowace ƙasa, kuma kowane irin harshe zai iya samun adabin kasuwa a cikin wani zangon rayuwar adabin. Domin inganta bincike, ya dace mu bi salsala, mu ga yadda aka samar da abin da yawanci ake kira Adabin Kasuwar Kano tsakanin Hausawa.

Rayuwar Farko : 1984-1989

Abin da aka daɗe ana kira Adabin Kasuwar Kano ya samo asali ne a farkon shekarun 1980, kuma wannan shekaru a ƙasar Hausa ko Arewacin Nijeriya baki ɗaya, shekaru ne masu tarihi a ɓangaren samuwar ilmin boko da rubutu.

A daidai wannan zangon rayuwa ne ɗaliban UPE, shirin gwamnatin tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da rububin abubuwan karantawa, domin ɗaliban farko na wannan shiri sun baro firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye ɗalibai har kashi huɗu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke buƙatar abin karantawa.

Haka wannan zango ya zo daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da ɗab’i a ƙasar Hausa wato NNPC ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durƙushewa. A daidai wannan lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishaɗi, bayan kuma ga dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da  shauƙin irin waɗannan littattafai da babu su.

Wannan shiri na UPE, duk da cewa bai zaunu da gindinsa ba, amma ya samar da sababbin makaranta a farkon shekarun 1980. Kuma a daidai wannan lokaci sai ga shi tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙara inganta, saboda gano man fetur da aka yi, ya ƙara wa ƙasar hanyar samun kuɗaɗen shiga masu yawa.

Bincike kuma ya nuna cewa duk lokacin da irin wannan harka ta kasance haka, wato ga masu ilmi gwargwado, sa’annan ga ‘yan kuɗi a hannun jama’a, kamar yadda muka gani a fasalin Adabin Kasuwar Kitsch na Jamus, sai ka ga hanyoyin samar da adabi, mai kyau ko maras kyau, suna wadatuwa.

Da yake tun can azal akwai kayayyakin rubutu da ɗab’i gwargwado a ƙasar Hausa, sai ya ba matasa damar da suka tsunduma cikin wannan harka ta wallafa littattafai ba ji ba gani, kamar yadda Furniss (2001) ya yi nuni. Sai dai ko kafin shekarar 1984 da littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed ya fito kasuwa akwai ɓirɓishin rubuce-rubuce na soyayya a ƙasar Hausa.

Idan ba a manta ba a shekarar 1978 kamfanin NNPC ya shirya gasa da ta samar da littattafai a shekarar 1980, kamar su Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina da So Aljannar Duniya na Hafsat Abdulwaheed da kuma Amadi na Malam Amah na Magaji Ɗambatta, (Haruna, 2009).

Sai dai abin lura shi ne waɗannan littatafai daga gasa suka fito, wato sai da aka yi shiri da tsari, haka kuma na hukuma ko kamfani ne, don haka sun biyo tsari da ingancin da ya bambanta su da adabin kasuwa. Ke nan za a iya cewa waɗannan littatafai na gasar 1978 sun dai nuna hanya ne na irin adabin da zai iya biyo bayansu, ba su ne farkon adabin na kasuwa a ƙasar Hausa ba.

A ɗaya ɓangaren kuma an danganta littafin Rabin Raina na Talatu Wada Ahmed da tushe ko tubalin samuwar adabin kasuwa a ƙasar Hausa saboda yanayin da ya samu da kuma yadda ya shiga kasuwa. Shi ma ba wai zama aka yi domin assasa wannan fage na adabin kasuwa ba tattare da shi ba.

Kamar yadda a karo na farko wadda aka danganta aikinta da Adabin Kasuwar Kano, Talatu ta bayyana wa Mujallar Garkuwa (2000) yadda ta samar da littafin, ta ce ita ba ta san da wani abu wai shi adabin kasuwa ba lokacin da take rubuta littafinta. Ta ƙara da cewa ta dai rubuta shi ne a lokacin tana makarantar WTC Katsina, tana aji uku, wato wajajen shekarar 1980.

Ta kuma rubuta shi ne daga gyauron labaran da take ba ‘yan uwanta ɗalibai lokacin suna makaranta can da dare kafin su yi barci. Bayan ta gama sakandire ne ta fitar da shi ta hanyar aika shi gidan rediyon tarayya Kaduna domin a karanta a shirin Shafa Labari Shuni, amma aka daɗe ba a karanta shi ba, daga baya ta miƙa wa wani kamfanin bakin hanya da ake kira Ogwu a Kaduna domin ya buga mata shi.

Kamfanin Ogwu ya buga, ya kuma shiga sayar da littafin da ya ga mutane sun dami suna son su karanta. A lokacin da Kamfanin Ogwu ya shiga sayar da littafin, ita Talatu tana Kwalejin Ilmi ta Kafanchan wajen ƙaro ilmi, a can ne wata ƙawarta ta zo da littafin, tana yi mata bayanin yadda littafin ya yi kasuwa, ita ba ta ma sani ba. Wannan daɗin abin da ya faru ya sa ta koma gida ta ji abin da ya auku.

Mahaifiyar Talatu ta ba ta kuɗin da aka samu, ta yi murna ƙwarai da ganin arzikin da wannan littafi ya jawo mata. Daga wannan lokaci ne ta shiga sake buga littafin, ana watsawa a cikin ƙasar Hausa, ta yadda abin ya dinga ba ta mamaki na ganin cewa mutane, musamman masu sayar da littatafai daga ko ina a faɗin ƙasar Hausa ke kira ko yo saƙon don Allah ta aika masu da kwafe 500 ko dubu ko dubu biyu ko ma fiye.

Fitar wannan littafi da yanayin da ya samu kan sa lokacin bugu da sayarwa da kuma hanyoyin da aka bi aka samar da shi ya nuna wa sauran marubuta cewa ashe akwai wata hanyar rubutu da wallafa littattafai ba dole sai ta bin kamfanonin bugu da wallafa na gwamnati ba.

Saboda haka daga samuwar wannan littafi na Rabin Raina a shekarar 1984 za mu iya cewa akalar adabin hira ko ƙagaggen labari ta soma sauyawa, kuma a iya cewa daga wannan lokacin ne Adabin Kasuwar Kano ya fara ginuwa. Sai dai abin da ke da muhimmanci a nan shi ne ba wai zama aka yi ba domin a tsara da gina wannan fasali na Adabin Kasuwar ta Kano ba, abu ne da ya kasance caccakuɗe, kuma tattare da abubuwa mabambanta da suka haɗa da :

  • Tun da farko dai akwai matsalar abubuwan karantawa a makarantu da kuma tsakanin sababbin makaranta kamar yadda muka yi bayani.
  • Ga halin da kamfanin NNPC ya shiga daga farkon shekarun 1980 da rashin buga littatafan hira.
  • Ga kuma ɗaruruwan ‘yan makaranta da waɗanda suka kammala makarantun, sun kuma rubuta littattafai masu yawa, ba wurin buga su, balle a san da su.
  • Shirin gidan Rediyon Tarayya Kaduna na Shafa Labari Shuni da wasu da dama a gidajen rediyon jihar Kano da Katsina da Sokoto da wasu wurare da dama ya taimaka wajen fito da waɗansu daga cikin marubutan da ke ɓoye.
  • Bugun littafin Talatu na bakin kasuwa da yadda ya sami karɓuwa ya sanya wasu, ƙila suka ce su ma bari su gwada bugawa da sayarwa.

Saboda haka littattafan da ake ta yayatawa a halin yanzu a matsayin waɗanda suka biyo bayan littafin Talatu daga 1984, ba wai shawara suka yi da juna ba, kuma ba su san wani na yin irin wannan aiki ba, kamar yadda bincike ya nuna a halin yanzu. Ke nan jawabin da Malumfashi, (1994) ko wanda Adamu, (1996) da Adamu (2000) suka yi na lissafa littatafan da suka biyo na Talatu kamar haka ba daidai ba ne, sai dai daga littafin Talatu na Rabin Raina sai:

  • Ibrahim Hamza Abdullahi da Soyayya Gamon Jini a 1986.
  • Idris S. Imam da In Da Rai a 1987.
  • Balaraba Ramat da Budurwar Zuciya a 1987.
  • A.M Zaharadden da Kogin Soyayya a 1988.
  • Idan so cuta ne, na Yusuf M. Adamu a 1989.

An yi wannan hasashe bisa hujjar da ta nuna cewa babu wani bincike da ya tabbatar da jeruwa da daidaituwar wannan tsari ko kuma wani bayani da ya ce an tattauna tsakanin waɗannan mutane na biyo sahun Talatu Wada.

Bari mu yi nazarin batun da kyau, tun da farko dai garuruwan marubutan daban-daban suke, Talatu na Kaduna, Ibrahim Hamza na Kano, Idris S. Imam kuwa tun 1984 aka buga littafin nasa ba wai a 1987, Balaraba kuwa ko kafin ta shigar da littafinta na Budurwar Zuciya a layin adabin kasuwa ta fuskar shiga ƙungiyar Raina Kama, an riga an buga littafin a Zaria,(Gaskiya Corporation a 1984).

Haka shi ma Zaharradeen a Kano yake, shi kuwa Yusuf Adamu yana ɗalibta a Sakkwato ne ya shigo da nasa littafin. Haka kuma daga binciken da aka gudanar an fahimci cewa ko kafin Ibrahim Hamza Abdullahi da littafinsa na Soyayya Gamon Jini a 1986, an samar da Hannunka Mai Sanda I na Ƙamarradeeen Imam a 1985, me ya sa ba a shigar da shi cikin layin na farko ba? Haka kuma a tsakanin 1984 da aka samar da littafin Talatu, ba wai littattafai huɗu ne kurum suka yi tashe ba, guda 13 ne.

Ke nan ba wata ƙungiya ba ce ko kuma wani taro aka yi ba aka ce a samar da wannan abu da aka kira Adabin Kasuwar Kano daga baya. Shi kuma Malumfashi (1994) da ya kira shi da wannan suna, ya yi haka ne daga abin da ya gani masu kama da juna tsakanin littattafan da irin waɗanda aka samar a Onisha kamar yadda ya bayyana daga baya, (Malumfashi, 2004).

Kamar yadda muka gani can baya, rayuwar adabi takan shiga cikin wani sauyi ne na wani lokaci, daga baya kuma ta kasance cikin wani tsari na daban, irin wannan shi ne ya faru da abin da aka kira Adabin Kasuwar Kano yanzu. Sai dai wani abu da za a yi la’akari da shi, shi ne, yawancin matasan da suka yi tashe a wancan lokaci a wannan fage ba su yi amfani da kamfanonin ɗab`i da ake da su don bayyanar da ayyukansu na adabi ga jama’a ba, ba don komi ba kuwa sai don ba wani kamfani da ya damu ya buga ire-iren waɗannan littattafai.

Ba kuma wai don ba su da kasuwa ko kuma ba su sami karɓuwa ba a tsakanin al`umma ba, a a, a tsakanin shekarun 1978-1982 ba abin da ya fi tashe da karɓuwa irin labaran da wasu suke rubutawa, suna aika wa gidajen rediyoyi daban-daban ana karantawa. Ba wani abu ya jawo hakan ba sai ganin litattafan da aka samar daga gasar da aka shirya a 1978 da suka samar da litattafan soyayya na farko da za a iya kira `yan zamani, sun yi tasiri ga rayuwar irin waɗannan matasa.

Sai dai da alama amfani da aka yi da kafar rediyo, wadda ta sanya ƙagaggun labarai irin waɗannan suka sami martaba, ba wai kawai tsakanin waɗanda suka yi boko ba kurum, har ga waɗanda aikinsu shi ne sauraron rediyo, ba su iya karatun ba.

Bisa wannan tafarkin aka shiga samar da sababbin marubuta, wasu ta hanyar kwaikwayon abin da aka rubuta, suka aika gidajen rediyoyin, wasu kuma ta sake wa tatsunniyoyi da labaran Hausa fasali, wasu ko ta kwaikwayo ko ɗaukar fasalin wasu labaran Ingilishi ko fassara kai-tsaye ko kuma naɗe fina-finan Indiya da na Turawa zuwa takarda.

Cikin ɗan lokaci ƙanƙani sai ga kabod-kabod na gidajen rediyoyin nan sun cika maƙil, wasu ma suka shiga ƙonawa, wanda ya sa masu rubutun suka shiga guna-guni idan ba a karanta nasu labaran ba. Sai dai kuma waɗanda Allah ya tarfa wa garinsu nono daga cikin waɗanda aka karanta nasu a gidajen rediyoyin, sai ga shi sun fara samun suna da ɗaukaka.

Wannan ya jawo wasiƙu suka shiga gilmawa zuwa gare su, ana yaba masu, ta haka kuma aka ga cewa ga wata kafa ta samu ta kashe waccan ƙishirwa ta rashin labaran Hausa da ta addabi matasa, ta yadda a tsakanin shekarar 1984 zuwa 1998 marubuta da sababbin littatafai suka baje kasuwarsu a ƙasar Hausa.

Idan aka yi nazari sosai za a ga ko da Talatu ta bayyana a 1984 a Kaduna, ba a Kadunar ta tsaya ba, domin littattafan sun baje duk faɗin ƙasar Hausa, musamman a Kano da suka dasa rayuwarsu. A Kanon akwai irin littafin Talatu Wada da ya riga ya shiga kasuwa shi ma kafin ma bayyanar na Talatu, wato Wasiyar Baba Kere na Ibrahim Sale Gumel, a kuma wannan shekara ta 1984, an sami ɗan uwan na Talatu, wato In Da Rai Da Rabo na Idris S. Imam.

Saboda haka ko da Ƙamarradeen ya shigo da nasa littafin a 1985, ba dole ba ne ya san da abin da Talatu ta yi ko kuma sauran da suka riga nata shiga kasuwa; musamman ganin cewa ɗa ne ga marigayi Abubakar Imam, kuma yana aiki da kamfanin Huda-Huda da ke Zaria, waɗanda su ne mawallafansa.

Yadda Kano ta shigo cikin harkar da litatattafan da ‘yan Kanon suka samar bai rasa nasaba da suna da tashe da littafin Talatu da na Idris da Ibrahim suka yi a kasuwar Kanon. Littattafai goma sha uku ne suka wanzu a wannan lokaci a tsakanin 1986 zuwa 1989. Ga alama kuma su ne suka sanya Kano ta sami karɓuwa da tagomashi a wannan harka ta yadda daga baya Gusau ta shigo sahu, Kanon ta sake bayyana daga can kuma sai Sakkwato tare da Yusuf Adamu.

Ga jerin waɗannan littattafai da suka kasance na farko ko suka kasance jijiyar da ta gina wannan sabon yanayin rubutu na Adabin Kasuwar Kano. Daga marubuta waɗannan littattafai an fahimci marubuta mata guda biyu suka wanzu, sauran kuma duk maza ne.

LAMBA LITTAFI MAWALLAFI SHEKARA
1 Wasiyyar Baba Kere Ibrahim Saleh Gumel 1983
2 In Da Rai da Rabo Idris S. Imam 1984
3 Rabin Raina Talatu Wada Ahmed 1984
4 Hannunka Mai Sanda 1 Ƙamaruddeen Imam 1985
5 Soyayya Gamon jini Ibrahim Hamza Bici 1986
6 Daji Bakwai Abba Ado Ɗandago 1987
7 In Da Rai… Idris S. Imam 1987
8 Kogin Soyayya Ahmed Mahmoud Zaharaddeen 1988
9 Turmi Sha Daka Kabiru Ibrahim Yakasai 1988
10 Budurwar Zuciya Balaraba Ramat Yakubu 1989
11 Soyayya Danƙon Zumunci Bashir Sanda Gusau 1989
12 Tsalle Ɗaya… Idris S. Imam 1989
13 Idan So Cuta Ne Yusuf M. Adamu 1989

Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

Danna nan don karanta Jigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceJigogin Adabin Kasuwannin Ƙasashe
Labarin na GabaKarin Lafazi (ACCENT)
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.