Abin Da Zai Faru Gobe

0
35

Ban san gaibu ba, amma tabbas na san abin da zai faru da ni gobe, domin kuwa yau ɗina yayar gobe ce tunda ni ne a yau ɗin kuma ni ne zan je goben.

In ban canza a yanda nake ba yau to gobe ma haka zan kasance, domin babban dalilin da ya sa aka samar da Yau da Gobe shi ne canjawar aiki da matsaya, lokaci da matafiya, dan gujewa kwan-gaba kwan-baya.

Idan ba a buƙatar a canja to babu hikimar saka lokaci, na sallah ne ko kwa na cin abinci, to bare a gane lokacin zuwa Masallaci ko kuma Coci.

Idan ba ka canza daga yanda kake ba har gobe ta yi to malam har yanzu a jiya kake, kasancewar ka a yau shi ne canjawar aikinka, ɗabi’arka, mahangarka da yanda kake tunaninka.

Dan haka akwai buƙatar in gobe ta yi na ji a jikina na shiga gobe, in kuwa ta wuce to cikin biyu ɗaya nake yi. Ko dai na bar jiya a taho da ni yau ko kuma na tsaya a jiya kafin na ƙaraso, wanda kuma bai cika yiyuwa ba, abin da ya fi kawai shi ne na dage na kyautata abubuwan da nake yi yau na kuma gama da su ba tare da na bar kwantai ba.

Sabo da haka kar ka yaudari kanka da cewa gobe ta Allah ce, domin ba a taɓa samun jahili a yarinta kuma ya zama malami sanda ya girma ba, musammam a ce bai canja jiyansa da yau ɗinsa ba.

Yanzu tunda kake ka taɓa ganin yaran banza bai zama babban banza ba? Ko ka taɓa ganin mummunar yau, ba ta haifar da wulaƙantacciyar gobe ba?

Abban Marke

Don karanta waƙar Yaushe Tura Za Ta Kai Bango danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceMe Za Ka Yi Idan Ka Ga Ɗan Uwanka Zai Mutu?
Labarin na GabaAlamomin Shigar So 1