Ita dai layya sunna ce wajiba a kan wanda yake da ikon yin ta. Sannan mafi ƙarancin abin da yake wadatarwa a layya awaki da tumaki shi ne; Wanda suka kai wata takwas kamar yadda ya zo a littafin Risala. Amma da akwai saɓani a kan haka.
Sannan abin da yake wadatarwa daga shanu shi ne; su cika shekara Uku (3) cif suka shiga ta Huɗu (4). Ɓangaren raƙumi kuma ya kasance sun cika shekara Biyar (5) sun shiga ta shida. Ana son mutum ya yanka Layyarsa (ɓangaren Awaki, Tumaki da Shanu) ko ya soke abin layyarsa (Ɓangaren Raƙuma) da hannunsa bayan Limamin garinsu ya yanka layyarsa.
Duk wanda ya riga limamin garinsu yanka ko soke layyarsa, to ya sake layyarsa. Sannan ga mutanen da ba su da idi a garinsu sai su jira dai-dai lokacin da limamin Gari mafi kusa da su zai yanka layyarsa. Bayan haka mai layya zai ci daga cikin naman ya kyautar da wani abu daga ciki ga waɗanda ba su yi lalyya ba sannan ya sadakar da wani ɓangare. Allah SWT yace: “Kuci daga ciki sannan ku bada ragowar ga Fakirai”
Suratul Hajj (28).
SIFFAR YANKA
Ana son idan lokacin yanka ya yi, sai mutum ya kamo dabbar layyarsa, ya kawo ta wajen yankawa sannan ya fuskantar da ita Alƙibla, kai ya kasance a gefen hagu, sannan sauran jiki a gefen dama sannan ya ɗauko wuƙa mai kaifi (don sauwaƙewa ga dabbar), Yace:
Bismillahi, Allahu Akbar bayan jini ya zuba sai yace: Allahumma Haza minka wa Laka, Rabbana Takabbal minni (In shi kaɗai ne) minna (in shi da iyalansa ne)
Ma’ana: Da sunan Allah, Allah mai Girma. Bayan jini ya zuba sai yace: Ya Allah wannan dominka ne kuma naka ne, Ya Allah ka karba minni (in shi kadai ne) ka karba mana (in shi da iyalansa ne). Sannan sai ya yanka.
DABBOBIN DA BA SU WADATARWA A YANKA SU A LAYYA
1. Maras lafiya: Dabbar da rashin lafiyarta ya bayyana ba ta wadatarwa ga Layya.
2. Ramammiya: Dabbar da ta rame wanda babu nama a jikinta ba ta wadatarwa ga Layya.
3. Tsohuwa: Dabbar da ta gama tsufa ita ma ba ta wadatarwa ga Layya. Ma’ana wanda ba ta da ɓargo.
4. Mai Ido ɗaya: Dabba mai ido ɗaya ita ma ba ta wadatarwa ga Layya.
5. Gurguwa: Dabbar da take gurguwa ko kuma’ mai ɗingishi sosai (da ya bayyana ƙarara) ba ta wadatarwa ga Layya.
6. Mai gutsurarren ƙaho.
7. Mai yankakken ko tsagaggen kunnen da ya kai ɗaya bisa uku.
Don karanta Falalar Watan Dhul-Hajji danna nan
Edita@rumasau-kallamu