Za a iya gwajin ciki da na’ura a kowane lokaci na rana; amma dai da sassafe shi ne mafi dacewa. (fitsarin farko).
Ki yi fitsari a cikin roba ko kwano mai tsabta ko kofi ko duk abin da kike ganin fitsari zai iya zama a ciki.
- Sai ki yi fitsari a ciki, daidai gwargwado, wanda na’urar ba za ta lume duka a ciki ba
- Sai ki saka na’urar a cikin fitsarin; iya wajan tsinin ake so ya taɓa fitsarin.
Kar ki taɓa wajen nuna sakamakon ko wajan tsinin da hannunki
- Sai a tsaida na’urar a tsaye kada fitsarin ya wuce alamar (MAX)
- Sai ki bar shi ya ɗan jima a ciki kada ya yi ƙasa da sakon biyar (5)
- Bayan ya ɗan jima a ciki, sai ki ciro nau’rar daga cikin fitsarin.
- Sai ki sa na’urar ta kalli sama wajan ɓangaran da aka rubuta (MAX).
Idan ba za ki iya riƙe ta a hannu ba, za ki iya ajiye na’urar a waje mai tsafta domin jiran sakamako, ta yadda wajen alamar rubutun MAX din yana kallon sama.
Sakamako
- Idan ki ka ga layi mai launi wanda ya turu sosai guda biyu; to kina da ciki kamar yadda aka nuna a hoton nan.
- Idan kuma ki ka ga layuka guda biyu masu launi, amma ba turarru ba, kina da ciki.
- Idan kuma ki kaga layi ɗaya, to ba ki da ciki.
- Idan kuma ki ka ga layi ɗaya mai launi turarre ɗayan kuma ba turarre ba shi ma ba ki da ciki.
Karin bayani
- Yayin da ki ke jiran sakamako, za ki iya lura da layi mai launi yana motsawa a cikin wajen nuna sakamakon, wannan ba matsala.
- Kina buƙatar jira minti 10 don tabbatar da sakamakon.
- Ba a amfani da sakamakon da gwajin ya bayar bayan minti 30.
- Sakamako yakan iya canzawa ya danganta da irin na’urar da ki kai amfani da ita, amma wannan shi ne wanda aka fi amfani da shi.