Yadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take

0
20

Waɗannan ƙurajen da kan bayyana a fuskar manya da ƙananan yara wanda ake kira da “Molluscum Contagiosum” a kimiyyance, inda da Hausa akan kira su da DANYA, ƙuraje ne na larura da ƙwayar cutar Virus rukunin waɗanda ke sa cutar ƙyandar biri da cutar cin zanzana ke haddasawa, wato (monkey pox & small pox).

Abinda ke bambance su da sauran ƙuraje shi ne lotsewar da tsakiyar ƙurjin ko tsirorin ke da shi. Sannan wani lokacin bayyanar wannan ƙurajen da yawa a jika musamman ga manya wanda suka san suna ‘ƴan tsalle-tsalle tsakanin abubuwa, toh fa hakan ka iya zamowa alamar farko da ke nuna mutum na ɗauke da cutar ƙanjamau.

Kuma rashin zuwa a tantance shi ka iya sa su rikiɗe mutum ya yi karo da cutar cancer a fata wato “Kafosi sakoma” amma ga masu HIV/AIDS kurum. Shi yasa ko ba wannan ba, kar wanda yasan yana da HIV ya yi wasa da wani canji da zai gani a fatar sa. 

  • Ana iya ɗaukar su daga wani zuwa wani ta hanyar;
  • Musayar soson wanka da me su,
  • Ko taɓa ruwan ƙurjin a zo kuma a taɓa jiki ba tare da an wanke ba,
  • ko haɗa kayan sawa da me su,
  • ko kwanciya a gadon me shi,
  • ko tayar da kai da pillow ɗin da me su ke ta-da kai.

Da dai duk wata hanya da ake iya samun cuɗanya da fatar me ɗauke da su. Na san wasu ƙurajen kan ba su sha’awa musamman idan sun fito a saman fatar ido musamman Mata, toh amma fa wannan ba abin so ba ne. Galibin wanda za ka gani da su alama ce ta ba su da ingantacciyar garkuwar jiki (Good immunity). 

MAGANINSU SHI NE

  • A wasu wanda suke da garkuwar jiki me ƙarfi ko da sun kamu da su watanni 4 zuwa 6 a neme su a rasa ba tare da an yi maganin komai ba, a wasu kuma suna iya jimawa fiye da shekara ɗaya zuwa huɗu kafin su tafi.
  • A wasu kuma takan kai ga sai an ba su magungunan shafawa kafin su tafi.
  • A masu cuta me karya garkuwar jiki (HIV/AIDS) dole sai sun mayar da hankali a kan maganin su, ko kuwa in sabbin gano ciwon ne sai an ɗora su a kan magani akan iya warkar da ƙurajen danyar ko da kuwa an yi maganin danyar ba za ta tafi ba ba tare da maganin ƙanjamau ɗin ba.
  • A wanda al’amarin ya yi ƙamari sai an kai ga ciccire musu ita ta hanyar amfani da na’urar daskarar da su da sinadarin sanyi a reɗe su (cryotherapy), ko kuma na’urar ƙonewa tare da yankewa wato (electrocautery).
  • Galibi dai jinkirta magance su bai haddasa wata mummunar matsala, sai dai barinsu ba tare da ɗaukar mataki ba na iya sa su yi yawan da za su lulluɓe fuska ko su ɓata jiki baki ɗaya, kuma mutum ya zamto ya riƙa cutar da wasu musamman ƙananun yara da kan so hawan jikin mutane.
  • Hakanan kaucewa haɗa kayan sa wa, Gadon kwanciya, robar wanki ɗaya, runguma, musayar matashi da me su shi ma hanyar kare kai ne idan ana tare da me su.

Karanta Illolin Sinadaran Samun Ƙwazo Da Kuzari

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci
Labarin na GabaTarihin Garin Rimin Gado