Tarihin Garin Gurin Gawa

0
31

Kamar yadda marubutan littafin ‘Urban Society ‘ Gist da Halbert suka faɗa, kuma kamar yadda yake game da asalin ita kanta wayewar, tushen kowanne birni kusan ya samo asali ne daga hijirar mutanen ƙauyuka.

Birane su ne cibiyar hadar-hadar kasuwanci, tsaro, al’adu, ilimi da bincike. Don haka ya sanya mutanen karkara na kusa da na nesa, da ma wasu mutanen da ke wasu biranen da dama kan ziyarci birane domin samun mafakar tsaro, ko kasuwanci, ko samun ilimi ko cimma wani dalili na al’ada da ma sauran muradai walau ziyarar ta kasance ta wucin gadi ko kuma ta-din-din-din.

Akwai ilimin tarihi mai yawa da mukan rasa yayin kawar da kawunan mu ga tafarkan da suke sadar da mutane zuwa waɗancan birane. Wannan kuwa ya haɗar da tarihin wasu muhimman abubuwa da aka taɓa yi ko kuma muhimman wurare masu dangantaka da biranen kansu.

Sau tari a ƙasar Hausa mutane kan niƙi gari domin ziyartar wani birni amma sai su shantake a wasu wurare na kusa ko na nesa da biranen bisa wasu dalilai. Haka kuma a wasu lokutan, sauyawar yanayai kan tursasa mutanen cikin birane komawa makusanta ko manesantan garuruwa ko birane da zama.

Garin Gurin Gawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da suka kafu a turbar kano. Hasashe ya nuna cewar mabanbantan mutane da akasarin su ƴan tafarki ne suka kafa garin tsawon lokaci da ya shuɗe. Garin yana kudu da garin kano, akan turbar da za ta shigar da mutum birnin kano ta ƙofar Ɗan Agundi (wadda aka sara a wajajen shekarar 1499AD). Don haka duk mutanen da suke son shiga kano daga yankunan Rano, Jos, sassan ƙasar Bauchi da makamantan su sai sun bi ta wannan turba.

ASALIN SUNAN GURIN GAWA

Akwai mabanbantan zantuka game da asalin sunan Gurin Gawa.

1. Na ɗaya: Gurin Gawa daga Gurin Gawarwaki. An ce an samo sunan ne daga kasancewar wurin filin daga. Watau a zamanin yaƙi, da zarar kano ta samu labarin an tunkaro ta da yaƙi ta wannan shiyya, sai ta turo dakarunta ta jibge su a wannan wuri. Don haka a nan za a fafata yaƙi, anan kuma za a samu tulin gawarwaki bayan ƙarewar yaƙi.

2. Na biyu: Gurin Gawa daga ‘Gurin-Ge‘: Wannan ra’ayin yana cewa an samu sunan ne daga wani Bafillatani mai suna Gurin-ge, wanda kiwo ya biyo da shi ta wajen har kuma dabbobin sa suka gano masa wani kwarmin ruwa, don haka ya mayar da wajen mazaunin sa, daga bisani ƴanuwansa fulani suka riƙa riskar sa da zama.

3. Na uku: Gurin gawa daga Gurin da aka samu  gawar Kuyangar Sarkin Rano: An ce akwai wani rafi tsakanin Medile da Gurin Gawa wanda ake kira ‘Ci-kuyangi’, saboda yadda ya yi silar mutuwar kuyangi da dama a ciki har da wata amintacciyar kuyangar Sarkin Rano wadda ta rasu a wurin a kan hanyarta ta shiga Kano, an ce daga nan aka samo sunan na Gurin Gawa.

Zuwa yanzu, garin ya kasu kashi biyu, akwai Ruga inda fulani masu sarautar garin suke, da kuma ɓangaren Hausawa inda ake kira Dausayi. A nan ne mahaifiyar shahararren masani marigayi Sheikh Nasir Kabara ta ke.

TASIRIN SHAHARAR KANO GA SAURAN MAKUSANTAN GARURUWA

Kasancewar birnin Kano birnin kasuwanci ne ba birnin Siyasa ba, ya samu ɗaukaka tsawon lokaci saboda yadda fatake ke tururuwar zuwa gare shi bisa dalilan kasuwanci. Wannan ya taimakawa birnin wajen zamowa shahararre, shahararsa kuwa ta yi tasiri ga makusantan ƙauyuka wajen karɓar baƙi a ko-da-yaushe, da kuma hada-hadar kasuwanci.

Kamar yadda aka sani, a baya babu tsarikan otal ko masaukai a ƙasar Hausa, sannan akan rufe ƙofofin shiga birane idan dare ya yi. Saboda haka, matafiya a zamanin baya sukan samu waje da suka aminta da amincin sa su ya-da zango idan dare ya yi kafin su ƙarasa cikin birni. Don haka kafuwar ƙauyuka a kusa da birane kan zamo masaukai ga baƙin da suke haramar shiga kano yayin da dare ya yi musu.

A irin haka ne aka samu wani mutumi daga ƙasar Bade ta cikin jihar Yobe a yanzu haka ya ya-da zango a Gurin Gawa tare da soma sana’ar Kwarami (awo), inda ya samu shahara a wannan sana’ar, ya rinƙa sauƙaƙawa fatake masu zuwa kano da jakuna siyan hatsi da kuma masu fitowa daga Kano neman haja ba tare da sun yi dogon zango ba. (Har yanzu ana yi wa mazaunin wancan babarbare laƙabi da suna ‘Marken Bade’).

A ƙarshe, ina da ra’ayin cewar muhimmancin buƙatar bibiyar tarihin manyan tafarkan da suke sadarwa zuwa biranen mu tamkar na sanin tarihin biranen ne.

Karanta Yadda Aka Yi Bautar Kurmin Jakara A Kano

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaƙa Mai Taken Baƙar Sana’a
Labarin na GabaIllolin Sinadaran Samun Ƙwazo Da Kuzari
Sadiq Tukur Gwarzo
Sadiq Tukur Gwarzo marubuci ne mai binciken tarihi da son taskance ilimi da taimakon al'umma.