Kansa a cike yake saboda rashin bacci ga damuwa, don haka yana shiga office ɗin ya rufo ƙofar ya kwanta a kan 3-seater ɗin da take wajen. Yana rufe ido ya fara nadama; ya aka yi ya saki Khadeeja? Ya aka yi ya bari har ta gama idda bai mayar da ita ba? Tunda dai ai da ya mayar da ita ya san ba ta da wani zaɓi dole ta zauna da shi tunda ba za ta saki kanta ba.
Tunda yake da Khadeeja bai taɓa ganin wata damuwa game da yaransa ba, ga shi wata takwas kacal da ta bar su gidan yana neman ya gagare shi. A da ya yi zaton Naja za ta fi ta kulawa da su musamman yanda ya ga tana nuna ƙauna garesu kafin ya aureta.
To me ya canza mata ra’ayi har aka kai inda ba su da damar da za su ci abinda suke so a gidan ubansu? Lallai dole ya ɗau mataki. Haka ya wuni a office ɗin cikin rashin sukuni; yana tunani halin da yaransa suke ciki a gida sannan kuma ga shi zuciyarsa taƙki ta ƙyale shi da tunanin Khadeeja.
Tabbas da Khadeeja tana nan da babu yanda za a yi ya wuni a office yana tunanin halin da yaran suke ciki. Domin ya tabbatar duk halin da suke ciki to ita ma tana cikin wannan halin a tare da su. Ya tuno lokacin da tace ba za ta yi musu girki ba yanda suka gaya masa gari suka sha kuma garin ma tare da ita suka sha.
Ya yi dariya a fili; tabbas Khadeeja tana da rigima amma ta iya rigimarta. Ya tabbatar babu yanda za a yi ta ci kaza ta bar yara da baƙin shayi. Haka ya zauna yana aiki yana tuno rigimarsu da Khadeeja yana murmushi shi kaɗai. Bai taɓa zaton zai yi kewar rigimar Khadeeja ba amma yanzu tabbas kewar rigimar tata yake yi.
Ƙarfe ɗaya da rabi daidai suka idar da sallah a farfajiyar office ɗin su. Yana shiga office ɗinsa ya zauna a kan kujerarsa ya tura ta baya kaɗan yana juyawa ya ɗauki wayarsa wadda take kan tebur ɗin ya lalubo lambarta ya dannan mata kira, ya kara a kunnensa bayan da ta amsa yace ‘Hello.’
Bayan sun gama gaisawa yace ‘Kina ina ne? Da mamaki a muryarta tace ‘Ina office mana, akwai wata matsala ne? Murya a sanyaye yace ‘No, babu matsala kawai dai ina son ganinki. Zan iya zuwa office ɗin yanzu? ‘Umm! Akwai matsala ne? Ta sake tambaya. Ya yi ‘yar dariya ‘Babu matasala fa, akwai dai maganar da nake so mu yi. Zan iya zuwa, minti talatin kawai ya isa. ‘Ok, ina jiranka duk da dai na kusa tashi.’
Ya ajiye wayar ya miƙe ya ɗauki mukullan motarsa ya kama hanya. Yana sane ya ƙi ya kirawo ta da ya isa don so yake ya shiga ya same ta a office ɗin nata, don haka bayan ya ajiye motarsa sai ya fito ya shiga gidan talabijin ya tambaya. Ba tare da ɓata lokaci ba aka nuna masa office ɗin nata.
A hankali ya ƙwanƙwasa ƙofar, daga ciki muryarta ta ba shi amsa ‘Shigo a buɗe ƙofar take. Ya tura ƙofar ya shiga da sallama. Tana zaune a kan kujerar zaman mutum ɗaya wadda take gefe guda, da jakarta a gefenta tana ta danna waya; da alama ta gama shirin tafiya gida. Bayan ta amsa sallamarsa ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ya ƙarasa ya yi wa kansa mazauni a kujerar da take kusa da wadda take zaune a kai.
Bai san dalilin da yasa ganinta ya saka shi jin daɗi ba amma dai ya san ya ji daɗin ganinta. Cikin girmamawa ta gaishe shi kamar babu wata damuwa a tsakaninsu. Bayan ya amsa tace ‘Allah ya sa dai ba wata matsala don tunda kace za ka zo nake ta tunani.’ Ya yi murmushi yace ‘Babu wata matsala, kawai dai ina son ganinki ne.’
Ta ɗan yi gajeren murmushi tace ‘Uhm, to gani. Ya yi dariya yace ‘Kamar dai kina kora ta. Ba korarka nake ba, kawai dai ina son na tafi gida don wallahi na gaji. Ya gyara zama; ya rasa ma ta inda zai fara domin ganinta ya goge masa duk zantukan da ya tsaro zai zo ya gaya mata. ‘Yara suna kewarki.’ Ya faɗa bayan ya gama nazarin ta inda zai fara.
Nan da nan murmushinta ya ƙara faɗi, tace ‘Allah sarki ni da Hammad ma muna kewarsu. Don ma Yaya Habib yana zuwa gidan Mommy yana gaishe mu. Ya girgiza kai domin Habib bai taɓa gaya masa yana zuwa wajen Khadeeja ba, bai ma taɓa yi masa maganar Khadeejan ba tun bayan da suka rabu.
‘Ya Hammad? Ba ya kukan makaranta?’ Ya tambaya. ‘Baya yi, ka san ya haɗa wayon yayyinsa gaba ɗaya.’ Ta faɗa tana dariya. Suka yi shiru na ɗan lokaci; ita duk ta ƙosa domin so take ta tafi gida yayin da shi kuma ya gyara zama yana kwaso hira. Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan yace ‘Khadeeja. ‘Na’am.’ Ta amsa tana kallonshi.
‘Wai me yasa kika ce na sake ki? Ya tambaya yana tsare ta da ido. Ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido sannan ta sake yi masa wannan murmushin nata wanda yake ɗauke da ma’anoni daban daban tace ‘Right question at the wrong time; amma dai zan ba ka amsa.’
Ta sunkuyar da kai a daidai lokacin da murmushin fuskarta ya gushe, ta ɗago suka sake haɗa ido sannan ta gyara zama tace ‘Gajiya na yi Musatapha. Ka san idan mutum wanda bai iya swimming ba ya faɗa ruwa to zai yi ta ƙoƙarin ganin ya fita da rai ko, amma duk daɗewa zai gaji. To haka ce ta faru da ni.
Soyayya ce ta saka na aure ka, amma idan dai ba na manta lissafin ba tun a shekarar farko na rasa soyayyarka. Haka na dinga kokawar janyo attention ɗinka ko za ka fahimce ni amma ba ka ko kalli inda nake ba; kai dai abinda kake so kawai shi kake so. Na haƙura ina zama da kai a haka saboda I was ok with just sleeping beside you every night; sai kuma ka ɗauko aure.
Duk wani abu da nake so daga wajenka a lokacin ka ɗauka ka ba ta ina kallo. Haka na cigaba da kokawar samun attention ɗinka, ina ƙoƙarin ganin ka yi mana adalci amma hakan bai samu ba. Na tuna tun ina ni kaɗai ma ka fara kasa yi min adalci to balle yanzu mun zama mu biyu; ni da rabin ranka. So I gave up, ba zan iya ba, na gaji da faɗan da ba shi da ranar ƙarewa don na gane bana ma gabanka.
Shi yasa na nemi saki kuma Allah ya taimake ni ka ba ni kuma ka bar ni har na gama idda. Idanuwansa suna kan fuskarta har ta gama ta yi shiru, ya cije leɓe yace ‘Kuma ba ki gaya min ba Khadeeja? How did I not see all this? Ta yi dariya tace ‘Da wanne yaren zan gaya maka?’
Suka sake yin shiru na ɗan lokaci. Ta danna wayarta ta kalli agogo sannan tace ‘Time yana tafiya, wallahi so nake na tafi gida don na gaji. ‘Oh, sorry Suka sake yin shiru na ɗan lokaci sannan yace ‘Khadeeja yi haƙuri mu mayar da aurenmu, in sha Allahu haka ba za ta sake faruwa ba.’
Ta miƙe tsaye tana dariya tace ‘Ka yi haƙuri Mustapha amma aure ba zan sake yi da kai ba, babu wannan zance don Allah kada ka sake yinsa. Shekarun da muka yi Allah ya amfana su kuma Allah ya sa kaffara ne amma kada Allah ya maimaita mana. Ya dafe kansa da hannuwansa biyu na ɗan lokaci sannan ya sauke hannuwan ya miƙe tsaye.
Ta buɗe ƙofar ya fice sannan ta biyo bayansa suka fito daga office ɗin. Suka jero suka fito harabar office ɗin. Nan suka tsaya yana ta faman lallaɓata ta bari ya kai ta gida amma ta ƙi; yana ji yana gani ta tare taxi ta hau. Sai da ya tabbatar ta zauna a bayan motar sannan ya zagaya ya ba wa direban taxi ɗin kuɗinta. Suka ja mota shi ma ya koma ya shiga motarsa ya kama hanya.
Ya dai ji tace ba za ta taɓa sake aurensa ba amma tabbas bai yarda ba, yana ji a jikinsa in sha Allahu za ta yarda su mayar da aurensu. Yanda zai yi da baffa ne ma yafi damunsa domin ya san tabbas Baffa ba zai saurara masa ba. Haka har ya isa gida yana wannan tunanin, sai dai yana saka ƙafarsa cikin gidan ransa ya ƙara ɓaci. Bai san a yanda zai je ya sami yaran ba sannan kuma ita kanta Najan yana jin haushinta do ba zai taɓa ba ta dama ta wulaƙanta masa yara ba.
Ana cikin kiran sallar magriba ya shiga gidan, don haka ko zama bai yi ba ya ɗaura alwala ya ja Habin suka wuce masallaci. Ko da aka idar da sallar a can ya tsaya wajen magidantan unguwar suna hira, har sai da suka yi sallar isha’i sannan suka tashi daga hirar kowa ya koma gida.
A parlor ɗin kasa ya sami yaran suna harkokinsu, ya wuce ya haye sama. Tana zaune a parlor tana jiransa saboda ba ta son yanda tun da safe ya ƙi ya ko kalli inda take. Ita idan ana faɗa ta fi so a yi hayaniya kowa ya faɗi abinda yake ransa, amma ya ma ƙi ya tambaye ta me yasa ta yi wa yaran haka balle ta samu ta yi masa bayani.
Ba ta jin ya amsa sannu da zuwan da ta yi masa, idan kuma har ya amsa to tabbas ita dai ba ta ji ba. Ba tare da ya kalli inda take ba ya shige ɗakinsa. A fusace ta miƙe ta bi bayanshi. Yana tsaye a gaban mudubi yana rufe durowa ta shiga ta turo ƙofar, ta tsaya a bayan ƙofar ta rungume hannu tace ‘Ga abinci can a dining table.’
Ba tare da ya kalle ta ba yace ‘Ki sauka da shi ƙasa a can zan ci ni da yara. Ta sunkuyar da kai ‘To bari nace su hawo sai ku ci a nan, duk da su ma na zuba musu nasu abincin kuma duk tuwon ne dai. ‘Ba sai sun hawo ba ni zan sauka, ki ɗauka ki kai can.’ Ya faɗa sannan ya juya ya zauna a gefen gado.
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi, ta dafa gwiwarsa ta dan marairaice tace ‘Don Allah ka ba wa Hajia haƙuri, wallahi abinda ta gani ba haka ba ne. Kai ma ka san babu yanda za a yi na ci wani abu na hana yara. Hawowa ne ba su yi ba na ajiye musu nasu a kitchen kuma da ka shiga za ka gani.’
Ya kalle ta sheƙeƙe yace ‘Ai ba yau kika fara ba, kuma ba yau na fara yi miki magana ba. Babu wani haƙuri da zan ba ta idan kin gyara halinki su yaran za su gaya mata ai. Mugun halin da kike nuna musu kuma ki cigaba kada ki fasa. Ya miƙe zai fita, ta kama hannunsa ita ma ta miƙe tana cewa ‘Don Allah ka yi hakuri, yaran da nake hidimarsu tun kafin na aure ka kuma yanzu ribar me zan ci idan na yi musu mugunta?’
‘Ni ma shi ne abinda nake mamaki, wataƙila daman ba don Allah kike yi ba ko kuma zuga ki aka yi kika canza hali ni ban sani ba. Abinda na sani kawai shi ne kusan tun da Khadeeja ta bar gidan nan kika dage sai kin raba rayuwarki da ta yaran nan, ina kula da yanda kike ƙoƙarin ganin ba su hawo benen nan ba saboda tsabar samun waje…’
‘Don Allah ka dai wannan maganar, wallahi kai ma ka san ba haka ba ne. Na ga dai ko gidan waye akwai part ɗin mai gida inda ba a bari yara su shiga, amma in sha Allahu ba zan sake hakan ba tunda na ga kai ba haka ne tsarinka ba.’ Ta katse shi cikin ƙosawa. Ya zare hannunsa da ta riƙe ya miƙe yana cewa ‘Ki kawo min abincin parlor ɗin ƙasa yanzu.’
Ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba. Haka ta gama zumɓura baki ta sauko ta kawo masa abincin nan parlor ɗin ƙasa inda ya zauna suka ci da yaran; duk da sun nuna masa su ma tuwo aka ba su irin nashi. Haka ya kafa mata dokar idan dai yana gidan to a parlor ɗin ƙasa zai dinga cin abinci wajen yara, babu roƙon da ba ta yi masa ba a kan ya bari yaran su dinga hawowa saman ana cin abincin tare amma ya ƙi ya saurare ta.
Ya kula cewa ganin saman bene take kamar wani abu na musamman don haka ya yanke shawarar bar mata saman benen ita kaɗai. Ya yanke shawarar a ƙasa zai dinga zama hira kuma a nan zai dinga kallo yana cin abinci, in ya so idan zai yi bacci ya dinga hawa saman ya kwanta. Ta yi yanda take so da saman ita kaɗai.
Yana sane ya ƙi zuwa gidan Hajia a ranan sai washegari; ya san idan ya je zancen nan bai huce ba Hajia da Alaji haɗuwa za su yi a kansa har sai ya rasa abinda yake masa daɗi. Don haka washegari yana tashi daga office ya wuce gidan Hajia. Bayan sun gaggaisa ya sami Alhaji a parlor, yana gama amsa gaisuwarsa yace ‘Mustapha me yake faruwa ne a gidan naka? Ban ji daɗin bayanan da na samu daga wajen Habib ba kuma sai ga Hajia ta je ta gani da idonta. Me yake faruwa ne?’
Ya gyara zama ya shafa kansa sannan yace ‘Wallahi Alhaji ‘yar matsala ce aka samu kuma na ma yi mata magana in sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba. Ya tashi daga kashingiɗar da yake yana cewa ‘Yar matsala? ‘Yar matsala fa kace Mustapha? An bar yara a ƙasa kamar masu zaman kansu amma kana cewa ‘yar matsala? Gidan naka har ya kai an raba tukunya, ta marayun yaranka daban ta matar gida daban.
Anya kuwa Mustapha? Rashin uwa ai ba hauka ba ne da za ka wulaƙanta su saboda Allah ya ɗauki ran mahaifiyarsu. Ya sake shafa kansa ‘Wallahi Alhaji akasi aka samu kuma in sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba. Ya kawar da kai cike da damuwa ya yi shiru, jimawa kaɗan ya cigaba ‘Ita Khadeeja ya wajen nata da Muhamadun? Kana zuwa dai?’
Ya gyara zama yana murmushi ‘Eh, ina zuwa. Jiya ma na je. ‘To ya kamata dai ka san yanda za a yi ku daidaita tsakaninku tunda dai ka ga ita ba a taɓa samun wata matsala tsakaninta da yaran nan ba, haɗawa ta yi ta riƙe su tun kafin ma ta sami nata. Kuma da ta sami natan ma babu abinda ya canza. Ka ga ita ce ta zama uwa ta gari a wajensu tunda ga su ƙalau da tarbiyyarsu.’
‘Haka ne Alhaji, in sha Allahu za mu daidaita. ‘Ya kamata dai ka san abun yi tunda ka san dai yanzu a kasuwa take, idan ba ka maida hankali ba wani zai iya yi maka shigar sauri. Suka ƙarasa hirarrakinsu sannan ya yi musu sallama ya wuce office.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Talatin Da Biyu
Edita@rumasau-kallamu






