Ba ƙaramin mamaki Hajia da Alhaji suka yi ba da Mustapha ya gaya musu ya saki Khadeeja. Shi kaɗai ya shiga da yaran don ita Naja ma cewa ya yi ta zauna a mota saboda kada taɓbata musu lokaci. Suna shiga yaran suka wuce cikin gida shi da Hajia da Alhaji suka tsaya a parlor yana musu bayanin abinda ya faru.
Alhaji yace ‘To kai wane irin rashin hankali ne wannan? Ai don mace tace a sake ta ba a sakin nata. Zuciya ce ta kwashe ta kuma sai daga baya za ta zo tana nadama. Da ka sani ka ba rta da aurenta idan ma tafiyar za ta yi ta tafi idan ka dawo ƙalau za ka ga ta dawo.’
A fusace yace ‘Alhaji yarinyar ce ta ƙure ni, ita kullum sai dai a yi mata yanda take so amma ita ba za ta yi yanda ake so ba? Ta je idan mutuwar aure daɗi ne ai ta samu sai ta ɗana ta fi shiga hankalinta. Hajiya tace ‘Ai shikenan tunda haka ta zaɓa. To yanzu ina Hammad ɗin da Rukayya? Ban gansu tare da ‘yan uwansu ba.’
‘Shi Hammad dama yana gidansu, ita kuma Rukayya gidansu ta kai ta. Ai shikenan, Allah ya sauwaƙe. Idan ka dawo a san yanda za a yi domin dai aure bai kamata ya mutu saboda kujerar hajji ba.’ Alhaji ya faɗa cike da nadama. Mustapha ya dubi Hajia yace ‘Mukullin gida yana hannun Habib in an jima Baba Sani abokina zai zo ya kai su shi da Afaf su ɗebo kayansu su rufo gidan.
Idan sun dawo sai ya ba wa Alhaji mukullin gidan ya ajiye min. Akwai ATM card ɗina hannun Afaf idan ana buƙatar wani abu na kuɗi sai ta je ta ciro ta bayar. Ya yi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da damuwa.
Zuciyarta fayau ta fito daga gidan tana addu’ar Allah ya sa iyakar zamanta kenan da Mustapha tunda ta san saki ɗaya ya yi mata. Suna tsaye a bakin titi ita da Hafsa suna jiran mota ya zo ya wuce su a guje a tashi motar. Ta bi bayan motar da kallo tana murmushi; ta tuna lokutan da yake zuwa ya wuce ta a titi za ta tafi makaranta amma ba zai iya rage mata hanya ba.
Ta yi murmushi ta kawar da kai. Jimawa kaɗan da wucewarsu ta sami mota, suka hau suka nufi gidan Mommy. Tana tura gate ɗin gidan Baffa ne a tsaye yake rufe motarsa, da alama dawowarsa kenan. Suna haɗa ido da shi hawayen da ta kasa fitarwa ya ƙwace, ta saki akwatin da take ja.
Ahmad wanda yake tsaye a kusa da shi ya ƙarasa ya riƙe akwatin yayin da ita kuma ta ƙarasa ta faɗa jikin Baffa wanda yake bin ta da kallon mamaki. Ya rungume ta sannan ya dafa kanta wanda ta kwantar a ƙirjinsa yana cewa ‘Subhanallahi! Me ya faru da ku Khadeeja? Ta kasa magana sai kuka kawai take har da shessheƙa.
Baffa ya fara shafa bayanta yana cewa ‘Ya isa haka, ya isa, ki gaya min me ya faru? ‘Ya sake ni.’ Ta faɗa a cikin shessheƙar kuka kamar mai raɗa. Take fuskar Baffa ta canza, ranshi ya yi matuƙar ɓaci. Yace ‘Mustaphan ya sake ki? Ta ɗaga masa kai. Ya sake shafa kanta cikin yanayi na lallashi yana cewa ‘To shikenan, ya isa haka.’
Ya ja hannunta suka shige gidan; da yake Mommy tana ɗakinsa kai tsaye can ya wuce da Khadeeja. Mommy tana ƙoƙarin yi masa sannu da zuwa ta kula da Khadeeja, tace ‘A a, Baffa a ina ka samo wannan? Ya zaunar da ita a gefen gadonsa yace ‘Mustapha ya sake ta. ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Saki kuma? A yau ɗin? Na ɗauka ce min kika yi yau jirginsu zai tashi?’
Ta share ragowar hawayenta ta ajiye jakar hannunta sannan tace ‘Eh, kafin su tafi airport ɗin ne ya sake ni saki ɗaya. Lallai Mustapha, to me kika yi masa ya sake ki? Ko kuwa dai tsabar wulaƙanci ne ya ga gara ya sake ki kafin ya wuce ya yi ibada?’ Mommy ta tambaya tana daga tsaye.
Ba ta yi tunanin wata amsa da za ta bayar idan an yi mata wannan tambayar ba, amma dai tana jin gara ta faɗi gaskiya don ma kada ya zo shi ya ba da amsa da ta bambanta da tata. Ta ɗaga fuskarta suka haɗa ido da Mommy sannan ta sunkuyar da kai. Murya kasa-kasa tace ‘Ni nace ya sake ni.’
Saura kaɗan wayar da take hannun Mommy ta kufce ta faɗi, ta riƙe wayar sannan tace ‘Kika ce ya sake ki Khadeeja? Saboda rashin hankali ko saboda me? Baffa da yake tsaye a gaban wardrobe ɗinsa yana rataye babbar rigarsa ya zagayo ya zauna a kusa da ita yana kallonta yace ‘Dije me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
Kafin ta yi magana Mommy tace ‘Saboda wulaƙanci mana, ko kuma saboda yace ba zai je da ita aikin Hajji ba sai ya je da amaryarsa. Kallonta kawai Baffa ya yi ta yi shiru, ta gyara tsayuwarta tana binsu da kallo. Ya dubi Khadeejan ya sake cewa ‘Deeje me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
Ta kalle shi suka haɗa ido sannan ta sake sunkuyar da kai tace ‘Baffa na gaji, wallahi Baffa ba ka ga zaman da muke yi a gidan nan ba. Tun kafin ya auri matarsa Baffa dama haƙuri nake, matsayina a gidan da kaɗan ya wuce matsayin ‘yar aiki. Kuma bayan ya auro ta ma ya kara tabbatar min da hakan; duk wani abu na walwala da jin daɗi da ita ake yi amma wallahi idan aiki ne da wahala Baffa ni zai kawowa kuma dole na yi.
Ita kanta matar tasa haka yake saka ni na yi mata aiki babu sannu bare na gode. Shi yasa kwanaki da nace ba zan yi ba ya zo ya kawo maka ƙarata. Wallahi Baffa a lokacin sai da na yi wata takwas ina mata aikin gida da girki da komai kuma kullum shi a wajenta yake kwana.’Ta sake sunkuyar da kai ‘Na gaji Baffa, ba ya sona, wulaƙancin da yake min suna da yawa, gara na haƙura kawai shi yasa nace ya sake ni.’
Ya kama hannunta wanda take wasa da shi a kan cinyarta ya kalle ta suka haɗa ido yace ‘To ya isa, kuka ya isa haka. Ki je ki kai kayanki ɗaki ki huta ma yi magana wani lokacin.’ Ta gyaɗa kai ta miƙe ta fice daga ɗakin. A fusace Mommy ta bi bayanta, cikin sauri Baffa yace ‘Zo mana.’
Ta juyo a daidai lokacin da Khadeejan ta rufe ƙofa, ya nuna mata inda Khadeejan ta tashi ta zauna. Sai da ya ɗauki lokaci yana kallonta sannan yace ‘Ki bi ta a hankali tunda dai kin ji bayaninta. Ni da na ba shi aurenta ai ba ‘yar aiki na ba shi ba ko? In ya dawo ya zo ya yi bayani in ya so sai a san matakin da za a ɗauka.
Shi a zaman aure ma wani lokacin hutu kawai mutum yake buƙata; kada ki je ki ɗaga mata hankali. Ki barta ta huta ƙarshenta in ya dawo sai dai ki ji da kanta tana gaya miki ya mayar da ita za ta koma. Da-Allah kada ki ɗaga mata hankali tunda dai ita ta kawo mutumin nan tace tana so ai ba laifi ba ne idan ta dawo tace bata son shi.
Ki ba ta lokaci ta sami nutsuwa tukunna. Ta sauke numfashi sannan tace ‘To. Ta tashi ta fice ta bar shi a ɗakin. A nan gidan Hajia ya ajiye motarsa ya samar musu taxi wadda za ta kai su airport, ya shiga gaban mota ita kuma ta shiga baya. Suna kama hanya ta zaro wayarta ta lalubo lambar Anti Wiyya ta tura mata sako ta wahtsapp tana sanar da ita an saki Khadeeja.
Bayan sun gama hirarrakinsu na murna da nuna jin daɗi Anti Wiyya ta turo mata saƙo kamar haka “Kije ki yi ta addu’a Allah ya sa kada kuna dawowa ya dawo da ita. Nan ma in sha Allah akwai wani malami da zan kai wa abin sadaka ya yi miki aikin da ba za ta taɓa dawowa gidan ba, kin ga kin ci gida se yanda kika yi.”
Ta turo mata emoji na dariya ta rufe wayar, ta mayar da hankalinta kan hanya zuciyarta fes cike da fatan Allah ya sa kada ya dawo da Khadeeja tunda ya ce saki ɗaya ne; in ya so sai ta ji da yaran kawai. A hankali Khadeeja ta ba je kayanta a gida; ta sanar da Baffa ko da ya dawo ma ba za ta koma ba domin ko ya mayar da aurenta to kotu za ta kai shi ya sake ta.
A haka dai aka bar maganar domin shi Baffa gani yake kamar idan aka ba ta lokaci ta huce za su yi wa kansu sulhu ita da shi. Tun Baffa yana sa rai zai ji kira daga wajen iyayen Mustapha sun biyo sawu har ya fitar da rai. Saura kwana biyu babbar sallah suna zaune a parlor shi da Mommy suna hira yace ‘Mutanen nan dai shiru, babu wanda ya biyo sawun Dije.
Na san dai babu yanda za a yi su ce ba su san ya sake ta ba tunda ai za su ga ba ita ya barwa yaransa ko? ‘Uhm, ni abun har ya ishe ni ma wallahi. To amma ko tuntuɓarsu za ka yi ka ji, tunda ai ba za mu taru mu zama ɗaya ba ko?’ Mommy ta ba shi amsa. Ya yi ‘yar dariya yace ‘Babu wanda zan tuntuɓa tunda ai da zan ba su aurenta ba ni na tuntuɓe su ba su suka zo har gida suka tuntuɓe ni.
Idan na tuntuɓe su haƙuri zan ba su ko me? Ni aka yi wa wulaƙanci aka saki ‘yata ko ma don wanne dalili ne amma kuma ni ake jira na yi magana? To su cigaba da zamansu kada ma su zo inda nake. A haka suka bar zance domin Mommy ta san in dai Baffa ne yanda ya kafe ba zai yi magana ba to tabbas ba zai yin ba.
Su ma daga can gidansu Mustapha a tunaninsu Baffan Khadeeja ne ya kamata ya neme su don ya kamata idan ta je gida a bincika a ji, sai dai har aka shiga hidimar bikin sallah babu wanda ya neme su. Sai suka bar maganar kawai suna jiran Mustaphan ya dawo su ji ko shi ya yi magana da iyayen nata.
Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Tara
Edita@rumasau-kallamu








