Majin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Biyu

0
6

Ta yi zaton ranar da kwana zai dawo kanta za ta ji tana cikin yanayin murna, sai dai ba hakan ya kasance ba. Yau ne za ta karɓi kwana amma sai ta ji kamar ma ba za ta iya bari ya kusance ta ba saboda kamar dai har yanzu ƙoƙari take ta saba da cewa su biyu ne matansa.

Haka dai ta tashi ta gama duk wata hidima da take yi. Ya riga ya sanar da su cewa da daddare za a dinga karɓar kwanan don haka tun yamma ta shirya abincin dare; duk da ba ta cikin walwala amma haka ta girka abincin da ta tabbatar yana so; tuwo miyar kuɓewa danya. Ta haɗa komai ta jera a table ɗin sama.

Sai dai ga mamakinta har wannan lokaci Naja tana ɗakinsa na sama, don haka ma ba ta ko je kusa da ɗakin ba tana jiran ya dawo ta ji ko shi ne zai biyo ta ɗakinta tunda dai kwananta ne. Da yake bayan ya ci abincin rana ya sake fita sai wajen 8pm ya shigo gidan.

A ɗakinta ya same ta tana miƙe a kan gado da Hammad a kwance a kan cikinta yana wutsil-wutsil ɗinsa. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya ƙarasa ya zauna gefen gadon ya sa hannu ya ɗauki Hammad yana masa wasa. Suka ɗan taɓa hira sanna tace ‘Um ga abinci can a dinin fa, idan ka shirya sai mu je mu ci.

Yara dai sun ci nasu don yau tun magriba Nas ta fara jin yunwa. ‘Oh,Ok.’ Ya amsa kamar mara gaskiya. Tace ‘Kuma na ga amarya har yanzu tana ɗakin naka fa, ko a nan za mu kwana ne? Kamar wanda aka tayar daga bacci yace ‘Umm. No, umm kin gane? Dama ina so na yi miki magana don da na san za ki dafa abincin daren zan ce ki dakata.’

Ta kalle shi da mamaki tana jira ta ji ƙarashen bayanin, suka haɗa ido ya yi sauri ya kawar da idonsa. Suka ɗan yi jim sannan ya cigaba ‘Ina ga ya kamata tunda ke kina jego ki bar mata kwanakin naki zuwa lokacin da za ki cika arba’in ko? Ta tashi zaune tana ƙarewa Mustapha kallo ko zai sauya maganarsa, kamar bai fahimci saƙon ba don sai ya ƙara haɗe rai yana wasu muzurai.

Ta yi murmushin yaƙe tace ‘Oh, yanzu kenan kwanan gaba ɗaya na amarya ne har sai na cika arba’in da haihuwar Hammad? ‘Eh, to ai kinga kina jego. Menene amfanin kwanan? Ta sunkuyar da kai, ta ɗago ta kalle shi sanna ta yi gajeran murmushi tace ‘Haka ne, Allah ya kai mu arba’in ɗin.’

Kamar wanda aka tsikara ya miƙe yana yage baki yana cewa ‘Yauwa, to bari na je sai da safe ko. Cikin sauri ya miƙa mata Hammad fice daga ɗakin kamar wanda yake tsoron kada ta riƙe shi tace ta fasa. Ta bi ƙofar da kallo bayan ya fice; wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan fuskarta a daidai lokacin da wani malolo ya taso ya tokare mata maƙogoro take neman kasa numfashi.

Sautin rufe ƙofar ya dawo da tunaninta cikin ɗakin bayan da ta kifta idonta; ta yi murmushi mai ciwo tare da sunkuyar da kai. Wato dai yanzu Mustapha ya yi sabuwar amarya har ya fara gudunta, tunda ai lokacin da ta yi ɓari sai da ya nuna ɓacin ransa a kan tafiyar da ta yi gida. To me yake nufi da ita?

Wato idan wahala ce ta je ita kaɗai ta yi ta sha kenan, lokacin da zai iya morarta shi ne lokacin da zai ba ta kwana. Lallai akwai aiki amma dai ba za ta fasa addu’a duk da zuwa yanzu duk dan wani karsashin kyautatawa Mustapha da take so ta yi ya zirare. Sai da Hammad ya fara kuka sannan ta yi ajiyar zuciya ta sa bayan hannunta ta share hawayenta sannan ta miƙa hannu ta ɗauko shi daga inda yake kwance ta saka masa nono.

Har ya gama shan nonon ya saki tana ajiyar zuciya, ta shirya shi ta goya shi sannan ta fice daga ɗakin. Da yake dare ya yi tana jiyo muryarsu ƙasa-ƙasa sun hira tunda ɗakin nasa yana jikin nata ɗakin. Haka ta wuce da yake a parlor ɗinta ta jera musu abincin daren can ta wuce ta je ta kwashe ta mayar kitchen tana ƙwafa. Ta dawo suka kwanta ita da Hammad.

Duk yanda take jin bacci a wannan daren kasawa ta yi, sai dai da yake bacci ɓarawo ne sai da ya faki idonta ya sace ta; sai ji kawai ta yi ana assalatu. Duk da ba sallah za ta yi ba sai da ta tashi ta wanke fuska sanna ta zauna ta yi azkar ɗinta sannan ta koma ta kwanta.

Tun kafin a ɗaura aurensa da Naja ya riga ya gaya mata amarci za su yi na kusan kwana talatin domin lokacin da za ta tare zai yi daidai da kwanan Khadeeja goma sha biyu da haihuwa. Don haka ya sanar da ita gaba ɗaya kwanan nata ne har sai Khadeeja ta gama jego kwana arba’in. Ita Khadeejan ce bai gayawa ba shi yasa ma ta zata za a yi yanda aka saba ne ta karɓi kwananta bayan kwana bakwai.

Ba ƙaramin daɗi ya ji ba da Khadeeja ta amsa masa ko da yake dama bai sa ran za ta ba shi matsala ba tunda dai ta san ba za ta biya masa buƙatarsa ba wadda a wannan lokacin ko Allah ma bai haramta masa ya kai wa ɗaya matar tasa buƙatar ba. Cikin walwala suka kwana shi da amaryarsa, ko da ya fito da asuba zai tafi masallaci ya hango fitila ta kasan kofar ɗakin Khadeeja don haka ma ya san ta riga ta tashi.

Da sallama ya shigo parlor ɗin bayan ya dawo daga masallaci, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin don ya jiyo motsinta a can. Tana tsaye da goyon Hammad tana zuba ruwan zafi a flask. Bayan ta amsa sallamarsa ta gaishe shi; yana ta wani kau da kai yana muzurai kamar yanda ya saba idan yana so ya gwada mata son kai haka ya amsa gaisuwar tata.

Ta mayar da kettle ɗin inda take sanna ta buɗe fridge don ta ɗauko ragowar peppersoup ɗinta. Yace ‘Ina yaran? Ba su taso ba. ‘Eh.’ Ta amsa a gajarce ba tare da ta bar abinda take yi ba. Ya kula da yanayinta idan ya takura ta za ta iya birkice masa a safiyar don haka yace ‘Ok, idan sun shirya ki ce su buga min ƙofa please.’

‘Ok.’ Ta sake ba shi amsa a gajarce. Ya juya ya fice daga kitchen ɗin. Ta ƙarasa ɗumama soup ɗinta ta juye a flask, ta ɗauki ruwan zafinta ta haɗa ta kai ɗaki sannan ta dawo ta ɗauki kayan shayi duka ta shigar ɗaki. Ta zauna ta ci burodi da soup ta sha shayinta mai kauri sannan ta koma ta kwantar da Hammad ita ma ta kwanta.

Ba ta daɗe da kwanciya ba kuwa bacci ya ɗauke ta saboda dama na jiya ba isar ta ya yi ba. Kamar a mafarki ta ji ana buga mata ƙofa, ta yi firgigit ta buɗe ido. Ko ba a gaya mata ba ta san wannan bugun Habib ne don haka ta tashi zaune ta janyo wayarta ta duba lokaci; 8:25am. Ta janyo zanin goyon Hammad da ke kusa ta rufe jikinta sanna tace ‘Shigo Habib.’

Ya turo ƙofar ya shigo da sallama, tun kafin ta gama amsa sallamar tasa yace ‘Anti yau makara kika yi ne? Yanzu har past 8 fa kin ga ba mu tafi makaranta ba. To me yasa ba ku tafi ba? Ni ai na zata kun tafi tuni. Ya ƙarasa ya zauna a bakin gadon da mamaki a fuskarsa yana cewa ‘Anti ba ki tashe mu ba fa; ni ma bayan mun dawo daga masallaci da Abba har na yi wanka fa na ɗan kwanta don na san za ki tashe ni shi ne bacci ya kwashe ni.

Su Afaf ma ga su can ko sallah ma ba su yi ba sai yanzu na taso su har Hafsan. Ta kama haɓa tana cewa ‘Ikon Allah. To ai ba ni ce da girki ba Habib, Antin ku ce. Ita ce za ta tashi kowa ta shirya shi yasa ma ka ga ban fito ba. Ya taɓe baki yana zare ido ‘Tab, to ai kuwa daga ita har Abban babu wanda ya fito.’

‘To Allah ya sa dai lafiya, ka je ka buga musu ƙofa. Ka murɗa kofar parlor ɗin a buɗe take sai ka ƙwanƙwasa ɗakin ka ji. Ya miƙe ya fice daga ɗakin yayin da ita kuma ta zame ta gyara kwanciyarta da niyyar komawa bacci.

A tsakiyar parlor ɗin Habib ya ci karo da Abban nashi yana fitowa da gaggawa, suka haɗu a tsakiya suka yi cirko-cirko. Abban nasu yace ‘Kai Habib meye haka? Na cewa Anti ku taso ni idan kun shirya me yasa ba ku taso ni ba? Kai ko uniform ma ba ka saka ba. Yace ‘Abba ai makara muka yi, Anti Najan ba ta tashe mu mun shirya ba.”

Kafin ya ba shi amsa sauran yaran suka shigo kowa da kayan bacci, ya kalle su sannan ya mayar da hankalinsa kan Habib din yana cewa ‘Wace Anti Naja kuma, ko dai Anti Khadeeja? ‘To ai ita ma Antin bacci take yi yanzu na je tashinta tace min ba ita ce da girki ba Anti Naja ce za ta shirya mu.’

Mamaki ya kama shi; ya za a yi Khadeeja ta gayawa yaro wannan maganar? Wane irin wulaƙanci ne bayan ita ce ta saba shirya yaran kawai kuma yanzu sai tace Naja ce za ta shirya su? Ba tare da yace komai ba ya wuce yaran ya nufi ɗakin Khadeejan. Habib ya dubi ‘yanuwansa yace ‘Yau dai mun yi mising school, ni yunwa nake ji ma ku zo mu je ƙasa bread yana can ko shayi sai mu haɗa.’

Ya wuce suka bi shi suka sauka ƙasa. Kusan a fusace ya tura ƙofar, hango ta da ya yi a kwance tana bacci ya ƙara harzuƙa shi. Sautin buɗe ƙofar ne ya farkar da Hammad daga bacci. Ta tashi zaune tana mittsike ido sanna ta miƙa hannu ta ɗauke shi. Ta dubi Mustapha cikin halin ko in kula tace ‘Ohhh! Abba ka tayar min da yaro yanzu babu sauran bacci.

Ta ɗaga shi ya yi miƙa sannan ta saka masa nono yayin da Mustaphan yake cewa ‘Me ya faru na ga ba ki tashi kin shirya yara ba bayan yau akwai makaranta, kuma fa ko da asuba sai da na ce miki idan sun shirya ki ce su yi min magana? Tace ‘Oh! Ai ba su zo sun ce min sun shirya ba na zata ma sun gaya maka kun wuce sai da Habib ya gaya min yanzu sannan na sani.’

‘Ban gane ba, wai wace magana kike yi ne? To me yasa ba ki tashi kin shirya su ba? ‘Oh to ai wadda take da kwana ita ce da gida musamman ma da yake ni ina jego. Na zata da ka kai mata kwanan ka gaya mata abinda aka saba yi na running gidan. Mamakin da yake fuskarsa ya ƙaru ya haɗe da takaicin Khadeeja, yace ‘Ban gane wadda take da kwana ita ce take da gida ba Khadeeja.

Ke kika saba shirya yaran nan kullum kuma kin san haka, shi ne yau saboda ganin ido za ki ce ita za ta shirya su? Idan kina jin haushina ai sai ki gaya min tunda ba dole na yi miki kika bar mata kwanan ba ko? Za ki fara wulaƙancin naki ko Khadeeja? Ta yi dariyar yaƙe tace ‘Wallahi ni duk ban gane ba.

Ai ni a yanda na sani duk matar da take da kwana da girki ita ce take duk wata harka ta kula da gida, ni ma idan na karɓi girki sai na haɗa gaba ɗaya na yi. ‘Khadeeja, ba na son wulaƙanci. Yaran nan a hannunki suke kuma da ke suka saba, ya za a yi tana zuwa ki ɗora mata kula da su ita da yau za ta koma aiki ma.’

‘Amma dai ba da su na zo ba a nan na same su ko? Kuma idan ban manta ba ni ma daga zuwana aka haɗa ni da su, kamar ma ita an ɗaga mata ƙafa. Hidimarsu ta makaranta ma wadda ta riga ta saba yi tun ma kafin ta auri ubansu balle yanzu da ta aure ka, ai ina ga wannan ma ƙaramin abu ne.’

Ya gama ƙulewa har wani huci yake, ya cije leɓe sannan yace ‘Khadeeja ba na son wulaƙancinki fa, yanzu me kike nufi da yaran nan? ‘Alkhairi nake nufi da kowa, kawai dai duk wadda take da kwana ta haɗa duk har gidan da yaran ta kula da su. Shikenan. Har ya juya zai fita ya juyo ya nuna ta da yatsa yana cewa ‘Yanzu shikenan kin tura mata yara har tsawon sati huɗu?

Ta ɗago ta kalle shi cikin halin ko in kula tana cewa ‘Na tura mata mijin ma? ‘Mtsewww!’ ya ja dogon tsaki ya fice ya maka mata ƙofar. Ta yi ‘yar dariya ta cigaba da wasa da Hammad. Har ya koma ɗakin tana kwance tana baccinta domin office ɗin da za ta ta riga tace sai wajen sha ɗaya za ta tafi saboda an canza mata branch sakamakon aurensu da Mustapha; ta san tunda yau za ta fara reporting tana da damar makara.

A hankali ya buɗe ƙofar ya shiga saboda kada ya tashe ta daga bacci, ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon. Ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yana shafa fuskar, gaba ɗaya kansa ya kulle. Ya yi zaton yaran nan tunda suna wajen Khadeeja shikenan a wajenta za su cigaba da zamansu ko da ya ƙara aure.

Gaba ɗaya ma shi bai taɓa zama sun yi maganar yara da Naja ba, kawai dai yana saka ta hidimarsu idan ta kama kuma yana nuna mata cewa yana so su sami kulawar da yake jin sun rasa daga wajenta. Baya jin za ta ba shi matsala saboda yanda ya ga tana kulawa da su tun ma kafin ta aure shi balle yanzu da za ta yi da hujja. Ya juya ya ɗan taɓa ta. Ta buɗe ido ta kalle shi ta yi murmushi sannan ta yi miƙa.

Tace ‘Honey har ka dawo? Ya ɗan kawar da kai sanna yace ‘Daga ina? ‘Umm! Na zata ‘yan makaranta ka kai. ‘No, ban kai su ba sun riga sun makara sosai sai gobe. ‘Ok, Allah ya kai mu. Ta zuro ƙafafunta ƙasan gadon ta kwanta a kafaɗarsa tana cewa ‘Bari na je na yi wanka sai na fito na haɗa mana breakfast. Ina jin ma kawai sai na shirya ka ba ni lift.’

Yace ‘Ai kuwa sai ki yi sauri don ga yara can ma ke suke jira ki zo ki ba mu abincin gaba ɗaya. Ta ɗaga kafaɗarsa ta ɗan kalli fuskarsa da mamaki ‘Antin ba ta nan ne? Ya kawar da kai daga kallon da ta kafe shi da shi, yace ‘Tana nan. To ai kin ga kece da kwana don haka ke ce za ki dinga yin abincin duka gida kina kula da yara, in ya so idan ta karɓi kwana sai ta cigaba.

Duk wadda take da kwana ita ce da gida. Ta sake leƙa fuskarsa da mamaki a kan fuskarta tace ‘Ban gane ba, ai ni ban karɓi girki ba, kwana ne kace ka tambaye ta ta ba mu har ta yi arba’in. kuma yara ai na zata tunda a wajenta suke sai su yi zamansu duk abinda ya kama ai zan saka hannu.’

‘A a, wadda take da kwana ita ce za ta dinga haɗawa ta yi komai kawai. Ki yi sauri ki yi wankan ki zo ki ba mu abinci. Shiru ta yi kawai tana bin shi da kallo. Jimawa kaɗan ya kalle ta suka haɗa ido, ya gyara zama ya kama hannuwanta duka biyun ya riƙe sannan yace ‘Kin ga wannan fa ba wani abun damuwa ba ne, ai dama kin san duk inda ake da mace sama da ɗaya ai dama duk wata hidima rabawa ake yi.

Idan yanzu kika ki yin wani abu ai sai ki janyo kwanan amarcin ya ƙare tunda kin ga dole ne na koma kan tsarin kwana bibbiyu don tabbatarwa an yi adalci ko? Ta sunkuyar da kai tana kallon ƙasa don gaskiya ita ba ta zata haka ba; ba wai ba za ta kular masa da yara ba amma dai ta sa rai za su yi zamansu a wajen uwarsu ita ce za ta dinga hidimarsu ta kullum in ya so ita duk wanda ya zo inda take a cikinsu za ta yi masa duk wani abu da ya kama.

Ta ɗago ta kalle shi tace ‘To yanzu kenan duk wadda take da kwana ita ce za ta dinga tashi tana yi wa yara komai? Ya ɗaga mata kai alamar e. ‘To idan za ni aiki fa. Ya kama haɓarta ya ɗago fuskarta, suka haɗa ido ya yi mata murmushi sannan yace ‘Ki bari wannan a hankali za mu ga yanda za a yi.’

Ta ɗan ja baya za ta tashi, ya riƙe fukarta ya sake tsare ta da ido har sai da ta yi murmushi, ya sumbaci leɓenta sannan ya miƙe yana cewa ‘Muna ƙasa muna jiranki ni da yara. ‘Ok.’ Ta amsa sannan ta shige banɗaki. Ya tashi yafito daga ɗakin. A parlor ya tarar da yaran suna zaune suna shan shayi da burodi wanda Hafsa ta dafa musu ruwan zafin. Ya nemi waje ya zauna ya ɗauki remote ya canza channel.

Ya fi minti talatin da zama shi da yaran suna ta hira sannan ta sauko, ta sha kwalliya sai ƙamshi take yi. Bayan ta amsa gaisuwar yaran kai tsaye ta wuce part ɗinta, nan da nan ya tashi ya bi bayanta yayin da Nasreen da Shukra suka rufa masa baya. Nan da nan ta soya ƙwai ta haɗa musu da shayi suka zauna shi da ita a dining table suka karya.

Suna gama karyawa shi ma Mustaphan ya shirya suka fito tare. Har za su sauka daga bene sai kuma ya ba ta mukullin motar yace ta fito ta jira shi zai yi sallama da Khadeeja. A parlor ɗinta ya same ta tana kwance a kan doguwar kujera da remote a hannunta yayin da Hammad yake cikin baby rocker ɗinsa yana ta wutsil-wutsil.

Tana daga kwance ta amsa sallamarsa, ya ƙarasa kusa da kanta yace ‘Za mu fita ni da Naja, ita ma yau za ta koma aiki. Tace ‘Ok, a dawo lafiya. Har ya juya zai fita tace ‘Ta dai bar wa yara abincinsu ko? Ga shi za su je islamiyya ko da yake na san sun yi wanka in lokacin ya yi ko Hafsa sai ta taya su shiryawa su wuce.’

Ya juyo ya tsaya ya zuba mata ido na ɗan lokaci; ya ma rasa ta ina zai fara. Ya kan rasa yaren da zai yi wa Khadeeja magana da shi idan ta fara wannan taurin kan nata, lokuta da dama ya kan ɗauka cewa tana jin tsoronsa amma fitinar da yake gani a ƙwayar idonta idan tana wannan taurin kan tana ba shi tsoro. Ya cije leɓensa sanna yace ‘Fita fa nace miki za mu yi, ya kike so ta yi da abincin ranansu?’

Ta tashi zaune ta gyara zamanta sannan tace ‘Yanda nake yi idan zan tafi makaranta ko? Ya jijjiga kai sanna yace ‘Khadeeja please kada ki saka min ciwon kai da safen nan, ga yara nan ki ba su abinci in ya so idan mun dawo ta ba su na dare. Idan kuma kin ga dama ki bar su da yunwa. Ta kalle shi suka haɗa ido ta yi masa gajeran murmushin yaƙe ta zame ta kwanta ba tare da ta ce masa komai.

Haka shi ma ya juya ya fice zuciyarsa cike da wasi-wasi saboda ya san wannan murmushin nata ba wai yana nufin za ta kula da su ba ne, amma dai ya tafi yana addu’ar Allah ya sa ta kula masa da su.

Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Ɗaya
Labarin na GabaWasu Kayan Aikin Ƙira
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.