Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Biyu

0
79

Ranar Sallah yana tashi ruwan shayi kawai ya sha ya shirya ya fice; bayan an idar da sallar idi kai tsaye gidan Mama ya wuce wajen yaransa. Yana gamawa da su ya wuce gidan Mommy wajen Khadeej; ko da dai ya ji haushin yanda ta yi zamanta a gidansu ta ƙi dawowa amma ya san ya yi kewarta.

Duk wani haushi nata da yake ji ya riga ya huce, abu ɗaya yake so a yanzu shi ne ta dawo gida ya samu ya daina fama yawo shi da yaransa sai kace wasu waɗanda ba su da gata. Ya kalli kayan sallarta waɗanda ya taho da su ya kai mata ko za ta ƙara, ya kau da kai ya cigaba da tuƙinsa.

Shi ya ga ma kamar ba ta damu da kayan sallar ba tunda da ita aka kai ɗinkin amma da yake ta so ta yi sallah a gida ko bi ta kansu ba ta yi ba sai ma ce masa da ta yi Baffa ya yi mata kayan sallah. Haka dai ya yi ta tunani kala-kala har ya ƙarasa gidansu Khadeeja.

Lafiya ƙalau suka gaisa cikin mutunci kamar babu wanda yake jin haushin wani a tsakaninsu; ya shiga ya gaida Mommy sannan ya gaida Baffa. Suka dawo ita da shi suka zauna a parlor ɗin baƙi inda ba tare da ɓata lokaci ba ta kawo masa tuwon sallah da lafiyayyen zobo mai sanyi. Suka zauna yana ci tana yi masa hira.

Bayan ya gama ya huta ya yi wa Baffa sallama inda Baffan ya sanar da shi jibi ya zo ya ɗauki matarsa. Suka fito tare da Khadeejan ta rako shi bakin mota. Tana tsaye riƙe da murfin kofar motar yayin da shi kuma yake zaune a kujerar direba ya juya kujerar baya ya ɗauko ledar da take ajiye a kan kujerar ya miƙa mata yana cewa ‘Ga kayan sallarki duk da na ga ba ki damu da su ba.’

Ta yi ‘yar dariya tana tura masa ledar tace ‘Ka koma da su ka ajiye min a ɗakina tunda jibi zan dawo. Shi ma dariyar ya yi yana mayar da kayan yana cewa ‘Ko dubawa ma fa ba ki yi ba. Haba kayan da na riga na sansu, idan na dawo zan duba sannan na yi kwalliyar sallah ta.’

Cike da farin ciki da walwala suka yi sallama sannan ya wuce gidan Hajia. Yana shiga gidan ya tarar da Hajia a parlor ɗinta suna hira ita da Yaya Jidda, yaranta kuma suna ta kai wa da kawowa a tsakar gidan. Bayan ya gaida Hajia ya yi mata barka da sallah ya juya suka gaisa da Yaya Jidda wadda take ta faman shan kunu tana basarwa saboda kar ya yi mata wata magana.

Bayan sun gaisa sun ɗan taɓa hira da hajia ya dubi Yaya Jiddan yace ‘Yaya bari na ba ki account number ki turo min 10k ɗin da na tura miki ta yi wa yara sayayyar kayan shayi; tunda sun ce min ba a saya ba ko? Ta sake haɗe girar sama da ƙasa ta kalli hajia sanna ta kalle shi tace ‘Ban gane ba a siya ba, an siya mana.

Kawai dai ba ranar da ka bayar ba don kafin ka turo kuɗin masu kantunan sun rufe. Shi yasa ba a samu an saya ba har sai ranar da aka sake buɗe gari, ranar da ka zo kenan ka kwashe su. Da safen da ka tafi da su ai da sun zo za su tarar da kayan komai an saya don har ciko ma nayi.’

Hajia tace ‘Ai kuwa ka ga babu maganar dawo da kuɗi tunda an sayi kaya.’Takaici ya kama shi don ko ɗaya bai yarda da wannan zancen nata ba, ya kawar da kai sannan ya sake dubanta yace ‘Haka ne, to shi kenan, sai a ɗauko min ragowar na tafi da su tunda jibi yaran za su dawo har Khadeejan kuma ko suga babu a gidan sai na sake siya.

Ki aika a ɗauko min su tunda kusan ma ba a yi amfani da su ba kenan tunda ranar da aka siyo ranar suka tafi. Kafin ta yi magana Hajia tace ‘To su sauran yaran gidan ba ‘yayanka ba ne da ba za a ba su ba, kayan shayin kawai ba wani abu.’ Ta dubi Jiddan tace ‘Ko da yake bari na barku wataƙila suna nan ki ba shi ya kai gidan nasa.’

Ta sake kicin kicin sannan tace ‘Hajia kema dai kin san yaran nan ba za su bari ga kayan shayin har da Indomie su bari na ajiye ba tare da na ba su ba. Sai dai kawai idan biyansa zan yi na yi wa babansu waya ya biya abinda ‘yayansa suka ci tunda yana kallo suna ci kuma ya san ba shi ya siyo ba.’

Hajia tace ‘A a ba za a yi haka ba, sai kace a garin matsiyata ake.’ Ta dubi Mustaphan tace ‘Kai Mustapha ka yi haƙuri, ba na son wannan rigimar taka. Wannan ma ai ba wani abu ba ne da za a ɗaga tunda daga yaranta har nakan duk ‘yayanka ne. Muryarsa a maƙogoro yace ‘Shikenan Hajiya.

Ya miƙe tsaye yana cewa ‘Bari na je wajen Alhaji mu ci tuwon tare, ko da yake ma a ƙoshe nake me sanyin kawai zan sha. Yana shigewa Jidda ta kalli Hajia tace ‘Kin gani ko Hajia, a kan kayan shiya zai yaga min rigar mutunci, wallahi yaron nan har yanzu bai yi hankali ba.’

Tace ‘Ya fi ki gaskiya, ya za ki karɓi kuɗinsa kuma ki dinga bar masa yara da yunwa?Hajia wallahi na gaya miki ƙarya yaran nan suke yi, kawai don sun san za a biye musu ne suke abinda suka ga dama. Idan banda haka ya za a yi na hana su abinci na ba wa su Nawwara tunda ai duk tare suke wuni suna wasansu; kawai dai suna so su nuna su ubansu mai kuɗi ne.’

‘Ki dai bi shi a hankali kin ji na gaya miki. Bari ma ya fito na ji sai yaushe zai kawo min yaran yawon Sallah ko kuma ni ma laifin naki ne ya shafe ni ya kai yaran wajen wadda da ba ya son ya bar mata su?’

Haka yana ji yana gani ya haƙura ya ƙyale Yaya Jidda; daman ya riga ya san Hajia ba za ta taɓa bari a ga laifinta ba. Kamar yanda aka yi alƙawari ranar uku ga sallah tun wajen ƙarfe tara na safe ya tafi ɗaukan Khadeeja; da yake sun riga sun yi waya a shirye ya same ta don haka ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ɗauko ta ita da mai aikinta Rashida suka kama hanya.

Sai da suka tsaya a gidan Mama suka kwashi yara sannan suka wuce gidan Hajia. Nan suka zauna a parlor ana ta hira yayin da yara suke ta kai wa da kawowarsu. Jimawa kaɗan Yaya Jidda ta dubi Khadeeja tana nuna Rashida tace ‘Wannan yarinyar taki kuwa za ta iya wani aikin kirki? Kada fu ku je a kama ku da child abuse?’

Ta yi dariya duk da yanda maganar ta ɓata mata rai tace ‘Ah haba dai, shekarunta fa sha biyar yaya don dai kawai ba ta da girma ne. Aiki kam ta iya sosai ko a gida ma Mommy ta koya mata.’‘To amma idan Habi ta dawo sai a mayar da ita ko? Tunda na ji Habi ɗin tace baku da wata matsala da ita kuma tana nan ita ma tana shirin dawowa.’

‘Uhm, sai a haɗa biyu ma tunda kin ga ga hidimar gida ga ta yara, kuma ina zuwa makaranta. Haba wace hidima ce sai an haɗa ‘yan aiki har biyu a wannan gidan? Hidimar har nawa take? Kafin ta ba ta amsa Mustapha ya shigo yana cewa ‘Ku tashi mu tafi ko, don na san kuna da aiki a gidan nan don duk ya yi ƙura.’

Suka fara shirin miƙewa yayin da ita kuma Yaya Jidda ta kalli Mustaphan tace ‘Na ga kun samo ‘yar aiki, Baba Habi ma fa tana nan tana shirin dawowa. Yace ‘Ah ai kawai sai ki ce mata ta yi zamanta tunda dai gaskiya ba mu da inda za mu ajiye ‘yan aiki har biyu. Da nace ta mayar da wannan ɗin idan Baba Habi ta dawo?’

‘To ga ta nan ku yi magana idan ta fi son Baba Habi ɗin sai a mayar da wannan ɗin.’

Ba tare da ɓata lokaci ba Khadeeja tace ‘Uhm ai gara a bar wannan ɗin, in ya so in da wata matsala sai na yi magana a nan ɗin a kawo wata. Haka dai dole Yaya Jidda ta bar su suka tafi ba tare da ta iya gamsar da su cewa Baba Habi za ta dawo ba.

Kamar yanda ya faɗa kuwa kaca-kaca suka tarar da gidan, sai dai suna shiga suka fara ƙoƙarin gyarawa. Kuma da yake yana ajiye su ya sake fita har da Afaf da Habib aka yi aikin, don haka cikin ƙanƙanin lokaci suka gama.

A haka rayuwa ta cigaba; sai dai a ɓangaren Mustapha idan dai yana gidan ba a saka masa yara aiki, sai dai su su yi ta gara Rashida komai ita za su aika ko su saka. Khadeeja tana son ta tsawatar musu amma tana tsoron abinda ubansu zai ce tunda ta ga sun ɗan sami natsuwa babu wata hatsaniya, ba ta so ta ja rigima. Don haka haka ta zuba musu ido; abu kaɗan sai a ƙwalawa Rashida kira ko da kuwa aikin Khadeejan take yi dole ta bari ta je ta yi musu yanda suke so.

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 31st Octoba 2025
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Uku
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.